Fatika TV Hausa

Fatika TV Hausa Ku tuntuɓe mu kai tsaye ta Whatsapp no:+2349043985471. EDUCATIVE,ENLIGHTEN AND ENTERTAINMENT PROGRAMMES

FATIKA TV HAUSA, Shafi ne da aka samar dashi a ranar 01 ga watan Janairu 2026 don wallafa Sahiha Labarai da Rahotanni, shirye shirye masu Ilimantarwa da Nishadantarwa a cikin harshen Hausa.

Sabon jakadan Nijeriya a Sudan ya gabatar da takardar k**a aiki a ƙasar Sabon jakadan Nijeriya a Sudan, Yakubu Nyaku Dan...
31/08/2026

Sabon jakadan Nijeriya a Sudan ya gabatar da takardar k**a aiki a ƙasar

Sabon jakadan Nijeriya a Sudan, Yakubu Nyaku Danladi, ya gabatar da takardar shaidar aikinsa ga shugaban majalisar mulkin Sudan ta wucin gadi, Janar Abdalfattah Al-Burhan Abdalrahman, a fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum k**ar yadda gidan talabijin na NTA News ya ruwaito.

source:dcl Hausa/ Fatika Yv Hausa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shigar da ƙara gaban kungiyar tarayyar Afirka (AU) kan hare-haren ƙyamatar baƙi da ke f...
31/08/2026

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shigar da ƙara gaban kungiyar tarayyar Afirka (AU) kan hare-haren ƙyamatar baƙi da ke faruwa a Afirka ta Kudu

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa shugaban ya bukaci kungiyar ta dauki matakin gaggawa don kawo karshen wannan damuwa.

An kashe Naira biliyan 37.64 kan tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu cikin shekaru uku - RahotoBinciken bayanan kashe kuɗin gw...
31/08/2026

An kashe Naira biliyan 37.64 kan tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu cikin shekaru uku - Rahoto

Binciken bayanan kashe kuɗin gwamnati ya nuna cewa fadar shugaba Tinubu ta kashe Naira biliyan 37.64 cikin shekaru uku wajen tafiye-tafiyen cikin gida da na ƙasashen waje.

Bayanan, waɗanda GovSpend, mai sa ido kan kashe-kashen kuɗaɗen gwamnati a Nijeriya ta fitar, sun shafi tafiye-tafiyen shugaban ƙasa daga watan Yunin 2023 zuwa Afrilun 2026, k**ar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai an gaza samun ji daga bakin Bayo Onanuga da Daniel Bwala kan wannan batu, duk da yunkurin tuntubar su a lokacin hada wannan rahoto.

Tashar Fatika TV Hausa a koda yaushe mun tsaya tsayuwar daka domin al'umma, ta hanyar yaƙi da labaran karya, koyar da al...
31/08/2026

Tashar Fatika TV Hausa a koda yaushe mun tsaya tsayuwar daka domin al'umma, ta hanyar yaƙi da labaran karya, koyar da al'umma ilimin gami da nishaɗi a koda yaushe.

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa Najeriya ce ke kan gaba a fannin zuba jarin mai da iskar gas a Afirka, wanda jimillars...
31/08/2026

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa Najeriya ce ke kan gaba a fannin zuba jarin mai da iskar gas a Afirka, wanda jimillarsa ta kai dala biliyan 221 a faɗin nahiyar.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke faɗi-tashin neman ingantaccen mak**ashi, lamarin da ke sake tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin jagorar fannin mak**ashi a Afirka.

Rahoton wanda kamfanin binciken mak**ashi na Industrial Info Resources ya fitar, ya nuna cewa a halin yanzu ana bin diddigin manyan ayyukan samar da mai da iskar gas sama da 800 a ƙasashen Afirka daban-daban.

Wannan rahoto ya nuna yadda manyan kamfanonin ƙetare ke ci gaba da amfani da albarkatun makashin da nahiyar ke da su, duk da kiraye-kirayen da ake yi na komawa ga mak**ashin da baya gurɓata muhalli.

Najeriya na sa ran samo sabbin hannayen jarin da ya kai tsakanin dala biliyan 30 zuwa biliyan 50 nan da shekara ta 2030, ta hanyar manyan ayyukan hakar mai da iskar gas har guda 22 a cikin teku

Ana sa ran wadannan ayyukan za su taimaka wa Najeriya wajen cimma burinta na samar da tataccen mai har ganga miliyan 3 a kowace rana nan da shekara ta 2030.

Tottenham ta tuntuɓi AC Milan kan ɗanwawasan Amurka mai shekara 27 Christian Pulisic. (Teamtalk)Liverpool da Everton na ...
31/08/2026

Tottenham ta tuntuɓi AC Milan kan ɗanwawasan Amurka mai shekara 27 Christian Pulisic. (Teamtalk)

Liverpool da Everton na son ɗanwasan Stuttgart Jamie Leweling, mai shekara 25, yayin da ita ma Roma ke son ɗanwasan na Jamus. (Patrick Berger, external/Sky Sport Germany)

Newcastle na son cimma yarjejeniya kan ɗanwasan gaba na Lille Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21, amma babu wani cigaba a tattaunawa kan ɗanwasan na Belgium. (Florian Plettenberg)

Everton na koƙarin sake karɓo aron ɗanwasan Man City da Ingila Jack Grealish. (Athletic)

Crystal Palace ba ta son rabuwa da golanta Dean Henderson, mai shekara 29, bayan Nottingham Forest ta nuna tana so. (Mail - subscription required)

Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, jam’iyyu da ’yan siyasa na ƙara shirye-shiryen neman goyon bayan al’umma.Ku fa, wa ...
30/08/2026

Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara matsowa, jam’iyyu da ’yan siyasa na ƙara shirye-shiryen neman goyon bayan al’umma.

Ku fa, wa kuke ganin ya fi cancanta ya zama shugaban Najeriya a 2027?

Rubuta sunan ɗan takararka a comment section

Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya soki tafiyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya y...
30/08/2026

Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya soki tafiyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi zuwa nahiyar Turai domin hutu na tsawon makwanni uku, yana mai bayyana matakin a matsayin rashin kyakkyawan shugabanci a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsanancin halin ƙunci da rashin tsaro.

Atiku ya bayyana haka ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa yayin da miliyoyin 'yan Nijeriya ke tsaka da fama da matsin rayuwa ta yadda ba sa iya yin tafiya, shugabansu kuwa yana can yana shawagi a sararin samaniya.

Babu gaskiya a cikin wannan lamari, karyace tsagwaranta, muna nan daram. Kamafan opay ya fitar gaskiya labarin dake yawo...
30/08/2026

Babu gaskiya a cikin wannan lamari, karyace tsagwaranta, muna nan daram.

Kamafan opay ya fitar gaskiya labarin dake yawo a shafukan sada zumunta, na cewar kamfanin zai dakatar da ayyukan sa tare da umartan duk masu amfani da bankin dasu kwashe kuɗaɗen su kafin ranar 1 ga saptamba 2026 da zamu shiga , inda kamfanin ya sanar da cewa babu gaskiya a cikin wannan labari.

Ya kukaji a lokacin da kuka tsinkayi wannan labarin?

Za mu amfana da yarjejeniyar ɗanyen mai da muka ƙulla da Amurka - Shugabar Venezuela.Shugabar riƙon ƙwarya a Venezuela, ...
30/08/2026

Za mu amfana da yarjejeniyar ɗanyen mai da muka ƙulla da Amurka - Shugabar Venezuela.

Shugabar riƙon ƙwarya a Venezuela, Delcy Rodriguez, ta ce yarjejeniyar man fetur da ƙasarta ta ƙulla da Amurka, wadda aka sanar a ranar Asabar, za ta tabbatar da ci gaba da ikon Venezuela kan albarkatun ƙasarta.

Fatika TV Hausa

Address

Dorayi
Kano
700241

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fatika TV Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Fatika TV Hausa:

Shortcuts

Share