Map Magazine TV

Map Magazine TV Map magazine TV is a Television and Magazine station on internet, we broadcast programs in Hausa language. GOMBE

KEDCO na barazanar katse wutar Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano kan bashi na Naira miliyan 949.88
15/09/2025

KEDCO na barazanar katse wutar Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano kan bashi na Naira miliyan 949.88

🚨EFCC ta tsare tsohon shugaban kamfanin mai na ƙasa Mele Kyari. Kyari ya isa hukumar da ƙarfe 2:15pm kuma yana amsa tamb...
10/09/2025

🚨EFCC ta tsare tsohon shugaban kamfanin mai na ƙasa Mele Kyari.

Kyari ya isa hukumar da ƙarfe 2:15pm kuma yana amsa tambayoyi kan batun satar kuɗaɗe lokacin shugabancinsa a NNPC.

Badakalar Dala Biliyan 7.2 ta gyaran matatun mai ita ce kan gaba cikin batutuwan da ake matsa Kyari akai.

NasaraRadio

Da Dumi Dumi Babban layin wutar lantarki na Nijeriya ya sake tsayawa
10/09/2025

Da Dumi Dumi

Babban layin wutar lantarki na Nijeriya ya sake tsayawa

Wannan Ita Ce Hanyar Mahaifar Ministan Sufuri Na Najeriya Sa'idu Ahmed Alkhali Wannan ita ce hanyar Dukku zuwa Gombe wad...
09/09/2025

Wannan Ita Ce Hanyar Mahaifar Ministan Sufuri Na Najeriya Sa'idu Ahmed Alkhali

Wannan ita ce hanyar Dukku zuwa Gombe wadda ta ɗauki lokaci mai tsawo ana fama da matsalar amma an kasa gyarawa, tun Ministan ya na Sanata a mazabar Gombe ta Arewa.

A halin yanzu suna da Ɗan Majalisa Wakilai mai wakiltar Dukku/Nafada Hon. El-rasheed Abdullahi Kelly, amma duk da haka an kasa magance wannan matsalar.

Shin a ganin ku me ya jawo hakan?

Daga Shafin Rariya

Akwai yuwu war Nan bada jimawa ba Tinubu ya fara ciwo bashi Daga opay ko monie point Inji Barr Dino melayo
09/09/2025

Akwai yuwu war Nan bada jimawa ba Tinubu ya fara ciwo bashi Daga opay ko monie point

Inji Barr Dino melayo

08/09/2025

Tattaunawa Da Shugaban Asibitin kwararru na jihar Gombe Dr Sambo (specialist Hospital) Wanda yayi bayani Game Da Zargin Da sowore yayi na Lalacewar Harkar kiwon Lafiya

Ayi sauraro Lafiya

Tunda Allah Ya Sa Mun Fafata Da Ƴan Bìndìģà Kuma Sun Ji Wuta, Har Suna Neman Sulhu, To A Shirye Muke Mu Yi Sulhu Da Su, ...
08/09/2025

Tunda Allah Ya Sa Mun Fafata Da Ƴan Bìndìģà Kuma Sun Ji Wuta, Har Suna Neman Sulhu, To A Shirye Muke Mu Yi Sulhu Da Su, Kuma Sulhu Na Ainahin Gaskiya Da Gaskiya Ba Na Ƙarya Ba, Inda Za Mu Tallafawa Waɗanda S**a Cutar, Shima Wanda Ya Karɓi Sulhun Gwamnati Ta Tallafa Masa, Cewar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

JERIN SUNAYE: Jihohin Sokoto da Bayelsa da Gombe sun fi yawan matalauta a kididdigar da jaridar TheCable ta wallafa.Kidi...
08/09/2025

JERIN SUNAYE: Jihohin Sokoto da Bayelsa da Gombe sun fi yawan matalauta a kididdigar da jaridar TheCable ta wallafa.

Kididdigar ta bayyana cewa 9 cikin mutane 10 na mazauna Jihar Sokoto talakawa ne.

Ga yadda jerin jihohin ya ke bisa matakin talaucin su.

1. Sokoto: 90.5%

2. Bayelsa: 88.5%

3. Gombe: 86.2%

4. Jigawa: 84.3%

5. Plateau: 84%

6. Yobe: 83.5%

7. Kebbi: 82.2%

8. Taraba: 79.4%

9. Ebonyi: 78%

10. Zamfara: 78%

11. Cross River: 75.4%

12. Benue: 75%

13. Bauchi: 73.9%

14. Kaduna: 73.9%

15. Katsina: 72.7%

16. Borno: 72.5%

17. Akwa Ibom: 71.3%

18. Neja: 69.1%

19. Adamawa: 68.7%

20. Ogun: 68.1%

21. Kano: 66.3%

22. Enugu: 63.1%

23. Ribas: 62.4%

24. Kogi: 61.3%

25. Nasarawa: 60.7%

26. Oyo: 48.7%

27. Kwara: 48.3%

28. FCT: 48.3%

29. Delta: 47.6%

30. Imo: 40.7%

31. Osun: 40.7%

32. Ekiti: 36%

33. Edo: 35.4%

34. Anambra: 32.1%

35. Abia: 29.8%

36. Legas: 29.4%

37. Ondo: 27.2%



Hukumar kula da sufurin jiragen sama za ta fara bayyana sunayen kamfanonin da ke karya ka'idojinta a Najeriya
08/09/2025

Hukumar kula da sufurin jiragen sama za ta fara bayyana sunayen kamfanonin da ke karya ka'idojinta a Najeriya

Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen jihar Kano ta sanar da korar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓ...
06/09/2025

Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen jihar Kano ta sanar da korar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin aikata zagon ƙasa ga jam’iyya da kuma rashin biyan kuɗin jam’iyya.

Shugaban NNPP a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa ’yan jarida jawabi ranar Asabar, inda ya ce wannan hukunci ya biyo bayan fitowar da Kofan ya yi a kafafen watsa labarai da dama yana sukar jam’iyyar da shugabanninta.

DA DUMIDUMINSA: Za Mu Bayyana Sùnàyèn Masu Aĺàkà Dà Ƴan Bìnďìiga Da Masu Amfàni Tà'àďdañçi Wajen Cimmà Manufar Sù Tà Siy...
05/09/2025

DA DUMIDUMINSA: Za Mu Bayyana Sùnàyèn Masu Aĺàkà Dà Ƴan Bìnďìiga Da Masu Amfàni Tà'àďdañçi Wajen Cimmà Manufar Sù Tà Siyasa, Inji Dan Bello

Me za ku ce?

Zan iya kawo ƙarshen ƴan bindiga cikin watanni biyu – Gwamnan ZamfaraGwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa...
04/09/2025

Zan iya kawo ƙarshen ƴan bindiga cikin watanni biyu – Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa yana da ƙarfin kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga a cikin watanni biyu idan aka ba shi cikakken iko kan hukumomin tsaro.

Gwamnan, wanda ya fashe da kuka yayin da yake bayyana hare-haren kwanan nan a cikin wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, ya ce babban cikas wajen kawo ƙarshen wannan rikici shi ne dakarun tsaro a Zamfara suna ci gaba da karɓar umarni daga Abuja maimakon daga gwamnatin jihar.

Lawal ya jaddada cewa da sanin da yake da shi game da yankin da kuma wuraren da shugabannin ƴan ta’adda suke, zai iya kawo ƙarshen wannan fitina cikin gaggawa idan aka ba shi dukkan ikon da ake bukata.

Address

Al Hamsad Tower Opp ShopRite Zoo Road
Kano
00076

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Map Magazine TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Map Magazine TV:

Share