Kabeer 2pac

Kabeer 2pac WANNAN SHINE FACEBOOK ACCOUNT DINA
KUYI LIKE DA FOLLOW TARE DA SHARES

Nasboi Kabeer 2pac
24/05/2025

Nasboi Kabeer 2pac

14/04/2025
YANZU-YANZU| Gwamnatin jahar kano zata gudanar da aikin tsabtar muhalli na musamman a gobe asabar wacce ta kasance ranar...
24/12/2021

YANZU-YANZU| Gwamnatin jahar kano zata gudanar da aikin tsabtar muhalli na musamman a gobe asabar wacce ta kasance ranar bikin Cirsimeti, kwamishinan ma'aikatar muhalli ta jahar kano Hon Dr Kabiru Ibrahim Getso, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman kwamitin da Gwamnatin jahar ta kafa wanda kwamishinan ma'aikatar Muhallin ke jagoranta sai dai kuma yace a lokacin baza'a takaita zirga-zirgar ababan hawa ba, domin bawa mabiya addinin cirista damar gudanar da shagul-gulansu.

Kwamishinan yace za'a gudanar da aikin tsabtar muhalli a Kasuwanni, guraren aiki da tashoshin mota a ranar Juma'a 31 gawatan December na shekarar 2021, kamar yadda aka saba a kowanne karshen wata.

Daganan Kwamishinan yaja hankalin Al'umma dasu cigaba da bin dokokin yaki da annobar cutar Coronavirus tare da cigaba da anfani da safar rufe baki da hanki wato (facemask) domin zai temaka wajen rage yaduwar cutar.

Daga Comr Aliyu Abdul Garo.

01/02/2021

: Hira Ta Musamma Tareda Babban Mataimaki Ga Gwamna Kano Akan Ilimi Mai Zurfi Dr Hussaini Jarma, Ayi Saurare Lafiya.

SHEKARA DAYA MAI AL'BARKA. Daga: Bello NasirMataimaki na musamman P.AMaigirma Babban mai bawa Gwamna shawara a bangaren ...
01/02/2021

SHEKARA DAYA MAI AL'BARKA.

Daga: Bello Nasir
Mataimaki na musamman P.A

Maigirma Babban mai bawa Gwamna shawara a bangaren kafafen Yada Labarai na zamani (Social Media) Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, Yacika shekara daya a Ofishinsa bayan Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje Ofr, Ya dawoshi a matsayin SSA karo na Biyu.

Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, Mutunne mai Haquri da Jajirtacewa Wajen Gudanar da Aikinsa, wanda Kullin burinsa shine na kara inganta Harkokin Social Media a jahar kano Domin Matasa su Amfana.

A Lakacin zangon Mulkin farko na Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje Ofr, Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, Yayi Ayyuka da dama ciki harda Bada Horo ga matasa sama da 200 Yan social Media Wadanda s**a samu shedar kwarewa ta musamman.

Muna Kara Jaddada Godiya ga Maigirma Gwanman jahar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Ofr, bisa kara bawa Hon. Abubakar Aminu Ibrahim, wannan matsayi na SSA karo na biyu domin Cigaba da Bunkasa Wannan Harka ta Social Media.

23/12/2020

Gov. Ganduje ya saka hannu akan kasafin kudin shekarar 2021 akan kudi N177Billion.

Daga: Salisu Muhd Mati

Gwamnan Jihar kano Dr Abdullahi umar Ganduje OFR, ya kaddamar da wasu tsare tsaren kula da lafiyaDaga: Salisu Muhd Mati....
21/12/2020

Gwamnan Jihar kano Dr Abdullahi umar Ganduje OFR, ya kaddamar da wasu tsare tsaren kula da lafiya

Daga: Salisu Muhd Mati.
Special Assistant To The Governor On Social Media.

Gwamnan Jihar kano Dr Abdullahi umar Ganduje OFR, ya kaddamar da wasu tsare tsaren kula da lafiyar al'umar jihar kano guda uku a matakin farko, da s**a hadar da yaye mata sama da dubu guda da zasuyi aikin bada shawarwari kan kula da lafiyar yara da mata masu juna biyu da tsarin dagatai nasa ido wajen kula da lafiya.

Taran ya samu halarta shugaban majalisar dokoki na jihar kano da sauran shugabannin majalisar da shugaban jam'iyar APC da kwamishinoni da hakimai da wakilan kungiyoyin kasa da kasa dake taimakawa wajen marawa gwabnati baya a harkar kula da lafiya.

TAKAITATCAN TARIHI KARATUN GWAMNA KANO DR ABUDULLAHI UMAR GANDUJE ofr.By: Salisu Muhd Mati Special Assistant To The Gove...
15/12/2020

TAKAITATCAN TARIHI KARATUN GWAMNA KANO DR ABUDULLAHI UMAR GANDUJE ofr.

By: Salisu Muhd Mati
Special Assistant To The Governor Kano On Social Media

An Haifi Abdullahi Umar Ganduje cikin 25 ga watan satumba 1949 cikin gidan masarautar garin Ganduje dake Karamar hukumar Dawakin Tofar Jahar kano. Bayan karatunsa na islamiya Dr. Abdullahi ya Fara karatunsa na Firamare school cikin shekarar 1956-1963. Gwamna Ganduje yaci gaba da karatunsa zuwa 'Government college' Birnin kudu'. wacce yanzu haka ke cikin jihar jigawa, Inda Yasamu Nasarar kammalawa tare da samun shahadar kammala da Kuma shahadar Jarrabawar ta hukumar ta Africa WAEC cikin shekarar 1964. Dr. Abdullahi Umar Ganduje yaci gaba da zurfafa neman limi a Kwalejin horar da malamin Makaranta Inda Yasamu shahadar kwarewa Kan Babbar Shedar malinta ta kasa 'N.C.E cikin 1969-1972. Sabida kishin ilimi da sha'awar bada gudunmawa ga Jaharsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje yaci gaba Zuwa jami'ar Ahmadu Bello dake Birnin zazzau (A.B.U). Inda ana ma Yasamu Nasarar kammala digirinsa na farko akan llimi cikin shekarar 1972-1975. Cikin shekarar 1977-1979 Daktan ya Kara zurfafa karatunsa Zuwa Jami'ar Bayero ta kano, Inda ya samu Nasarar kammala digirinsa na biyu a fanin sha anin Mulki. Cikin 1977-1979

Sanna Yakara Cigaba Da Karatunsa Na Digiri na 3 PhD Wanda Ya Fara A 1989-1993 Wanda Yayishi A Jami'ar Ibadan Allah ya azurta Shi Da Samu Dr.

Ya Kure duk wata shahada da Dan Boko ke fatan samu a fanin Koyo da Koyarwa, Kimanin Shekara 40 data gabata, Gwamna Ganduje Yana Da Kwarewa Wajen Koyarwa Domin ya Koyar a Makarantu kamar haka: Kwalejin Sakandire ta Oleh dake Jahar Rivers, ma'aikatar llimi ta Jahar Kano 1976, Makarantar horar da Malamai ta kasar Gumel 'college of education Gumel' a matsayin lecture, yaci Gaba da hidimar bada ilimi a jamiar Jahar kanawa Bayero University Kano a matsayin lecture cikin shekarar 1976.

-Gwamna Ganduje Shekarar Sa (45) Da Kammala Digirinsa Na Farko.
-Gwamna Ganduje Shekarar Sa (41) Da Kammala Digirins

GWAMNATIN KANO TA MAYE GURBIN -DG RAMATDaga; Salisu Muhd MatiSpecial Assistant To the Governor Kano StateMai Girma Gwamn...
15/12/2020

GWAMNATIN KANO TA MAYE GURBIN -DG RAMAT

Daga; Salisu Muhd Mati
Special Assistant To the Governor Kano State

Mai Girma Gwamna Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Rukon Kwarya Manajan Darakta ta Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kano (KHEDCO) Injiniya Hadiza Ahmad Tukur a matsayin mai rikon mukamin Darakta Janar na (Metropolitan Agency).

Darakta Janar na Hukumar na yanzu, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, wanda ke neman mukamin Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, yanzu an maye gurbinsa da MD KHEDCO, a matsayin mai rikon Kwarya, Mukamin yafara nan danan.

Da yake jawabi Gwamna Ganduje yaja Han kalin sabuwar Darakta mai rikon mukamin da ta kula da lamuran Hukumar yadda ya kamata.

Address

Kano

Telephone

+18025079203

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kabeer 2pac posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kabeer 2pac:

Share