02/01/2026
Gwamna Yusuf zai sauya sheka zuwa APC a ranar Litinin - Rahoto
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, zai shiga jam’iyya mai mulki ta APC a hukumance a ranar Litinin, k**ar yadda DAILY NIGERIAN ta rawaito.
Abba Yusuf, wanda shi kaɗai ne gwamna a jam’iyyar NNPP, ya riga ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen sauya shekar tasa.
Majiyoyi da ke da masaniya kan shirin sauya shekar gwamnan sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe, ne za su karɓi gwamnan a Abuja.
Tuni dai an dawo da jagoran APC a Kano, Abdullahi Ganduje, daga wata tafiya da yake yi a Dubai. Haka kuma an umarci shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, da ya taƙaita tafiyarsa ta Umara domin ya miƙa katin zama ɗan APC ga gwamnan a mazabarsa ta Diso, da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, a cikin makon nan.
Daily Nigerian Hausa