Zauren Tarihi

Zauren Tarihi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zauren Tarihi, TV Channel, Kano.

12/12/2025

Tarihin Annabawa da Sahabbai a harshen Hausa.

02/12/2025

Labarin YAJUJU da MAJUJU

29/11/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! خديجة خلود, Ibrahimsani Muhammad, Shamsudeen Abubakar, Muhd-Tukur Musa Baba, Muhammad Jamilu Tijjani, Aliyu Abubakar

28/11/2025

Mene ne sunan rana da za a tara mutane gaba ɗaya?

A. Yawmul-Hisab
B. Yawmul-Jam’
C. Yawmul-Fasl
D. Yawmul-Ghadab

Kuyi following dina domin amsa irin tambayoyinnan

Bismillahir Rahmanir Rahim.Kusan shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), akwai w...
22/11/2025

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Kusan shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), akwai wata al’umma da ke zaune a ƙasar Sham, a yankin Harran. Wannan al’umma ta juya daga bautar Allah, ta fara yin sujada ga gumaka da ƙarya alloli.

Don komar da su zuwa hanya madaidaiciya, Allah Ya zaɓi Ayyub (Alaihissalam) a matsayin annabinsa. An aiko da shi ne ya kira mutanensa zuwa ga tauhidi, wato imani da Allah guda ɗaya ba tare da haɗa Shi da abokin tarayya ba

Annabawa ana saninsu da sunan da ke nuna halayensu, kuma Ayyub (AS) bai bambanta ba. Sunansa “Ayyub” yana nufin wanda yake dawowa, wanda yake komawa ga Allah. An ba shi wannan suna ne saboda a duk lokacin da ya fuskanci wahala, sai ya koma ga Allah kaɗai.

DOMIN SAMUN BIDIYON WANNAN TARIHI KUJE YOUTUBE CHANNEL DIN MU MAI SUNA " ZAUREN TARIHI"

Ayyub (AS) yana cikin annabawan da Alƙur’ani ya ambata, waɗanda Allah Ya ba su ilimi da hikima. Ya kasance mutumin kirki mai tsoron Allah kuma yana guje wa mugunta. Ya zama abin koyi na haƙuri da godiya.

Uwar Ayyub (AS) ita ce ’yar Annabi Lut (AS), kuma uban sa a cewar Imam At-Tabari, jikan Annabi Ishaq ne.
Ayyub (AS) ya kasance kyakkyawan mutum ƙwarai, dogo, mai jiki mai ƙarfi, kuma yana da idanu masu kyau.

Allah Ya albarkace shi da ƙarfi mai yawa, ta hanyar addu’a da albarkar kakansa, Allah Ya ba shi arziki da yalwa.
Yana da ’ya’ya maza guda goma sha biyu (12), dukansu masu imani ne da tsoron Allah.
Matarsa Rahimah ta fito daga zuriyar Annabi Yusuf (AS), mace ce mai tsarki da biyayya, kullum tana tare da Ayyub (AS) cikin wahala da sauƙi, tana nuna ƙauna da aminci gare shi.

Allah Ya ba Ayyub (AS) dukiya mai yawa ƙwarai a ƙasarsa — yana da filaye masu faɗi, raƙuma marasa adadi, shanu, dawakai, jakuna, da awaki.
Gidansa ya zama mafakar bayi da ma’aikata da yawa, kuma kowa yana samun kulawa da alheri daga gare shi.

Duk da yawan dukiyarsa, girman kai bai taɓa shiga zuciyarsa ba, kuma dukiyarsa bata taɓa shagaltar da shi daga hanyar Allah ba.

17/11/2025

Wace ce matar Annabi Ayyub da ta yi masa hidima a lokacin jarrabawa?
A. Rahima
B. Maryama
C. Zulaiha
D. Hajara

TARIHIN SARAUNIYA BALQIS Ta yi shawara ta tara duk ma’aikatan sarauta da masu ba ta shawara a fannin yaƙi.Ko za su iya y...
11/11/2025

TARIHIN SARAUNIYA BALQIS

Ta yi shawara ta tara duk ma’aikatan sarauta da masu ba ta shawara a fannin yaƙi.
Ko za su iya yaƙi a wannan hali da suke ciki?Taron zai zama mahimmi sosai.

A haka nan, Annabi Sulaiman (AS) ya shirya taro a garinsa.
Ma’aikatan sa sun haɗa da ministoci, masana yaƙi, da malamai.
Dabobin zakuna biyu sun tsaya kusa don kare taron.
Hudhud ma yana nan, shiri yake don bayanin abin da ke faruwa.

Sulaiman ya buɗe taron da cewa:
“Na gode wa Allah domin duk arziki da ikon da ya ba mu.”
Ko da yake cikin fushi, bai bayyana a wajan mutane.

Ya ci gaba da cewa:
“Yaya zai iya zama muna rayuwa, muna tafiya da tutar Tawhid, amma wasu suna bautar rana? Wannan kaskanci ne ga mu.”

Sulaiman ba ya mulki domin darajar sa, amma domin mulkin Allah.
Saboda haka, ya ji fushi da alhaki.

wani Jarumi ya tashi da takobi a hannu yace:
“Ka ba ni umarni, zan halaka kujerar Sarauniyar Balkis da mutanen da ke ƙin Allah.”

Amma Sulaiman ya ce:
“Ban son ta’asi. Dole mu nemi wata hanya. Ina fatan Sarauniya za ta zo gare ni. Amma kafin ta isa, wanene daga cikinku zai iya kawo kujerarta nan?”

Daya daga cikin Aljanu ya ce:
“Zan kawo Kafin ka Tashi tsaya...ka san karfina.”

Amma malami Alajani mai ilmi (Ilm al-Ladun) ya ce:
“Zan kawo ta gare ka kafin ka ma kifta ido.”

Da Sulaiman ya yarda, Nantake kujerar Queen Balkis ta bayyana gaban sa.
Kamar teleportation ne, abin da ba kowa ya taɓa yi ba.
Kowa ya cika da mamaki; kujerar tana da girma da kyau.
Hudhud na nan shima, yana ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru.

GARIN SABA

A garin Saba, duk ma’aikatan masarauta da masu yaƙi sun taru.
Sarauniya Balkis ta shugabanci taron.
Kowa yana bayyanar da fuska ta damuwa.

Ta ce:
“Yau muna fuskantar matsala mai wuya. Sulaiman na son mu Mika wuya gareshi, ya na barazana da halaka karfinmu. Na nemi ku don tallafi domin neman samun mafita”

Masu ba da shawara sun yarda cewa kila sarauniya da kanta ce kawai za ta iya zuwa ga Sulaiman.
Wataƙila hakan zai kawo sulhu.
Amma sun ce idan ya ƙi karɓa, yaƙi zai zama zaɓi ɗaya, kuma zai iya gogesu daga tarihi.

Sarauniya Balkis ta yanke shawara ta je ga fadar Sulaiman da kanta.
An fara shiri, sababbin kyautuka masu kyau da arziki sun shirya domin Sulaiman.
Annabi Sulaiman ya san cewa Sarauni tana da tunani marasa dacewa game da ikon sa.
Ta yi alfahari da ci gaban ƙasarta, amma Sulaiman na son koya musu gaskiya da darasi:
Girma na gaskiya da ci gaba na gaske na zo ne karkashin tutar Tawhid. DOMIN CIGABA KU KALLA A YOUTUBE 👇👇👇👇
https://youtu.be/AbPU8d765Ks?si=heKrtvXF6yVepr82

KU BIYO MU DOMIN SAMUN CIGABAN WANNAN LABARIN.
KARDA KU MANTA KUYI FOLLOWING ZAUREN TARIHI DOMIN SAMUN LABARAI NA TARIHI. KU ZIYARCI YOUTUBE CHANNEL DINMU DOMIN SAMUN CIKKEN VIDEO DIN TARIHIN SARAUNIYA BALQIS.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zauren Tarihi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category