31/10/2025
Natasha Ta Gayyaci Akpabio Zuwa Bikin Kaddamar da Ayyuka a Kogi
Dangantaka tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ta fara samun sauƙi bayan Akpoti-Uduaghan ta aika da gayyata ga Akpabio domin halartar bikin kaddamar da ayyuka a yankinta.
Gayyatar, wacce aka rubuta da hannunta, ta kuma haɗa da sauran sanatoci, kuma an karanta ta a zauren majalisar yayin zaman ranar Alhamis da Akpabio kansa ya karanta.
A cewar wasikar, bikin zai gudana ne a ranar Lahadi a Ihima, Jihar Kogi, domin bikin cika shekaru biyu da Akpoti-Uduaghan ta yi a majalisar dattawa.
“A yayin bikin cika shekaru biyu a matsayin Sanata mai wakiltar al’ummata, ina gayyatar sanatoci abokaina da su zo bikin kaddamar da ayyuka a Jihar Kogi,” in ji wasikar.
An bayyana Plot 101, Jimoh Akpoti Street, Ihima, Okene a matsayin wurin taro, inda aka ba da shawarar cewa sanatocin da ke tafiya ta jirgi su sauka a Obajana Airstrip kafin su ci gaba zuwa Ihima ta hanya.
Bayan karanta gayyatar, Akpabio ya taya ta murna a gaba da kowa da cewa:
“Ina taya ki murna a gaba.”
Wannan mataki na nuna sabon yanayi na sulhu bayan rikicin da ya barke a watan Fabrairu kan rabon kujeru a majalisar, wanda ya jawo dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida daga aiki a ranar 6 ga Maris.
Tun bayan dawowarta a ranar 24 ga Satumba, Sanatar ta fara sake shiga hulɗa da Akpabio a zauren majalisa, ciki har da bayar da gudunmawa a muhawara da dokoki. Amma wannan gayyatar ce ta fi nuna mataki kai tsaye na sulhu da shugabancin majalisar.