Usman imam Muhammad

Usman imam Muhammad Politician.

❤️
15/09/2025

❤️

15/09/2025

Kotu ta wanke Rogo - Gaskiya, ke saita tunanin jama'a wajen yanke hukunci - ba jita-jita ba.

Galibi rayuwar jama'a a Nigeria na cike da hayaniya. Yin Zarge-Zarge na babu gaira-babu dalili ke yaduwa cikin hanzari kamar wutar-daji, yayinda tabbatar da hukunci na kwarai na samuwa sannu a hankali. Kamata yayi a sani cewar, har yanzu wannan kundin tsarin da muke dashi, na nuni da cewa doka ce kadai keda hurumin tabbatar da laifin da aka aikata, ba wai shaci-fadin wasu mutane ba.

A ranar 18 ga watan Augusta, na shekara ta 2025, Babbar kotu ta jihar Kano dake Bichi ta sake jaddada wannan sharadi, bayan sake nazari Kan cikakken binciken da aka gudanar, da aka alakanta shi ga Malam Abdullahi Ibrahim Rogo, wanda kotun ta tabbatar da cewa babu wasu kwararan hujjoji bisa doron doka da zasu sanya a rika yi masa kallon wanda ake zargi akan binciken da ake gudanarwa na rashawa.

Hukunci kotu ya bashi kariya ta hakkikinsa na dan kasa bisa tanadin da tsarin mulki ya bashi na kare masa mutumci, yancinsa da kuma yi masa adalci wajen sauraron sa yadda yakamata ba tareda daukan wani mataki akansa daya saba da doka ba.

Anan yana da matukar muhimmanci ayi bayani dalla-dalla cewar Mr. Rogo ya shigar da kara a kashin kansa, ba wai a karkashin inuwar gwamnatin Jihar Kano ba, wanda kuma ya mika kansa kacokan ga karkashin ikon da kotu, kuma ya shigo da lauyoyinsa cikin wannan al'ammari tareda kyale doka ta gudanar aikinta kan ka'ida.

Hakan da yayi shine abinda doka take bukata akan kowane dan kasa.

Maimakon a girmama wannan mataki, sai ga wasu muryoyin kafafen yada labarai na shakulatin-bangaro da cusa raini duk cewa batun na gaban kotu, inda s**a dukufa wajen cigaba da yada zarge-zarge marasa tushe da ake alakantasu kan wannan bawan Allah, inda s**a cigaba da kiranshi da sunan ' Barawo', wanda cigaba da alakantashi da wannan suna da kafafen yada labarai ke cigaba da yadawa ya matukar dagula al'ammarin wajen kara munana masa zato, wanda cigaba da yin hakan kauda kaine bisa jerin hujjoji da aka gabatar wanda doka ta amince dasu.

A bayyane take cewar, a bangare guda, magana ce da akeyi ta wani dan kasa da ya yarda da tsarin doka ,ya kuma gabatar da wannan zargi da ake masa a inda yakamata, daga bisani kuma doka ta wanke shi daga zarge-zarge da akeyi masa.

A daya bangaren kuma, batu ne na wasu mutane ne da s**ayi kyuyar amsa gayyatar kuto, s**a rika maganganu na sauya zahirin zance na gaskiya, s**a fifita yin shari'a ta hanyar rubuta kanun labarai a maimakon bonito da kwararan hujjoji daya kamata a gabatar dasu a zahiri. Ta tabbata da cewa babu kanshin gaskiya a ciki, illa kau da kai daga tattaunawa ta gaskiya.

Wannan mataki bawai yunkuri na rufewa Yan jaridu bakunansu bane, kamata yayi a sani cewar, gudanar da aikin Jarida na aiwatar da bincike mai zurfi, wani muhimmin jigo ne dake shimfide a tsarin mulkin demokradiyya, wanda yakamata a tsarin aiwatar da irin wannan bincike mai zurfi a tabbatar da shaidu da hujjoji da zasu inganta sahihancin sakamako na gaskiya, ba wai a buge da kame-kame da labaran kanzon-kurege wanda zai haifar da labarai marasa tushe b***e makama ba.

Kotu ita kadai ke tabbatar da laifi akan wanda ake zargi bisa hujjoji na gaskiya da aka gabatar.

Saboda haka da akwai bukatar jawo hankulan mutane dasu kara fahimtar cewa dasu rika taka-tsantsan da jinjina sakamakon abinda aka gabatar musu dashi da kuma yin hankali domin auna nauyin dukkan zargi da aka alakanta shi da wani.

A kashin gaskiya, shi hukuncin babbar kotu ba wata kariya bace ga wasu shafaffu da-mai, saboda haka wannan bayanai wani hakki ne dake kunshe a kundin tsarin mulkin kasa wanda babu yadda zaayi ayi rashin adalci a cikinsa. A karshe dai tsantsar gaskiya ce zatayi halinta - ba babatu ko tada jijiyoyin wuya ba.

Daga S. A. Mohammed, Mai bada shawara ta fannin Shari'a Mallam Abdullahi Ibrahim Rogo.

Da Ran Su Da Lafiyar Su Zakayi Takwas 4+4 ABBA GIDA-GIDA.
14/09/2025

Da Ran Su Da Lafiyar Su Zakayi Takwas 4+4 ABBA GIDA-GIDA.

14/09/2025

Allahumma salii ala sayyidina Muhammadin wa ala aalihi wa sahbihi wa sallim.

Oshe Dubai
14/09/2025

Oshe Dubai

Address

Kano

Telephone

+2347068487822

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Usman imam Muhammad posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Usman imam Muhammad:

Share