
06/09/2025
Qafila Monthly Bulletin” (fitar 06/Satumba/2025).
Muhimman abubuwan da aka gabatar sun haɗa da:
1- Ziyara ga shugaban Majalisar Koli ta Musulmi a Najeriya, Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Al-Hussaini (R.T.A).
2- Halartar tarukan hadin kan Musulmi a garin Gombe, Bajoga/Funakaye, da kuma Funtua (Jihar Katsina).
3- Ziyara ga Sheikh Prof. Ibrahim Makari, Sheikh Nuru Khalid (Digital Imam), da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
4- Ziyara ga shugabannin darikun Sufaye ciki har da Darikar Qadiriyya da Majalisar Shura ta Tariqa Tijjaniyya a Kano.
5- Sauran ziyarce-ziyarce sun haɗa da Sheikh Bello Lau (Hedikwatar JIBWIS, Abuja), Sheikh Khalifa Baba Ali Abulfathi (Abuja), da Sheikh Abdulwahab Abdallah (Kano).
Mujallar ta jaddada manufar ƙarfafa haɗin kai, ƙauna da zumunci tsakanin Musulmi ta hanyar waɗannan ziyarce-ziyarcen da tarukan, tare da hotuna da s**a tabbatar da abubuwan da s**a gudana.
ALLAH YA BADA NASARA.