02/10/2025
Dakatar da Malam Lawan Triumph: Matakin doka ne ba zalunci ba – Ambassador Karibu Kabara
Ambassador Karibu Yahaya Lawan Kabara, wanda shi ne Chief Executive Officer kuma National Director General na Kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Global Community for Human Rights Network, ya bayyana matsayinsa kan batun dakatar da Malam Lawan Abubakar da kwamitin shura na jihar Kano ya yi.
Ambassador Kabara, wanda ke kula da ofishin ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam a yankin Afirka, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Doha babban birnin Qatar.
Kabara yace Matakin da kwamitin shura na jihar Kano ya ɗauka akan Malam Lawan Abubakar ya yi daidai, kuma yana tafiya akan doka da oda don tabbatar da kwanciyar hankali a jihar Kano.
Ya kara da cewa, duk da cewa Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗan kasa ’yancin fadin albarkacin baki, Sashe na 45 ya tanadi iyaka ga wannan yanci, musamman idan furucin na iya haddasa tashin hankali, firgici, ko karya zaman lafiya a jihar ko kasar baki ɗaya.
“Ba a amince da cin zarafi ko tabarbarewar martabar manyan mutane da al’umma ke bi da su ba, musamman ma Annabi (SAW) wanda yake da mabiya miliyoyi a fadin duniya.”
Ya jaddada cewa wannan mataki na gwamnati ya dace domin tabbatar da zaman lafiya, musamman ganin zarge-zargen da ake yi wa Malam Lawan Abubakar na taba martabar al’umma da addini.
“Ya k**ata Malam Lawan Abubakar ya samu damar kare kansa a kotu. Idan an tabbatar da zargin da ake masa, to ya ɗauki hukuncin da ya dace. Amma idan ba a same shi da laifi ba, to ya k**ata a sake shi.”
A ƙarshe, Ambassador Kabara ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta tsaurara matakai wajen tsara dokokin wa’azi a jihar, domin kowane malami ya gudanar da huduba cikin bin doka, tare da kauce wa fitina da tabbatar da zaman lafiya tsakanin ƙungiyoyi daban-daban.