06/04/2025
Wanda ya kafa bankin Stanbic IBTC ya caccaki rundunar ƴansanda ta ƙasa kan gayyatar Sarki Sanusi
Atedo Peterside, wanda ya kafa Bankin Stanbic IBTC , ya soki gayyatar da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi wa Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano, zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja.
An gayyaci Sanusi domin amsa tambayoyi kan kisan da aka yi a lokacin da Sarkin ke komawa gida bayan kammala sallar idi a ranar Lahadi da ta gabata.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na kafar X a yau Lahadi, Peterside ya ce rundunar ‘yansandan Kano ce ya fi da cewa ta gayyaci Sarkin.
“Mene ne Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ke kokarin mai da kasar nan? Najeriya ta zama kasa karkashin ikon ‘yan sanda ne? Shin akwai wata tambaya da Kwamishinan ‘Yan Sanda ba zai iya yi wa Sarkin Kano ba a cikin Kano a madadin manyansa da ke Abuja?” in ji shi.
Peterside ya kara da cewa gayyatar mutane daga jihohi daban-daban na nuni da “cin zarafi” ne kuma ya kamata a dakile irin wannan dabi’a.