Hausa Global Media

Hausa Global Media Distribution of educative contents for enlightenment and creating awareness.

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐Ÿ๐ŸŽWani hanzari ba gudu ba, mutum ba lallai ya iya gane kansa kai tsaye ba bayan ya duba waษ—annan nauโ€™i...
05/11/2025

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐Ÿ๐ŸŽ

Wani hanzari ba gudu ba, mutum ba lallai ya iya gane kansa kai tsaye ba bayan ya duba waษ—annan nauโ€™ikan na mutane, domin ai tunda ya taso yana yaro ba a waje ษ—aya yake ba, yana zuwa makaranta, ฦ™ila ma har ya gama ya fara sanaโ€™a. Akwai tasirin iyaye, abokai, malamai, irin aikin da ake yi da gogewar rayuwa a tare da shi, ba shakka! Don haka abun yakan ษ—an ษ—auki lokaci wa wasu kafin su gane abubuwan da suke da shi na ษ—abiโ€™a da yake tare da halittarsu, da kuma abubuwan da suke yi a yanzu da a hanya suka koye su.

Daษ—in daษ—awa kuma, kowanne mutum yakan haษ—a ษ“angare biyu ne na nauโ€™ukan. Maโ€™ana za ka iya samun mutum yana da halayen Na-mutane, yana kuma da na Miskili. Ko yana da na Jagora yana kuma da na ฦŠan-baiwa, ko yana da na Miskili da na ฦŠan-baiwa, ko Jagora - Miskili, har zuwa nauโ€™i goma sha biyu (12). Wasu da wuri suke gane inda ya fi rinjaye, wasu kuma sai sun nutsu sosai, yayin da wasu kuma ษ—aya ne ma yake bayyana saboda yanayin da suka taso a ciki.

Wani abu kuma, da rauni da ฦ™arfi na halittar duk za su iya zama baiwar mutum. Ko da kai tsaye rauni bai zama baiwar ba, zai iya zama dalilin da zai sa a gano wata baiwar har a ci moriyarta cikin sauฦ™i fiye da waษ—anda su ba su da wannan raunin.

Don haka ina da fahimtar cewa rauni ba naฦ™asu ba ne, yana zama naฦ™asu ne kaษ—ai idan mutum gaba ษ—aya ya tattara hankalinsa kan abubuwan da ya rasa a rayuwa, har ya gamsar da kansa shi kam ba shi da wata mamora.

Rauni da ฦ™arfi rabo ne da Allah Ya raba wa bayinsa yadda Ya so. Idan ka gane naka sai ka mayar da hankali wajen biyayya wa Allah, kana mai gode masa da niโ€™imar da ya ma, kana kuma amfani da ฦ™arfinka wajen cimma muradunka da manufofinka.

๐˜ผ๐™๐™ข๐™–๐™™ ๐™Ž๐™–๐™ฃ๐™ž
#๐™ƒ๐™–๐™ช๐™จ๐™–๐™‚๐™ก๐™ค๐™—๐™–๐™ก๐™ˆ๐™š๐™™๐™ž๐™–
5/11/2025

05/11/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Babangida Beti, Hassan Lawan, Sadie Sadie, Muhammad Mustapha, Jamilu Safiyanu KT

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ—A ฦ™arkashin wannan nauโ€™ikan ne aka sake fitar da wasu gidajen guda huษ—u, koโ€™ina sun samu biyu. Na yi...
03/11/2025

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ—

A ฦ™arkashin wannan nauโ€™ikan ne aka sake fitar da wasu gidajen guda huษ—u, koโ€™ina sun samu biyu. Na yi ฦ™oฦ™arin ba su sunayen da za su dace da ainihin siffarsu, ba wai fassarar kalma da kalma na yi ba.

๐‘ต๐’‚-๐’Ž๐’–๐’•๐’‚๐’๐’†
Waษ—annan su ne irin mutane masu yoyon magana ษ—in nan, ba sa iya riฦ™e bakinsu, duk inda suka shiga dole sai an san suna wurin, akwai su da haba-haba da mutane, ga su kuma ba su da wuyar sabo da saurin ฦ™ulla abota. Ba su san jimami ba, kuma komai suna iya mayar da shi raha, su dai kawai a yi ta farin ciki koyaushe.

๐‘ฑ๐’‚๐’ˆ๐’๐’“๐’‚
Shi Jagora bai kai โ€œNa-mutaneโ€ surutu ba, shi ma yana da saurin sabo da jamaโ€™a, sai dai shi maโ€™aikaci ne, yana da azama da zummar cimmawa, yana son ya ga yana jagoranci. Yanke abin da zai yi ba ya masa wahala, haka ma yanke wa waninsa, yakan wadatu da kansa, yana da buruka kuma yana tsara yadda zai cimma su. In aiki ya haษ—a ku zai matsa maka, yana ganin in bai yi hakan ba ba za a samu abin da ake so ba.

ฦŠ๐’‚๐’-๐’ƒ๐’‚๐’Š๐’˜๐’‚
Waษ—annan su ne irin mutane ma su basira ษ—in nan, wanda kowa yake mamakin baiwarsu, akwai su da lissafi, sadaukar da kai, da son ganin komai ya cika ษ—ari bisa ษ—ari (100%). Ba su da saurin ฦ™ulla abota amma in suka ฦ™ulla abota da kai ba za su ci amanarka ba, yanayinsu yana saurin canzawa dan haka sun fi duk sauran saurin shiga damuwa. Duk da ba su da surutu amma in suka samu wuri za ka rantse ba su ba ne (ko da kuwa a gaban kyamara ne ko wurin wani taro). Akwai su da tattali da rowa, in an ษ“ata musu rai suna da fushi amma ba kamar โ€œJagoraโ€ ba, su a zuci za su ci gaba da tafarfasa don haka akwai yiwuwar su ษ—auki fansa ma.

๐‘ด๐’Š๐’”๐’Œ๐’Š๐’๐’Š
Su waษ—annan shiru-shirunsu har ya fi na โ€œฦŠan-baiwaโ€ domin ba wani shauฦ™i da za su samu kansu a ciki da zai sa su zama masu surutu, ga zurfin ciki. Da wuya ka ga sun yi fushi ko an ษ“ata musu rai, suna da mugun sauฦ™in kai don haka sun fi sauran daษ—in zama. Suna da kakaci da wasa amma ba su cika dariya ba ko da sun yi kakacin, ba sa wuce iya abun da aka sa su, ba su cika son ษ—aukar nauyin komai ba, sukan jira rayuwa ta zo ta same su maimakon su yi wani hoษ“ษ“asa don gobensu.

Bayan ka gane a wanne kaso kake a cikin waษ—annan mutanen ba shi kenan ba, abun da za ka fara lura da shi shi ne irin ฦ™arfi da raunin halitta da nauโ€™in da kake ciki yake da shi, daga nan za ka fara samun haske kan irin abubuwan da za ka iya yi in ka sa kanka (wato baiwarka da take kwance).

๐˜ผ๐™๐™ข๐™–๐™™ ๐™Ž๐™–๐™ฃ๐™ž
#๐™ƒ๐™–๐™ช๐™จ๐™–๐™‚๐™ก๐™ค๐™—๐™–๐™ก๐™ˆ๐™š๐™™๐™ž๐™–
3/11/2025

01/11/2025

29/10/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Prince Abba, Ahmed Mohammed, Muhammad Mahdi, Abdul Abrash

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ–Kamar yadda na bayyana a littafin Ka San Kanka, akwai ษ—abiโ€™u da mutum yake zuwa duniya da su a matsa...
27/10/2025

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ–

Kamar yadda na bayyana a littafin Ka San Kanka, akwai ษ—abiโ€™u da mutum yake zuwa duniya da su a matsayinsa na shi. Suna kiran wannan da โ€œTemperament theoryโ€. Ban san me za mu kira shi da Hausa ba. Ko ma dai mene ne akwai ฦ™anshin gaskiya a lamarin, duba da cewa akwai hadisi daga bakin maโ€™aiki mai tsira da aminci da yake nuna hakan.

Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi ya ce โ€œ Allah ya halicci Annabi Adamu daga wata damฦ™a da ya yi daga ฦ™asa (a wurare mabambanta), don haka ฦดanโ€™adam an halicce su a gwargwadon haษ—e-haษ—en ฦ™asar. Sai ya zamto a cikin mutane akwai ja, akwai fari, akwai baฦ™i akwai kuma tsaka-tsakin dukkaninsu, akwai mai kyan hali, akwai mai munin hali, akwai mai sauฦ™in lamari, akwai mai wuyar shaโ€™aniโ€ (Abu-dawuda da Tirmizi suka rawaito, kuma sun ce hadisi ne kyakkayawa).

A duk rabe raben da aka yi wa ษ—abiโ€™un mutane da suke zuwa duniya da su, wanda Tim Lahaye ya yi amfani da shi a littafin โ€œWhy you act the way you doโ€ ya fi gamsar da ni, don haka ni ma na kawo shi a littafin โ€œKa san Kankaโ€. A gurguje za mu sake waiwayar dabarun sanin kai da aka kawo a littafin, don mutum ya gane shi waye kafin ya fara tunanin baiwar da yake da ita.

๐™ˆ๐’–๐™ฉ๐’‚๐™ฃ๐’† ๐’Š๐™ง๐’Š ๐’‰๐™ชษ—๐™ช ๐™ฃ๐’†
An kasafta mutane zuwa nauโ€™i biyu, masu surutu da shiga mutane, da masu shiru-shiru da rashin son jamaโ€™a. An raba mutanen ne zuwa wannan kashin duba da inda kowannensu ya fi samun karsashi, kuzari da shauฦ™in yin abubuwan da ya sa a gaba.
Shi mai shiga mutane da son surutu, in ba ya cikin jamaโ€™a gaba ษ—aya a kasalance yake jin sa, sai ya rasa me yake masa daษ—i. Babu wani karsashi ko kataษ“us da za ka gani a tattare da shi. Idan kana son ka gane asalin shi wane ne ka bar shi ya shiga mutane kawai. A taฦ™aice jikinsa yana samun ฦ™arfi daga yadda yake hada-hada da mutane.

A ษ—ayan ษ“angaren kuwa marasa magana da rashin son mutane suna kishiyantar wancan ne. Duk inda mutane ko hayaniya ta yawaita, to kamar ana zuฦ™e musu ฦ™arfinsu ne. Gaba ษ—aya za su ji komai ya gundure su, ba su da wani kuzari, ba sa jin shauฦ™in yin komai har sai sun samu sun keษ“ance. Kafin ka saba da su ko su saba da kai sai kana da haฦ™uri sosai.

๐‘จ๐’‰๐’Ž๐’‚๐’… ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š
27/10/2025
#๐‘ฏ๐’‚๐’–๐’”๐’‚๐‘ฎ๐’๐’๐’ƒ๐’‚๐’๐‘ด๐’†๐’…๐’Š๐’‚

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ•Kai wane ne?Ko ban faษ—a ba, na sa mai karatu zai yi tunanin lallai akwai alaฦ™a tsakanin mutum da bai...
25/10/2025

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ•

Kai wane ne?

Ko ban faษ—a ba, na sa mai karatu zai yi tunanin lallai akwai alaฦ™a tsakanin mutum da baiwarsa. Kamar yadda kake a duniya babu irin ka, haka ma za ka samu a irin tarin baiwar da Allah ya ma, babu wanda ya haษ—a masa irin su sak. Kenan sanin kai wane ne, ฦ™arfi da rauninka na halitta, inda ka taso da irin iliminka, tarbiyyar da aka ma da gwagwarmayar da ka sha a rayuwa zai ba ka damar gane irin baiwar da kake ษ—auke da ita, da yadda za ka amfanu da ita.

Wasu suna mamaki in aka ce kowanne mutum kafin a samu irinsa abun da wahala. Abun ba kamar ษ—aukar dala ba gammo ba ne, bari na muku bayanin me suke nufi.

Ka ษ—auka cewa mahaifinka su biyar (5) iyayensu suka haife su. Shi kuma kakanka su huษ—u ne a gidansu misali, shi kuma babansa su 3 ne a gidansu misali. Ko ba mu je da nisa ba, ka san da baban kakanka ya tashi aure, ba mata ษ—aya suka aura da sauran ฦดan uwansa ba, kenan ita ma matar ta fito daga wani tsatso, za ta zo da irin halayenta. To haka shi ma kakanka, matarsa daban da sauran ฦดan gidansu, haka shi ma ฦดaฦดansa kowa ya auri mace daban. Kar ka manta, matan da suke aura ba su da alaฦ™a da iyayensu mata, a can wani dangin ne suke samo su. Lura da wannan misalin kana ganin zai yiwu a danginku a samu irinka sak?

A zo ga batun gidanku, kowa yana ษ—auko hali da ษ—abiโ€™un wani a dangin iyaye guda biyu. Don haka za ka ga wani yana da surutu, wani ba shi da shi, wani yana yawan ฦ™arya, wani kuma gaskiya kawai ya iya fada, wani dogo, wani gajere, wani siriri, wani lukuti. Ko da ฦดan biyu da suka fito cibiya ษ—aya, za ka samu akwai bambancin halaye. Akwai wasu ฦดan biyu da na sani a unguwarmu (lokacin da nake Hotoro, Kano), ษ—aya sikila aka haife shi, ษ—ayan kuma lafiyarsa lau.

Idan mun fahimci wannan, za mu gane cewa lallai kowanne mutum da wahala a samu irinsa sak. Masu bincike suna cewa kusan kowa da yake duniya, ษ—aya ne cikin mutum biliyan ษ—ari 400. Maโ€™ana in da za a tattara mutane a yi ta zaฦ™ulawa, za a iya irga biliyan ษ—ari huษ—u (400) kafin a iya samun wani irinka, da zai zo a zamaninka, kamanninka, halayenka, iliminka, da sauransu. Lallai abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, mutum nawa ne ma yanzu a duniyar gaba daya?

๐‘จ๐’‰๐’Ž๐’‚๐’… ๐‘บ๐’‚๐’๐’Š
25/10/2025
#๐‘ฏ๐’‚๐’–๐’”๐’‚๐‘ฎ๐’๐’๐’ƒ๐’‚๐’๐‘ด๐’†๐’…๐’Š๐’‚

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ”Zan iya barin mai karatu cikin ruษ—ani idan na katse wannan babin a nan ba tare da ba da misalan baiw...
19/10/2025

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ”

Zan iya barin mai karatu cikin ruษ—ani idan na katse wannan babin a nan ba tare da ba da misalan baiwa ba. Idan muka koma kan maโ€™anar baiwa, za mu lura cewa ษ“angare biyu ce, abun da ake yi cikin sauฦ™i ba tare wata hoษ“ษ“asa ba, da abun da za a iya yi cikin sauฦ™i in an samu horo ko da kaษ—an ne. Kenan za mu iya cewa, baiwa akwai wacce ake ganinta zahiri (ta fili), akwai kuma wacce take kwance, sai an motsa ta ta bayyana.

Baiwar fili: misali, baiwar samarwa, baiwar ฦ™irฦ™ira, baiwar kwaikwayo, baiwar harshe, baiwar wasanni, baiwar ingantawa, baiwar ganowa, baiwar aikin hannu, baiwar jagoranci, baiwar kimiyya, baiwar rubutu, baiwar zane, baiwar hulษ—a da jamaโ€™a, baiwar mallakar kai, baiwar gamsarwa, baiwar lissafi, hadda, saurin koyo, da sauransu.

Wasu suna iya shiga cikin wasu, misali mai samarwa zai iya samarwa ta hanyar aikin hannu, ko ta hanyar rubutu ko zane ko ma kwaikwayo da sauran su.

Baiwar kwance: misali, iya shugabanci, tara ilimi, gane alaฦ™a tsakanin abubuwa, kazar-kazar da rashin kasala, gwada abubuwa da yawa, warware matsala, saurin sajewa, da sauransu. Wasu ma daga siffar mutum ne, kamar dogon mutum akwai yiyuwar ya iya wasannin gudu, mai babbar murya, akwai yiyuwar ya iya jan ragama ko gamsar da mutane. Duk wani abu da aka lura cewa in mutum ya samu horo zai gawurta a wani fanni na rayuwa, to suna nan ษ“angaren.

Baiwar fili kuma takan taka rawa wajen nuna wata kwancacciyar baiwa. Wani za ka samu ba ya magana, ko yana da jin kunya, amma kuma akwai yiyuwar in ya samu horo ya zama jagora a gaba saboda wasu abubuwan da yake da su.

Ina fatan mai karatu ya fahimci baiwa, sannan ya gamsu kowa yana da ita. A babukan da za su biyo baya, za mu ga yadda ake gano baiwa, yadda ake rainonta da ma yadda za a ci moriyarta, mu je zuwa.

๐˜ผ๐™๐™ข๐™–๐™™ ๐™Ž๐™–๐™ฃ๐™ž
19/10/2025
#๐™ƒ๐™–๐™ช๐™จ๐™–๐™‚๐™ก๐™ค๐™—๐™–๐™ก๐™ˆ๐™š๐™™๐™ž๐™–

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ“๐‘ป๐’‚ ๐’š๐’‚ ๐’›๐’‚ ๐’‚ ๐’‡๐’Š๐’•๐’‚ ๐’…๐’‚๐’ˆ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’‰๐’–๐’ ๐’•๐’–๐’๐’‚๐’๐’Š ๐’–๐’Œ๐’–๐’ ๐’๐’‚๐’?Dr Myles Munroe a cikin littafin โ€œUnderstanding Your Pote...
14/10/2025

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ“
๐‘ป๐’‚ ๐’š๐’‚ ๐’›๐’‚ ๐’‚ ๐’‡๐’Š๐’•๐’‚ ๐’…๐’‚๐’ˆ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’‰๐’–๐’ ๐’•๐’–๐’๐’‚๐’๐’Š ๐’–๐’Œ๐’–๐’ ๐’๐’‚๐’?

Dr Myles Munroe a cikin littafin โ€œUnderstanding Your Potentialโ€ ya buga wani misali da iri (na shuka) da nake ganin zai mana amfani wajen gane kowa yana da baiwa. Idan aka ba ka iri kafin a shuka shi ka san lallai iri ne guda daya a ka ba ka. Amma in aka shuka wannan irin fa? Allah ne kaษ—ai ya san ฦดaฦดa nawa zai haifar.

Kamar yadda wannan irin kafin a shuka shi ake masa kallon iri ฦ™waya ษ—aya kawai, amma Allah ya masa baiwar in an shuka shi zai haษ“aka ya ba da ninkin ba ninkin nasa. Haka nan kowanne mutum yake, yana da wani abu da aka halicce shi da shi, da shi ba lallai ya gane ba, watakila ma yana aiki da shi ba tare da ya sani ba, har sai ranar da aka hora shi (shuka shi) a ka masa ban ruwa da sauran abubuwan da za su tatso baiwar har a ci moriyarta.

Wanda yake tunanin baiwa ษ—aya gare shi, to ya duba rayuwarsa, a cikin me ya taso? Ina da ina ya shiga? Me da me ya gwada? Idan duk amsoshin tambayoyin nan zuwa abu guda suke kai shi, to alama ce da take nuna masa ba shi da hurumin cewa ba shi da baiwa a wasu abubuwan tunda bai taษ“a gwadawa ba. Kamar yadda ba ma iya bambance abincin da muka fi so idan kullum tuwo muke ci, haka ba ma iya gane wuraren da muke da baiwa in abu ษ—aya muke ta yi kaf rayuwarmu.

Wanda kuwa matsalarsa ita ce ganin baiwarsa tana cikin abubuwan da suka saษ“a wa addini da alโ€™ada. To lallai wannan yana munana tunani game da Ubangiji. Allah maษ—aukaki ya halicci mutane a kan yin rayuwa yadda ya dace, sai dai wurin da suka taso (muhalli) ya musu tasiri su sauฦ™a daga layi. Don kuษ“uta daga wannan tunanin, matakin farko mutum ya watsar da wannan tunanin, na biyu ya nemi sanin addini daidai gwargwado, na uku ya yi ฦ™oฦ™arin siffantuwa da kunya, na huษ—u ya gwada wasu abubuwan.

Asalin baiwa ba aiki ba ce, wani abu ne da kake da shi a kwance a jikinka, ganin damarka ne ka san da wanne irin aiki za ka motsa shi. A misalin da na ba ku a baya, na wanda aka hana waฦ™a, bayan matashin ya bar waฦ™a sai ya koma sanaโ€™ar ษ—inki. Cikin ฦ™anฦ™anin lokaci ya naฦ™alci ษ—inki ya goge, har aka yaye shi ya kafa nasa. Ashe Allah ya masa baiwa a fannin ฦ™irฦ™ira da ingantawa (creativity da innovation) ba tare da ya sani ba ya je ya sa ta a waฦ™a. Idan kai ma kana cikin wannan halin to kar ka kalli aikin da kake yi, ka kalli mene ne tun farko ya kai ka ga shaโ€™awar yin abun. Ta haka ne za ka gane wacce baiwarka ka ษ—auka ka sa a cikin aikin. Hakan zai ba ka damar juya akalar baiwar zuwa inda za a ci moriyarta.

๐˜ผ๐™๐™ข๐™–๐™™ ๐™Ž๐™–๐™ฃ๐™ž
#๐™ƒ๐™–๐™ช๐™จ๐™–๐™‚๐™ก๐™ค๐™—๐™–๐™ก๐™ˆ๐™š๐™™๐™ž๐™–
14/10/2025

    7/9/2025
07/10/2025


7/9/2025

01/10/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Saifullahi M Dawood, Sunusi Tukur Jami I, Idris Abdullahi Auwalu, Najib Abubakar Yusuf, Mubarak Al-Hameedy

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ’๐™ˆ๐™š๐™ฎ๐™–๐™จ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™จ๐™ช ๐™จ๐™ช๐™ ๐™š ๐™œ๐™–๐™ฃ๐™ž๐™ฃ ๐™—๐™–๐™ž๐™ฌ๐™–๐™ง๐™จ๐™ช ๐™– ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™™๐™– ๐™–๐™ ๐™š ฦ™๐™ฎ๐™–๐™ข๐™– ๐™ฃ๐™š?Wannan matsalar ta zama ruwan dare sosai a ci...
30/09/2025

๐ˆ๐ง๐š ๐๐š๐ข๐ฐ๐š๐ญ๐š ๐“๐š๐ค๐ž? ๐ŸŽ๐Ÿ’

๐™ˆ๐™š๐™ฎ๐™–๐™จ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™จ๐™ช ๐™จ๐™ช๐™ ๐™š ๐™œ๐™–๐™ฃ๐™ž๐™ฃ ๐™—๐™–๐™ž๐™ฌ๐™–๐™ง๐™จ๐™ช ๐™– ๐™–๐™—๐™ช๐™ฃ ๐™™๐™– ๐™–๐™ ๐™š ฦ™๐™ฎ๐™–๐™ข๐™– ๐™ฃ๐™š?

Wannan matsalar ta zama ruwan dare sosai a cikin mutane. Misali akwai wani a danginmu da nake yawan misali da shi, ya taso da shaโ€™awar yin waฦ™e-waฦ™e, har ta kai ya fara waฦ™oฦ™in zambo da habaici. Daga baya Allah ya taimake shi mahaifiyarsa ta hana shi waฦ™a, kuma ya ji maganarta ya daina ya kama wata sanaโ€™ar.

Mutane da dama suna samun kansu a irin wannan halin a ma fi yawancin lokuta ne a dalilin rashin samun mafaษ—i, wato ฦ™arancin tarbiyya daga gida. Idan mutum ya taso da tarbiyya akwai abubuwan da ma ba ya tunanin yi, in ma ya yi za a taka masa birki. Wanda na ba da misali da shi da ba shi da tarbiyyar da in an taka masa birki zai bari da wataฦ™ila har yanzu yana waฦ™a.

Wasu kuma addini ne bai ratsa su ba, suna ganin cewa ai wannan ba wani abu ba ne don na yi kaza da kaza, wasu ma na ganin shi ne wayewa, in ka ce musu ba kyau ma sai su ฦ™aryata ka. Sun gamsu da abun da hankalinsu da tunaninsu ya kimsa musu. Suna kuma tunanin to in aka hana su yin amfani da baiwarsu ya za su yi da rayuwarsu?

Wasu kuma ba a taso da su a kan wani abu da manufa ba ne, kawai an sake su haka ne suna rayuwarsu, duk abun da suka ga ana yayinsa a dandalin sada zumunta sai su ma kawai su ara su yafa, kafin su ankara sun faษ—a mummunan hannu. Tun ba sa samun kuษ—i har su kai ga an buษ—e musu yadda ake yi a samu kudi a wannan harkar, daga nan sai mutum ya afka ciki, ya yi nisa, ya daina jin kira, har ya fara tunanin ma hassada ce ake masa.

๐˜ผ๐™๐™ข๐™–๐™™ ๐™Ž๐™–๐™ฃ๐™ž
#๐™ƒ๐™–๐™ช๐™จ๐™–๐™‚๐™ก๐™ค๐™—๐™–๐™ก๐™ˆ๐™š๐™™๐™ž๐™–
30/9/2025

Address

Hotoro Rakad
Kano
700223

Telephone

+2348081193491

Website

https://hausaglobalmedia.com.ng/, https://youtube.com/@hausaglobalmediatv130, http

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Global Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa Global Media:

Share

Category