01/10/2021
NATIONAL DISCIPLINARY COMMITTEE SUN KAMMALA GANAWA DA SHUGABANNIN AGAJI NA JIHOHI DA NATIONAL ZONE.
Commitin national disciplinary na F.A.G OF F.I.N sun kammala ganawa da daukacin shugabannin Agaji na jihohi da Kuma na national zone bisa wasu gyare-gyare da s**a dakko, an tattauna abubuwa masu tarin yawan gaske mun Kuma gode musu bisa bamu lokacinsu da s**a yi muna fatan Abubuwan da muka tattauna da su za a samu damar tabbatar da su a jihohi.
Commiti din ya bada umarni a kafa Disciplinary Committee Mai dauke da mutun 7 wanda Displine na jaha zai zama chairman na Committi din haka L.G Haka rassa.
Commiti din ya sake jaddada cewar dole ne a tsaya a iya dokokin da Bylaw na Kungiya ya shimfida domin Tabbatar da doka da oda.
An haramta sanya wani launin kaya wanda ba Fari ba da sunan Uniform, dole ne uniform na Dan Agaji ya zama wando Fari Riga fari takalmi Fari blue din hula lanyan blue ko Mai ratsin Fari da blue.
Discipline na jiha zasu sanya jar hula da Jan lanyard kadai Haka Abin zai tafi har zuwa rassa.
Muna Kira ga Yan Agaji da su kasance masu biyayya da bada goyan baya domin samun cigaba a cikin wannan tafiya.
Allah ya bamu lafiya da zama lafiya.
Naxeer muhammad Musa
Information National Disciplinary Committee.