Fadila Yar Fulani

Fadila Yar Fulani An Kafar Kankara First News domin samar da ingantun,sahihai labarun cigaba.

HOTUNANYadda Wani Kansila Mai Suna Hon. Hassan Safiyanu Yargoje Kewa Al'ummar Mazabar Danmaidaki Aiki."Hon. Hassan Safiy...
25/07/2025

HOTUNAN
Yadda Wani Kansila Mai Suna Hon. Hassan Safiyanu Yargoje Kewa Al'ummar Mazabar Danmaidaki Aiki.

"Hon. Hassan Safiyanu Yargoje matashin dan siyane wanda yakeda zuciyar ganin Al'ummar yankin sunci gaba fiye da kanshi" Hakan yafito ne daga bakin wani mazaunin garin Yargoje ayayin ziyarar Ganin yadda ake gudanar da wani muhimmin aikin hanyar ruwa wato (DRAINAGE) atsakiyar Garin Yargoje dake Karamar hukumar Kankara.

Kamar yadda muka tarar ana cigaba da gudanar da aikin gadar tsallakawa da ababen hawa kebi, muntarar anar gudanar da ita cikin aminci da nagarta.

Munyi kokarin zantawa da Al'ummar yankin da akewa aikin inda wasu dama samu damar hakan s**a nuna matukar farin cikin su dasumawar aikin.

Haka zalika gamida godiya akan yimasu wannan Hanya ruwa mai dauke da Kwalbati, wadda arashinta abaya sun fuskanci rigingimu atsakankanin jama'a yankin da Ruwa ke bi.

Zamu cigaba da kawo maku yadda aikin ke gudana

📷
Rana24

SANARWAR DAURIN AURE:  Amadadin Iyalan Marigayi Malam Idris Maikayan Miya Kankara  Na Farin Cikin Gayyatar Al'umma Zuwa ...
27/07/2024

SANARWAR DAURIN AURE:
Amadadin Iyalan Marigayi Malam Idris Maikayan Miya Kankara Na Farin Cikin Gayyatar Al'umma Zuwa Daurin Auren Shugaban Jaridar Rana24 Wanda Za'ayi Kamar Haka 👇

RANA:9th, August -2024
LOKACI:2:30 Na Rana
WURI:Kofar Fada Kahutu Karamar Hukumar Danja Jihar Katsina

Kungiyar Tafoki Support Organisation Ta  Rabawa 'Yan Gudun Hijira Kayan Tallafi A Garin Kankara Jihar Katsina.✍️Mannir I...
30/03/2024

Kungiyar Tafoki Support Organisation Ta Rabawa 'Yan Gudun Hijira Kayan Tallafi A Garin Kankara Jihar Katsina.

✍️Mannir Idris Kankara

A ranar 28/3/2024 Kungiyar dake goyowa Dan majilisar wakilan mai wakiltar Kananan hukunomin Kankara, Faskari da Sabuwa a tarayya Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ta bayar da tallafi ga masu gudun hijira da Kuma gajiyayyu dake shiyyar Unguwar Nasarawa cikin garin kankara.

Kayan tallafin sun hada da Buhunnan shinkafa 2 kwalayen kilin da Kuma na sabulun wanka guda goma sha biyu.

Anashi jawabin shugaban kungiyar baki daya Malam Musbahu Tukur Kogunan sarkin Pauwa,yace wannan sun yini ne amatsayin somin dabine.
Hasalima sunyi hakane maimakon suje hannu , Amma akwai abubuwan da dama dake kan hanyar zuwa.

Shugaban kungiyar TSKmatakin karamar hukumar kankara Nasir Wada Zango ya yaba da gudumuwar tallafin yakuma gargadi ga shuwagaban rabon kayan.

Malam Nazir Abdullah wanda shine jogaran wadanda kayan yayi Godiva duba da yanda aka zabi makarantar shi amatsayin inda, za'a kaddamar dactallafin.

SAKON GODIYA ZUWA GA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KATSINA MAL. FARUK LAWAL JOBE|||Sakon Godiya Daga Kungiyar Multipurpose Co...
21/03/2024

SAKON GODIYA ZUWA GA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KATSINA MAL. FARUK LAWAL JOBE|||

Sakon Godiya Daga Kungiyar Multipurpose Cooperetive Society Kankara Zuwa Ga Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina His Excellency Faruk Lawal Jobe.

Kungiyar 'yan kasuwa masu gudanar da hada Hadar kasuwanci a mazaunin su dake Kan titin gidan Marigayi Alhaji Babajo Lawal Sarkin Pauwa mai suna Multipurpose Cooperative Society kankara tana isar da sakon godiyar ta abisa basu tallafin kudi da Mataimakin Gwamnan Katsina Malam Faruk Lawal Jobe Ya basu.

Tallafin kudin N50,000 ya biyo ta daya daga cikin mahima kuma nawakin Mataimakin gwamnan jihar katsina M20, ya damkashine ga hannun shugaban Kungiyar Malam Bilya Hamisu Kamshi.

Ajawabin shugaban godiyar Bilya amadadin yan kungiyar ya nuna farin cikin shi abisa wannan Abun arziki da aka turo masu dashi.

Yayin mika wanna tallafi Mawakin Jobe M20 ya yace wannan tallafi ne domin a gudanar da al'ammuran na rayuwa.

Shuwagabani da 'yan kungiyar sun nuna farin cikin su gamida godiya zuwa ga Mataimakin Gwamnan abisa basu wannan abub arziki da yayi masu.

Sponsored By
M20

Dan-majilisar Dattawa Sen. Muntari Mohammed Dandutse Ya Gwagwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Kudade.Daga: Mannir...
21/03/2024

Dan-majilisar Dattawa Sen. Muntari Mohammed Dandutse Ya Gwagwaje Al'ummar Karamar Hukumar Kankara Da Kudade.

Daga: Mannir Idris Kankara

A yau Laraba Dan-majalisar Dattawa yankin Katsina ta kudu Sen. Muntari Mohammed Dandutse ya rabawa mutane 400 N10,000 a karamar hukumar kankara.

Hon. Abubakar Nuhu wanda shine jagoran wakilan da s**a gudanar da rabon kudaden wadanda s**a zo daga garin Funtua ya fara da bayyanawa Mutanen das**a amfana da sakon godiya daga Danmsjilisar ga Al'immar karamar hukumar ta kankara bisa nuna kauna da goyon bayan da suke nuna mashii.

Sannnan ya kuma tabbatar da akwai wasu ayyukan alheri dake tafe zuwa garin na kankara Wanda Sanatan yasamo daga tarayya daga bisani ya lissafawa al'umma yadda tsarin rabon kudin yake zuwa kaso 4.

Kason farko akwai Malamai 100, 50,50 daga Darika da Izala, Mata 100,Dattawa 100 sainkuma matasa 100 Wanda jimillar s**a kai 400 Inda kowa yasamu kunshin N10, 000 hannu da hannu.

Malam Hamisu Donawa na daya daga cikin kwamitin rabon ya bayyana sun kasa rabon shiyyoyi 11 na mazabun da karamar hukumar ta kunsa, wanda Hakan yasa mutanen wajen gari sun amfana matuka.

Daya daga cikin Malaman da s**a amfana Malam Abdulrashid ya yaba sosai da wannan tsari domin zai ragewa mutane radadin halin da ake ciki, shima Malam Isah ya godewa Danmajilisar gamida yin addu'a ta Kara samun cigaba.

Mata da Maza dama ne s**a kasance cikin farin ciki.

Nazir Isiya wanda shine mai taimakawa wajen biyan Malamai Addini ya yaba da halin dattakon da aka nuna.

Haka zalika shima Aliyu shehu dake bangaren biyan mata ya nuna godiya da yadda matan s**a nuna yayin tantacewa.

Sauran Yan kwamitin tafiyar da rabon kudin sun hada da Bature Omo, Shamsuddeen Magaji, Abdulbasir Maihoto, Danjuma Direba da Kuma Sadiq Pauwa.

Anyi rabon batare da samun Wani tarnakiba.

MACE MAI KAMAR MAZA : Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawarma Akan Huddatayyar Gwamnatoci Excmo. Hadiza Hassan Maikudi ...
18/03/2024

MACE MAI KAMAR MAZA : Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawarma Akan Huddatayyar Gwamnatoci Excmo. Hadiza Hassan Maikudi Ta Rabawa Al'umma Buhunnan Shinkafa 40.

Honorable. Hadiza Hassan Maikudi wadda itace maibaiwa Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ta bayar da manyan Buhunnan shikafa masu nauyin 50 ga al'umma.

Kamar yadda wakilin mu ya tabbatas anyi rabon shinkafar ne Farfajiyar sabuwar Kasuwar Kankara wadda akafi sani da Modern Market dake kan titin Zuwa garin Dutsinma cikin garin Kankara. Shinkafar buhunna 40 masu nauyin 50 kowannanen su.

Ayayin jawabin shi Wakilin Rabon Shinkafar Ingr. Abdulbasir Gambo Kankara ya bayyana "Wannan rabon shinkafa Hajiya Hadiza tayine domin tallafawa al'umma domin Allah da zummar ragewa jama'a wahalhalin alfarmar wantan wata na Ramadán.

Al'umma sun Yaba da yadda Ingr. Abdulbasir ya tsaya Kai da fata tun daga farko rabo har karshen rabon wantan shinkafa.

Maitaimakawa gwamnan jihar Katsina ta fannin samar da labarai daga karamar hukumar kankara Muhammad Sale OC (Manga) wanda shima dayane daga masu rabon wannnan shinkafa Kuma daga cikin matasan da suke goyawa Excmo. Hadiza Baya ya tabbatar cewa wantan kadan ne daga cikin alkairan da Hajiyar keda zummar samawa al'umma.

Wasu daga cikin wadanda s**a amfana da wantan shinkafa sun yaba da wantan taimako datayi musanman acikin irin want yanayi da ake ciki na rayuwa. Sun Kuma Yi addua'ar Allah ya jikan iyayenta yasa agama da duniya Lafiya.

Daga cikin wadanda s**ai aikin rabon sun hada da Malam Ibrahim Gerente, Excmo. Aminu Suleiman da Sauransu

📷Rana24

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Kai Ziyarar Ta'azziyar Ga Iyalan Shugaban Hukumar Tsaron C-Watch Na...
23/02/2024

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Faruk Lawal Jobe Ya Kai Ziyarar Ta'azziyar Ga Iyalan Shugaban Hukumar Tsaron C-Watch Na Karamar Hukumar Kankara.

✍️Mannir Idris Kankara

A ranar Alhamis 22/2/2024 Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Maigirma Malam Faruk Lawal Jobe yakai Ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Malam Sanusi Hassan Kankara Shugaban hukumar Tsaro ta jihar Katsina.

Malam Sanusi ya yagamu da ajalin shi tahanyar harbin bindiga awata musayar wuta da aka gwabza da Yan ta'addar daji ajiya Laraba.

Ayayin ziyarar ta'aziyyar maigirma mataimakin Gwamnan Faruk Lawal Jobe ya jajantawa Iyalan Marigayin haka zalika yayi Addu'ar naman gafara ga mamacin da fatan Aljanna ce makomar shi.

Waɗanda s**a rufa mashi baya sun hada Kwaminshinan Ayyuka na musanman Alhaji Isah Mohammed, Shugaban gudanarwar na Babban Asibitin Garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango da sauran Al'umma.

Yakumayi Addu'ar Allah ya kawo tabbatacen zaman lafiya a karamar hukumar Kankara, Jihar Katsina da Najeriya baki daya.

📷 Rana24

Dan Majilasar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kankara, Faskari Da Sabuwa Ya Samawa Al'ummar Motocin Dauka Marasa ...
26/01/2024

Dan Majilasar Tarayya Mai Wakiltar Kananan
Hukumomin Kankara, Faskari Da Sabuwa Ya Samawa Al'ummar Motocin Dauka Marasa Lafiya

A ranar Alhamis 25/1/2024 Dan Majilasar , ,, mai Kananan hukumomin Kankara, Faskari Da Sabu,,wa ac tarayya Hon. Jamilu Mohammed Lion ya samar da motocin Asibiti a Kananan hukumomin dayake wakilta.

Hon. Jamilu Mohammed Lion Yana daya daga Cikin Yan Majilasar Wakilai da s**a ionsamu nasarar akarkashin Jam'iyyar PDP ga Jihar Katsina azaben gama gari daya gudana a Shekarar 2023.

Dan Majilasar Wakilan ya fara Ƙaddamar da mika motar Asibitin ne da karamar Karamar Hukumar Kankara ayau m alokacin Gudanar bikin Hon. Lion ya kuma samar da motar daukar Marasa Lafiya kirar Golf sabuwa gadagal ga Al'ummar Mazabar Garagi ta Kankara.

Haka zalika ya samar da Fayib Fayib na rijiyar tuka tuka kimanin guda 250 domin gyaran wasu rijiyoyin burtsatsen da s**a Samu matsala gamida hannuwan buga rijiyoyin burtsatsen Guda Biyu.

Hon. Jamilu lion Baitsayana Nan ba ya Samar da Buhunnan Shinkafa guda 80 dukka ga al'umma Mazabar Garagin ta Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.

Shugaban Jam'iyyar PDP a karamar hukumar Kankara Hon. Amadu Mai kanananzir yayiwa mahalarta taro barka da zuwa sannan yayi kira ga al'ummar Mazabar Garagi da kada su biye wani ya rudesu ayayin gudanar da Zaɓen Cika gurbin da za'a ayi nan GABA.

Comr. Nuraddeen Adam Tina Yayi kira da jan kunne ga al'umma yankin Garagi dasu tsaya tsaf su zabi Jam'iyyar PDP a Zaɓen mazabar domin cigaba da sharbar romon demokariya.

Shugaban Matasan Jam'iyyar PDP a Mazabar Garagi Alhaji Nura ya Tabbatarwa Dan Majilasar Wakilai da yardar Allah zasu Tabbatarwa duniya Mazabar Garagi ta PDP ce, yakuma godewa Waɗannan abubuwan Alheri da Hon. lion yasamar ayankin su.

Danmajilisar inda Zaku Iya tunawa bayan Zaɓen da ya gudana abonkin takararshi na Jam'iyyar APC Hon. Dalhatu Tafoki ya garzaya kutun sauraran kararraki zabe domin kalubalantar yanda aka gudanar da Zaɓen Saboda rashin yin zabw awasu rumfunan Zaɓe daga

Lambobin Karramawa (CERTIFICATES) kuWaɗanda S**a Karasa mana karin maganar  mu na Jiya. Ku Duba Acikin CERTIFICATES  Yan...
05/01/2024

Lambobin Karramawa (CERTIFICATES) ku
Waɗanda S**a Karasa mana karin maganar mu na Jiya.
Ku Duba Acikin CERTIFICATES Yanzu.

Muna baku barka da shiga sabuwar Shekarar 2024

Daraktan Babban Asibitin Garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango Ya Yabawa Kungiyar Kankara APC Social Media.Shuagaban bab...
30/11/2023

Daraktan Babban Asibitin Garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango Ya Yabawa Kungiyar Kankara APC Social Media.

Shuagaban babban Asibitin garin Katsina Dr. Mohammed Umar Zango ya nuna farin cikin shi duba da yadda kungiyar matasa masu amfani da kafar Zamani Mai suna Kankara APC Social Media Forum ta shirya taron karrama wasu zakakuran mutane.

Taron da aka gudanar a babban dakin taron hukumar Ilmin Karamar Hukumar dake kan hanyar zuwa Funtua a garin Kankara.

Dr. Mohammed Zango ya nuna gudanar da irin wannan taron Mai hada Al'ummar daga Ma'aikatu daban daban, yakuma Kara tabbatar da cigaba da kawowa Karamar hukumar Kankara abubuwan cigaba.

Bugu da kari Dr. Zango ya godewa Al'ummar das**a baro aiyukan su zuwa wannan taro Hadi da godema wadanda s**a shirya taron har karramawa ga Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe.

Kimanin matasa 6 yasamawa abunyi acikin Yan makonni kalilan da zamanshi zama matsayin dayake Kai ahalin yanzu.

28/11/2023


Za'a Gina Filin Wasa Na Zamani A Garin Kankara Insha Allah. - Inji Alh. Surajo Mika'ilu.

✍️ Mannir Idris Kankara

Sakataren din -din-din a hukamar matasa da wasanni ta jihar Katsina Alhaji Surajo Mika'ilu ya bayyana kokarin Gwamnatin jihar Katsina afannin ganin ta habaka rayuwar matasan Jihar Katsina.

Alhaji Surajo Mika'ilu ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi daya gudanar ataron da wata kungiya ta shirya domin karrama wasu zakakurarrun mutane da s**a taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban ga al'uma 'Yan Asalin Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

Alhaji Surajo Mika'ilu wanda shine Sakataren din din din ahukumar matasa da wasanni ta Jihar Katsina ya bayyana geamnatin Jihar ta Katsina karkashin Jagorancin Malam Dikko Umar Radda Gwagwaren Katsina tareda Mataimakin shi Malam Faruk Lawal Jobe na bakin kokari domin ganin habakawa matasa hanyoyin more rayuwa a fannoni da dama na rayuwa a duk fadin Jihar.

Bugu da kari, Surajo Mika'ilu yace Akwai wata kungiya ta cigaban Kankara data kaimashi ziyara inda s**a roki Gwamnatin jihar Katsina data ginama Karamar Hukumar Kankara filin wassanni na zamani, abisa hakan Akan wannan bukatuwa yanzu haka tuni akasa saka aikin na Karamar Hukumar Kankara cikin kasafin Kuɗin kasafin Kuɗin wannan Shekarar.

Inda kara dacewa "Za'a gina Filin Wasa Na Zamani A Garin Kankara Insha Allah."

📷 Rana24

Address

Kankara

Telephone

+2347035655275

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fadila Yar Fulani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Fadila Yar Fulani:

Shortcuts

Share