
02/05/2025
Labarin Tsoho Na Biyu Mai Karnuka:
Tsoho na biyu ma’abocin karnuka ya matso kusa da ifiritu ya fara bayar da labarinsa, ya ce, ka sani ya kai shugaban sarakunan aljanu, wadan nan karnuka biyu ‘yan uwana ne, ni ne na ukunsu. Mahaifinmu ya mutu ya bar mana gadon dinari dubu uku. Da aka raba wadan nan kudi aka ba wa kowa nasa, sai ni na bude rumfa a kasuwa ina ciniki a cikinta, ina saye ina sayarwa. Yan uwana kuwa s**a tafi fatauci.
Bayan shekara guda, sai yan uwan nan nawa s**a komo daga fatauci, babu komai tare da su na daga dukiya, duk sun salwantar da ita. Na ce da su, “Ya ‘yan uwana ashe dama ba sai da na ba ku shawarar kada ku tafi fataucin nan ba?” Su ka ce da ni, “Ya dan uwanmu ashe baka yarda da kaddarar Allah mai girma da daukaka da ya yi nufi akan mu ba?”
Na karbe su. Na rike su, na tafi da su gidana, na ba su abinci da sutura mai yawa, sannan na tafi da su zuwa ga rumfata ta kasuwa na ce da su na yarda su zauna mu yi kasuwanci tare da su, duk ribar da aka samu a raba ta uku dai dai, kowa ya dauki kashi daya.
Mu ka zauna akan haka har zuwa wani zamani mai tsawo. Sai wata rana ‘yan uwan nan nawa s**a ce suna so za su koma fatauci tunda yanzu sun sami nasu jari, s**a kwadaitar da ni akan mu tafi tare domin an fi samun riba mai yawa a fatauci. Na ki amincewa da in bar rumfata saboda na san ina samun riba sosai a cikinta.
‘Yan uwan nan nawa ba su gushe ba suna kwadaitar da ni akan zuwa fatauci har tsawon wasu shekaru. Daga karshe dai s**a shawo kaina na amince da za mu tafi tare da su. Muka kidaya kudin da ke gare mu, muka ga muna da dinari dubu shida. Na ba da shawarar mu raba kudin nan biyu, mu bisne rabi a kasa mu tafi da rabi, koda tafiya ba ta yi kyau ba, idan mun dawo muna da jarin da za mu ci gaba da kasuwancinmu. S**a aminta da wannan shawara tawa.
Muka raba kudin biyu, muka bisne dinari dubu uku a kasa, sannan kowannen mu ya rike dinari dubu daya. Muka sayi kaya, muka gama ciko, muka biya kudin jirgi, muka haura cikin bahar maliya.
TA IMAMU