
03/09/2025
Anata Kai Hare Hare Duk Da Sulhun Da Akayi Da Yan Bindiga
Rahotanni na nuna cewa 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare suna kashe mutane da kuma sace dabbobi da sauran dukiya a wasu sassa na yankin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, a Najeriya.
A lamari na bayan-bayan nan sai da 'yan bindigan s**a kashe mutum biyar, s**a raunata wasu hudu a garin Galadi.
Daga Musa Lokaci Dan Jarida