21/08/2020
ALHAMDULILLAH!
A Madadin wannan Gida mai albarka da daukaci abokan tafiyar wannan Gida mai albarka, hadi da mai gayya mai aiki, haziqi, fasihi, managarci, Dattijon arziqi wato Dr. Mal. Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) kuma Sanatan Kano ta Tsakiya (Senator Kano Central) keyiwa al'umar Musulmin Duniya barka da shiga Sabuwar shekara.
Fatan Ubangiji yasa munshigeta a sa'a, fitintinu da annoba da jarabta kala kala da mukasha a shekarar data gabata dama ayyukanmu na kura kurai Ubangiji Allah ya yafemana.
Fatanmu ayyukan da mukayi nagari ya karba mana, yasanya a mizaninmu, yakauda fitina da rashin kwanciyar hankali a tattare damu.
A madadin wannan Gida muna taya Mai Girma Super Senator kuma sardaunan Kano Mal. Dr. Shekarau da Mai Girma Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da Shugabancin Jam'iya qarqashin Prince Abdullahi Abbas, Da tsohon Sakataren Jam'iya kuma Tsohon Kwamishinan Kasuwanci kuma Tsohon SSA Special Project Alh. Rabiu Bako barka da shiga Sabuwar shekarar Musulunci Ta 1442AH.
Allah yasa muga qarshen ta lafiya ameen.