17/05/2025
FA’IDODI GUDA GOMA GA WANDA YA SAMU SALLAR ASUBA CIKIN JAM’I
1- FA’IDA TA DAYA.
“Samun Ladar Tsayuwar dare da ibada, idan kayi sallar assuba da isha’i a jam’i.
Annabi s.a.w yana cewa:
(Wanda yayi sallar isha’i a jam’i kamar ya
raya rabin dare da ibada,wanda ya kuma
ya kara da Sallar assuba a jam’i kamar ya
raya darene gaba daya). Tirmizy ya ruwaito shi.
2- FA’IDA TA BIYU.
“Samun kariya da alkawalin Allah”.
Annabi s.a.w yana cewa: "Wanda yayi sallar assuba acikin jam’i yana cikin alkawali da kulawar Allah".
3- FA’IDA TA UKU
“Shiga gidan aljanna” Annabi s.a.w yana cewa:
(Duk wanda ya sallaci sanyin nan guda biyu”Wato Sallar la’asar da assuba” zai shiga Aljanna).
4- FA’IDA TA HUDU
“Samun kubuta daga munafinci”.
Annabi s.a.w yana cewa: (Sallah mafi nauyi ga munafiki itace SallarAsuba da Isha’i, Kuma da yasan alkhairin dake cikinta da ya halascesu koda da rarrafe ne.
5- FA’IDA TA BIYAR.
“Samun ladar aikin hajji da Umara
cikakkiya ga wanda ya sallaci Sallar asuba
a jam’i sannan ya zauna yana rokan Allah
har rana ta fito”. Annabi s.a.w yana cewa:
{ ﻣﻦ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻐﺪﺍﺓ ﻓﻲ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺛﻢ ﻗﻌﺪ ﻳﺬﻛﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺘﻰ ﺗﻄﻠﻊ ﺍﻟﺸﻤﺲ ﺛﻢ ﺻﻠﻰ ﺭﻛﻌﺘﻴﻦ ﻛﺎﻧﺖ ﻟﻪ ﻛﺄﺟﺮ ﺣﺠﺔ ﻭﻋﻤﺮﺓ }…
6- FA’IDA TA SHIDA.
“Samun adduar mala’iku da kuma rubutaka cikin wadanda suke halartar sallar assuba a jam’i,Sannan zasu rubuta maka ita amatsayin aikinka na farko awannan yini,Sannan dayan mala’ikan zai rubuta maka ita a matsayin aikinka na karshe a daren da ya gabata”….
Annabi s.a.w yana cewa:
{ ﻳﺘﻌﺎﻗﺒﻮﻥ ﻓﻴﻜﻢ ﻣﻼﺋﻜﺔ ﺑﺎﻟﻠﻴﻞ ﻭﻣﻼﺋﻜﺔ ﺑﺎﻟﻨﻬﺎﺭ ، ﻭﻳﺠﺘﻤﻌﻮﻥ ﻓﻲ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﻭﺻﻼﺓ ﺍﻟﻌﺼﺮ ،ﺛﻢ ﻳﻌﺮﺝ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺑﺎﺗﻮﺍ ﻓﺒﻜﻢ ﻓﻴﺴﺄﻟﻬﻢ ﺭﺑﻬﻢ ﻭﻫﻮ ﺃﻋﻠﻢ ﺑﻬﻢ : ﻛﻴﻒ ﺗﺮﻛﺘﻢ ﻋﺒﺎﺩﻱ ؟ ﻓﻴﻘﻮﻟﻮﻥ :ﺗﺮﻛﻨﺎﻫﻢ ﻭﻫﻢ ﻳﺼﻠﻮﻥ ﻭﺃﺗﻴﻨﺎﻫﻢ ﻭﻫﻢ ﻳﺼﻠﻮﻥ }
7- FA’IDA TA BAKWAI
“Samun haske cikakke a ranar alkiyama”
Annabi s.a.w yana cewa:
:{ ﺑﺸﺮ ﺍﻟﻤﺸﺎﺋﻴﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﻈﻠﻢ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻤﺴﺎﺟﺪ ﺑﺎﻟﻨﻮﺭ ﺍﻟﺘﺎﻡ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ }
8- FA’IDA TA TAKWAS.
“Dacewa da falalar raka’a tanin fajir,wadda
Annabi s.a.w yake cewa tafi duniya da
abinda yake cikinta alkhairi”. Annabi s.a.w yana cewa:
:{ ﺭﻛﻌﺘﺎ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﻣﺎ