10/12/2025
SANARWA TA MUSAMMAN DAGA MIYETTI ALLAH KAUTAL H**E – KADUNA STATE
A madadin shugabanci da mambobin Miyetti Allah Kautal H**e Jihar Kaduna, muna mika gaisuwar yabo da taya murna bisa wannan gagarumin girmamawa da Mai Martaba Sarkin Kagarko, Alhaji Sa’adu Abubakar, ya yi wa ɗan’uwa namu, jagora kuma abin alfaharin matasa — Alhaji Aminu Jibril — ta hanyar naɗa shi Sarkin Samarin Kagarko.
Wannan sarauta ta zo a lokacin da matasa ke buƙatar nagartaccen wakili, mai hangen nesa, mai haɗin kai, kuma mai tsayawa kan gaskiya da ci gaban al’umma. Lallai wannan zaɓe ya tabbatar mana da cewa al’umma sun gane jajircewarsa, halayyarsa ta kwarai, da irin gudummawar da yake bayarwa a cikin jama’a.
Muna da yakinin cewa Alhaji Aminu Jibril zai ɗauki wannan nauyi da amana, ya zama jagora mai fuskar haɗin kai, ya ci gaba da kare mutuncin matasa, da kuma karfafa zaman lafiya tsakanin Fulani da sauran al’ummomi a yankin Kagarko da ma Jihar Kaduna gaba ɗaya.
Bikin Nadin Sarauta zai gudana kamar haka:
📅 Rana: 10 ga Janairu, 2026
⏰ Lokaci: 10:00am
📍 Wuri: Fadar Emir na Kagarko
Muna kira ga mambobin Miyetti Allah, dattawa, matasa da sauran al’umma da su halarta cikin girmamawa domin nuna goyon baya ga sabon Sarkin Samari, tare da addu’ar Allah Ya sa wannan sarauta ta zamo hanya ta alheri, kwanciyar hankali da cigaba mai dorewa.
Allah Ya ja zaman Mai Martaba, Allah Ya kara masa basira, hikima da nisa.
Allah Ya taya sabon sarki rikon amana, Ya sa wannan matsayi ya zamo alheri gare shi da al’umma baki ɗaya.