05/08/2025
YANZU-YANZU: Bello Turji ya ƙuduri niyyar ajiye mak**ai kuma ya saki mutane 32 - Asadus-Sunnah
Kasurgumin jagoran ƴan ta’adda a jihar Zamfara, Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su tare da amincewa da ya dena kaiwa manoma hari, bayan ganawa da malaman addinin Musulunci a dajin Fakai, karamar hukumar Shinkafi.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Malamin addini Musulunci, Musa Yusuf, wanda ya fi shahara da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan a wani taron addini a Kaduna, inda ya ce al’ummar Shinkafi ne s**a bukaci a shiga tsakani domin su samu damar komawa gonakinsu.
A cewar Yusuf, ganawar ta gudana sau uku a watan Yuli, kuma Turji da wasu fitattun mayaka k**ar Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya, ciki har da ajiye mak**ai da barin manoma su koma gonaki ba tare da fargaba ba.
Yusuf ya ce wadanda aka sako sun hada da mata da yara, kuma sun shafe kusan watanni hudu a hannun Turji.
Wasu daga cikinsu sun haifi yara a daji, yayin da daya daga cikinsu ta kamu da cizon maciji.
Ya ce tun bayan yarjejeniyar, zaman lafiya ya fara dawowa a yankin Shinkafi, inda manoma ke ci gaba da aikin gona cikin kwanciyar hankali.
Malamin ya gargadi wasu malamai da ke s**ar Turji a kafafen sada zumunta da su daina, yana mai cewa hakan na iya tayar da zaune tsaye.
Ya yabawa Shugaba Bola Tinubu, Nuhu Ribadu, Gwamna Dauda Lawal da Sanata Shehu Buba saboda goyon bayan hanyar zaman lafiya wajen magance matsalar tsaro a Zamfara.