Jibwis Kafur LG.

Jibwis Kafur LG. An organization for eradicating innovations and establishing Sunnah.

14/08/2026

Majalisin Karatun Sahihul Bukhari Nabanje Islamic Centre na sanar da dalibai cewa: Yau ba karatu sai Allah ya kaimu wani satin

06/08/2026

Gobe Juma'a akwai karatun sahihul Bukhari a Masallacin Juma'a Nabanje Islamic Centre.

A isar da sakon ga inda bai kai ba.

SANARWAR KARATUN DARE NA KAFUR LOCAL GOVERNMENT A madadin Kwamitin Matasa na Jibwis Kafur Local Government, muna sanarda...
06/08/2026

SANARWAR KARATUN DARE NA KAFUR LOCAL GOVERNMENT

A madadin Kwamitin Matasa na Jibwis Kafur Local Government, muna sanarda masu halartar karatun dare na wata-wata cewa wannan watan akwai karatu wanda zai gudana kamar yadda aka saba.

Rana: Alhamis 06/08/2026
Lokaci: 10pm
Wuri: Jibwis Central Masjid, Kafur

Ana sanar da na nesa a taho da wuri.

Allah ya bada ikon halarta Aameen.

P.R.O 1
Mustapha Abdurrauf S/kasa

SAKON TA'AZIYAIna mika sakon ta'aziyata ga Oga Habibu Ya'u (Divisional Commandant, Kafur Division) a bisa rasuwar Mahaif...
01/08/2026

SAKON TA'AZIYA

Ina mika sakon ta'aziyata ga Oga Habibu Ya'u (Divisional Commandant, Kafur Division) a bisa rasuwar Mahaifiyarsa, yau Juma'a 31/7/2026.

Ina Addu'a Allah ya ji kanta da Rahma, Amin.

31/07/2026

Muna bada haƙuri!
Yau Babu Karatun Sahihul Bukhari a Masallacin Juma'a Nabanje Islamic Centre.

17/07/2026

Yau akwai Karatun Sahihul Bukhari a Nabanje Islamic Centre

Gobe Juma'a 10/07/2026 za'a dawo Karatun Sahihul Bukhari a Masallacin Juma'a Nabanje Islamic Centre.Wanda yaga sanarwar ...
09/07/2026

Gobe Juma'a 10/07/2026 za'a dawo Karatun Sahihul Bukhari a Masallacin Juma'a Nabanje Islamic Centre.

Wanda yaga sanarwar yayi sharing zuwa ga wanda basu sani ba.

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta bada umarnin gabatar da Al-Qunut a faɗin jihar ...
29/06/2026

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta bada umarnin gabatar da Al-Qunut a faɗin jihar Katsina

A yau, Lahadi 13 Muharram 1448H, wanda ya yi daidai da 28 ga Yuni, 2026, Majalisar zartaswa ta Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta gudanar da muhimmin taro domin nazarin halin da ake ciki a jiha Katsina tare da ɗaukar matakan da s**a dace wajen samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen da al'umma ke fuskanta.

Da yake gabatar da jawabin buɗe taron, Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah), ya fara da godiya ga Allah (S.W.T) bisa ni'ima da amincewar shi ya haɗa fuskokin mu a daidai wannan lokaci domin tattaunawa akan abinda ya shafi da'awa. Ina roƙon Allah ya sanya albarka da nasara a cikin wannan zama da za mu gudanar.

Ya kara da bayyana cewa manufar kiran wannan taron ita ce tattauna manyan matsalolin da s**a addabi al'umma, musamman matsalar rashin tsaro da taɓarɓarewar tarbiyya, tare da tsara hanyoyin da za su taimaka wajen samun mafita bisa koyarwar Al-Qur'ani da Sunnah.

Shugaban ya kuma yi ishara da taron da Gwamnatin Jihar Katsina ta kira shugabannin ƙungiyoyin addini da malamai domin neman shawarwari kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Bayan dogon nazari, Majalisar ta bayyana cewa Allah (S.W.T) ya h**e wa al'umma matasa masu ƙwazo waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen shiryar da jama'a, dawo da kyawawan ɗabi'u, yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da kuma magance matsalar badala.

Majalisar ta kuma jaddada cewa gyaran al'umma ba zai cika ba sai an samar da shugabanci nagari. Saboda haka, ta ƙarfafa mambobinta da sauran al'umma su shiga cikin harkokin siyasa domin samar da shugabanni na gari tun daga matakin farko, domin a samu jagoranci nagari a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Da wannan ne ne aka amince da aiwatar da wani shiri na dogon zango da zai mayar da hankali kan wayar da kan al'umma, gina tarbiyya, da ƙarfafa shugabanci nagari.

Shirin zai mayar da hankali kan:
1. Gina ilimi a matsayin jigon addini da zaman lafiya.

2. Fahimtar al'amuran zamani bisa koyarwar Musulunci (Fiqhul Waqi').

3. Hada karfi da karfe domin magance matsalolin da su ke fuskantar wannan al-umma

4. Gina tarbiyya da ƙarfafa imani ga matasa.

5. Kira zuwa ga tuba da komawa ga Allah.

6. Wayar da kai kan haƙƙoƙin makwabtaka da zamantakewa a tsakanin al'umma.

Sakamakon da ake sa ran cimmawa ya haɗa da:
1. Ƙara fahimtar koyarwar musulunci kan shugabanci, zamantakewa da amana.

2. Gina al'umma mai haɗin kai da kyawawan ɗabi'u.

3. Samar da hanyoyin magance matsalolin matasa, iyalai da zamantakewa.

4. Ƙarfafa zaman lafiya da sake haɗa kan al'umma.

Maudu'an farko da za a gabatar sun haɗa da:

1. Muhimmancin kishin ƙasa da rawar da ake takawa wajen gina al'umma.

2. Gudummawar mutanen kirki a harkokin siyasa da wajabcin shiga domin gyaran al'umma.

3. Matsalolin taɓarɓarewar tarbiyyar matasa da hanyoyin magance su.

4. Muhimmancin haɗin kai, haƙuri da juriya wajen bunƙasa al'umma.

Bayan gabatar da waɗannan shawarwari, an buɗe ƙofa ga mahalarta taron domin gabatar da ra'ayoyi da shawarwari, tare da bayyana cewa ƙofar Majalisar a buɗe take ga duk wanda yake da wata shawara mai amfani, ba sai lokacin taro kaɗai ba.

A ƙarshe, Majalisar Zartaswa ta Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta amince da bada umarnin gabatar da Al-Qunut a dukkan masallatan kungiyar da ke faɗin jihar Katsina.

An umarci cewa za a riƙa gabatar da Al-Qunut a dukkan sallolin farilla guda biyar, tare da yin addu'o'i na musamman kan halin rashin tsaro da sauran ƙalubalen da al'umma ke fuskanta. Haka kuma, za a ci gaba da yin irin waɗannan addu'o'i a ƙarshen huɗubobin Juma'a kamar yadda aka saba.

Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah), tare da halartar dukkan masu riƙe da muƙaman kungiyar a matakin ƙasa da na jiha, shugabannin ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, shugabannin Majalisar Malamai na ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, shugabannin Majalisar Agaji na ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, da kuma shugabannin Kwamitin Limamai na ƙananan hukumomi.

JIBWIS Katsina
13 Muharram, 1448
28 June, 2026

Allah ya maida kowa gida lafiya
28/06/2026

Allah ya maida kowa gida lafiya

Sakon bangajiya da fatan Allah ya maida kowa gidansa lafiya ya sa mun amfana da abinda muka koya amin
28/06/2026

Sakon bangajiya da fatan Allah ya maida kowa gidansa lafiya ya sa mun amfana da abinda muka koya amin

Address

Malumfashi Zaria Road
Kafur
820001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Kafur LG. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share