23/10/2025
YANZU-YANZU: Ƴan Sanda Sun K**a Sowore A Kotu
Daga Yasir Kallah
Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta k**a mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam, kuma tsohon ɗan takarar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya, Omoyele Sowore, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Sowore, wanda ya jagoranci zanga-zangar neman sakin jagoran haramtacciyar ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra ta IPOB, Nnamdi Kanu, a ranar Litinin a Abuja ya tsare daga wajen zanga-zangar a lokacin da ƴan sanda s**a damƙe wasu daga cikin mabiyansa.
Kafin a fara zanga-zangar, rundunar ƴan sanda ta yi gargaɗi ga masu shirya zanga-zangar da su guji zuwa kusa da wasu wurare masu muhimmanci a Birnin Tarayyar amma Sawore ya yi kunnen uwar shegu, inda ya ce yana da ƴancin yin zanga-zangar.
A yau ne Soworen ya halarci zaman kotun da ke gudana a game da batun Kanu a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
"A yau, na haɗu da Kanu Agaji, babban lauyan Kanu Nnamdi, a Babbar Kotun Tarayya, kuma ya faɗa min cewa tawagarsa za ta janye daga ƙarar, inda za ta bar Nnamdi Kanu ya ci gaba da shari'arsa ba tare da wakili ba. Ya yi matuƙar tabbatar da cewa gabaki ɗaya siyasa ce," Soworen ya wallafa kafin a k**a shi.
A lokacin da yake ƙoƙarin fita daga kotun ne tawagar ƴan sanda ta tsayar da shi tare da umartar sa da ya bi su zuwa ofishinsu.
Bayan sun ɗan yi musayar yawu ne Soworen ya amince ya bi su.
Da yake magana game da kamun, ɗaya daga cikin makusantan Soworen ya shaida wa Daily Trust cewa tun da farko Kwamishinan Ƴan Sanda na Birnin Tarayyar ya tura wa Soworen saƙon gayyata kuma dama zai amsa gayyatar.