07/03/2025
BAKI SON HAIHUWA?
*
**
***
Da ace kin san abinda zan rubuta, da baki biyewa huɗubar turawan yamma ko shaiɗanun ƙawayen ki ba, ga su kamar haka:
1. Idan kika yi ciki, Allah zai sa dukkan Mala'iku su dinga nema miki gafarar sa kullum har ki haihu.
2. Allah zai rubuta miki ayyuka kyawawa dubu, ya shafe miki ayyukan ki munana guda dubu, kullum zai baki ladan azumi da rana, da daddare ya rubuta miki ladan ibada cikin dare.
3. Yayin da cikin ya fara baki wahala, Allah zai rubuta miki ladan wanda yayi jihadi.
4. Idan kika haihu, Allah zai baki ladan sallah da azumi na shekaru 70.
5. Duk jijiyar ki da ta wahala yayin naƙuda, Allah zai baki ladan aikin hajji adadin jijiyoyin.
6. Idan kika mutu a wurin haihuwa (naƙuda), kin mutu a matsayin shahidiya, za ki shiga Aljanna kai tsaye ba tareda hisabi ba b***e azaba.
Duk wannan fa sanadiyar Aure.
In kaga mace tana son aure amma bata son haihuwa da wuri ko haihuwa da yawa, akwai karancin sanin abubuwan da na faɗa. Sanin abubuwan da na faɗa yana cikin dalilin da yasa magabatan mu suke yin kyakkyawar karshe, gasu ba ilimi ba, ba kyau ba, ba iya kwalliya ba, amma abubuwan alherin da s**a tara a asusun su dake gun ubangiji sanadiyar aure suna da yawa, amma a yau sune ake kallo a matsayin wawayyun mutane, ita kuwa mace mai bijirewa miji da mai haihuwa adadin da taso a lokacin da taso, da mai fito na fito da mazaje, itace mace wayayya abin koyi, Allah ya sauwake.
In kayi magana sai ace maka ai haihuwa da yawa bai da amfani, ka haifi wayanda za aka iya kulawa dasu, sai gashi mafi yawa masu ya'ya kaɗan din sune iyayen lalatattun yara.
Ai da ace jama'a sun san ubangijin da ya raya yaron nan bayan uwar sa ta haife shi a sahara ta mutu amma ya girma ya zama sarki, da sunyi kuka fiye da wanda Azra'ilu yayi yayin da yake zare ran mahaifiyar yaron.
Babu wayewa bayan tsarin Annabi ﷺ
✍️✍️✍️ Sidi Sadauki ♥️
*** O'oh Ahmad Aliyyy ***