01/11/2025
Aniyar ki ta biki...
Kanwa uwar gami, uwar kitifi da ha'inci, tinkiya uwar timbele, kura mai kafirar zamba!
Nigeria kasa ce ta dimokradiyya duk da bara zanar da dimokradiyyar ke samu akwai sauki akan "freedom of speach" lallai inda kiristanci da kiristoci sunga alamar muzgunawa, ba sai turawan yamma sun yi magana akai ba!
Domin suna da bakin su, suna da ilimin su, suna da hankalin su kuma yan kasa ne ba bakin haure ba! Kenan sun san abinda ya dace suyi...
Ko me yasa kuka dage sai kun hada mu rik¡cin addini?
Kun kunna mana fit!nar fahimtun addinai, kun kunna mana wutąr gaban junan kasashen africa, kun bijiro mana da band¡t, kun kawo mana adawar juna tsakanin Hausa Fulani, kun tare a kasar mu kuna kulla alaqoki da yan t9'9dd9 da bata garin shugabanni da sunan bada tallafi, kuna kwashe mana zakakuran masu ilimi ta hanyar biyan su kudi mai yawa don su koma kasar ku suyi muku bauta don su watsar da kasar mu dake bukatar su!
Mu ke da gold, oil da sauran ma'adanai!
Muke da yanayin zafi, sanyi, ruwa da sauran albarkan kasa tare da girmanta kuma cikin yawan al'umma amma muna cikin kasashen da s**a fi shan wahala a duniya! Kuma zaton da muke yi duk sakamakon kawancen mu da turawan yamma ne!
Ya dace gomnati tayi martani akan muna zaman lafiya tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba kuma muna ma juna fatan alkhairi...
Ya dace shuwagabannin addinai suyi kira akan hadin kan addinai da yin tarurruka na hadin kan addinan tare da yin martani akan masu cewa kiristoci na samun matsin lamba.
We are friends, both Muslims and Non Muslims especially Christians.
Allah ya zaunar da nigeria lafiya, ya hada kan musulmi, ya karo fahimta tare da kishin juna tsakanin musulmi da kirista, Allah ya kara dankon zumunci tsakanin Hausa Fulani, ya kara mana kaunar juna Kudu da Arewa ubangiji ya hade mana kasashen Africa wuri guda! ya karo mana arziki da wadata cikin ilimi tareda kariyar sa Amin.
Kana Taɓa Wannan shuɗin Rubutu Zai Kai Shafin Jaridar 👉 Duniyar labarai 👈Sai Ka Dangwali Alamar Like👍 Ko Follow, Kai Tsaye Zaka Ringa Sam