25/07/2025
HOTUNAN
Yadda Wani Kansila Mai Suna Hon. Hassan Safiyanu Yargoje Kewa Al'ummar Mazabar Danmaidaki Aiki.
"Hon. Hassan Safiyanu Yargoje matashin dan siyane wanda yakeda zuciyar ganin Al'ummar yankin sunci gaba fiye da kanshi" Hakan yafito ne daga bakin wani mazaunin garin Yargoje ayayin ziyarar Ganin yadda ake gudanar da wani muhimmin aikin hanyar ruwa wato (DRAINAGE) atsakiyar Garin Yargoje dake Karamar hukumar Kankara.
Kamar yadda muka tarar ana cigaba da gudanar da aikin gadar tsallakawa da ababen hawa kebi, muntarar anar gudanar da ita cikin aminci da nagarta.
Munyi kokarin zantawa da Al'ummar yankin da akewa aikin inda wasu dama samu damar hakan s**a nuna matukar farin cikin su dasumawar aikin.
Haka zalika gamida godiya akan yimasu wannan Hanya ruwa mai dauke da Kwalbati, wadda arashinta abaya sun fuskanci rigingimu atsakankanin jama'a yankin da Ruwa ke bi.
Zamu cigaba da kawo maku yadda aikin ke gudana
📷
Rana24