Sky Daily Hausa

Sky Daily Hausa Sky Daily Hausa Jarida ce da ke yada labaran siyasa, kasuwance da kuma wasanni. Mun shahara wajen ya

Trump ya fitar da Amurka daga kungiyoyin duniya 66Gwamnatin Trump ta sake fita daga kungiyoyin kasa da kasa guda 66 tare...
08/01/2026

Trump ya fitar da Amurka daga kungiyoyin duniya 66

Gwamnatin Trump ta sake fita daga kungiyoyin kasa da kasa guda 66 tare katse tallafin kudaden cikin gaggawa ga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya 31 da wasu kungiyoyi 35 wadanda ba na Majalisar Dinkin Duniya ba.

Shugaba Donald Trump ya ce matakin gwamnatinsa na janye Amurka daga kungiyoyin duniya, ya biyo bayan la'akari da ba su biyan bukatun kasarsa, ya umurci dakatar da duk wani tallaafin kudade ga kungiyoyin cikin gaggawa ciki har da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya 31 da wasu kungiyoyi 35 wadanda ba na Majalisar Dinkin Duniya ba.

Fadar White House ta ce kungiyoyin suna gudanar da ayyukan da s**a sabawa muradun Amurka na tsaro da wadatar tattalin arziki da kuma 'yancinta. "Ko ba komai, Amurka ta fice daga kungiyoyi masu adawa da ita kuma marasa amfani wadanda ake almubazzarancin kudi." inji Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio. Ya kara da cewa "Ana ci gaba da nazari kan wasu kungiyoyin da za a raba gari da su nan gaba." Yawancin kungiyoyin da matakin ya shafa suna aiki a fannoni k**ar muhalli da manufofin yanayi ko daidaiton jinsi.

Matakin Trump na raba gari da kungiyoyin bai fayyace adadin kudaden da gwamnatin za ta yi tsiminsu ba. Tun da ya koma kan karagar mulki wa'adi na biyu, Trump ya matsa kaimi wajen fitar da Amurka daga wasu tsare-tsare na kasa da kasa, da s**a hada da hukumar lafiya ta duniya da hukumar al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO.

A wa'adinsa na biyu kuma, Trump ya dakatar da tallafin Amurka ke ba wa kasashen duniya da dama ciki har da Afirka, ya kuma katse ayyukan kungiyoyi da wasu hukumomi wanddanda ya ce ba su da amfani.

DW Hausa

Gwamnan Bauchi ke zargin APC da tursasa wa 'yan hamayya don komawa cikintaA Najeriya, kura ta fara tashi game da yayin s...
04/01/2026

Gwamnan Bauchi ke zargin APC da tursasa wa 'yan hamayya don komawa cikinta

A Najeriya, kura ta fara tashi game da yayin sauyin sheka da gwamnoni da sauran jiga-jigan 'yan siyasa na jam'iyyun hamayyar kasar ke yi zuwa jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Gwamnan jihar Bauci, Bala Mohammed ya bayyana tirjiniya a kan abin da ya kira matsin lambar da ake yi masa ta hanyoyi daban-daban, don ya watsar da jam'iyyarsa ta PDP ya koma APC.

Sai dai jam'iyyar ta APC ta musanta wannan zargi, kuma ta ce ba ta tursasa wa kowa ya koma cikinta.

Yayin da a bayyane gwamnoni da yan majalisar dokokin Najeriya da mukarrabansu da dama da s**a yi sauyin sheka daga jam'iyyun hamayya zuwa APC mai mulkin kasar, suke cewa sun yi hakan ne don radin kansu, shi kuwa gwamnan jihar ta Bauchi ya yi zargin, cewa ana ta yi wa jam'iyyarsu ta PDP bi-ta-da-kulli, don a gurgunta su, a kuma tilasta masu sauya sheka.

Wani makusancin gwamnan, Babangida Maliya, wanda kuma shi ne shugaban karamar hukumar Shira a jihar ta Bauchin, ya yi karin haske:

''Kwarai kuwa da gaske akwai wannan. Ai idan ka duba yanayin rikicin jam'iyyar PDP da halin da take kasancewa. Yau jam'iyyar PDP an kasa barin ta ta zauna lafiya, inda suke amfani da wasu karnukan-farautarsu ko kuma makusantan shugaban kasa don lalata al'amuran jam'iyyun hamayya, musamman ma PDP wadda al'umma ke ganin ita ce mafitarsu a wannan kasa.

''Ita ce za ta share musu hawaye, shi ne ya sa ake mata wannan bi-ta-da-kulli don a ga cewa ba ta zauna lafiya ba.''

Maliya ya kara da cewa, ''daga baya-bayan nan kuma aka shiga matsin lamba da tursasawa ga gwamnan jihar Bauchin, a kokarin tilasta masa komawa jam'iyyar APC karfi da yaji.''

Ciki kuwa har da yi masa zarge-zargen yin almundahanar kudade, tare da k**a wasu jami'an gwamnatinsa, a cewar Babangida Maliya.

Sai dai kuma daraktan yada labarai na kasa na jam'iyyar APC, Bala Ibrahim, ya musanta wadannan zarge-zarge:

''Ya k**ata a san cewa ciki da gaskiya ba ya tsoron wuka. Tsari ne fa ake bi na dumukuradiyya ba na k**a-karya na mulkin soja ba.''

''Mene ne nasa na yin wadannan bayanai na barazana? Dole idan ka ga an haska fitila to ai an ga duhu ne a guri.''

''Su wadannan gwamnoni da s**a koma jam'iyyarmu su ya k**ata a bai wa dama su fada da bakinsu amma ba wasu su rika zargi suna hasashe suna zato ba,'' in ji Bala Ibrahim.

Ana kallon wannan ce-ce-ku-ce ne a matsayin wata sabat-ta-juyat-ta da ke aukuwa, sak**akon karatowar zaben shekara ta 2027, inda jam'iyyar APC ke neman wa'adin mulki na biyu, yayin da jam'iyyun hamayya ke neman yi mata jirga-in-maye.

BBC Hausa

Jami’an gidan hukumar gyaran hali a Kano tini sun kawo Sheikh Abduljabar Nasir Kabara harabar kotu domin yanke hukunci, ...
15/12/2022

Jami’an gidan hukumar gyaran hali a Kano tini sun kawo Sheikh Abduljabar Nasir Kabara harabar kotu domin yanke hukunci, k**ar yadda kotun ta sanya yau Alhamis.

Sababbin kudin da shugaba Buhari ya ƙaddamar a safiyar yau.
23/11/2022

Sababbin kudin da shugaba Buhari ya ƙaddamar a safiyar yau.

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sky Daily Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sky Daily Hausa:

Share