
28/09/2025
DA DUMI-DUMI: An kori Rev. Sister Kinse bayan ta fallasa, Fastoci da shuwagabannin coci na kwana da su
Rev. Sister Annastasia Kinse ta zargi wasu firistoci da shugabannin coci da zaluntar ‘yan’uwa mata (nuns), tana mai cewa "mu ba matan ku ko masoyanku ba ne, mata ne na Allah" wannan zargi nata ya jawo cece-kuce wanda, har kungiyar “Congregation of Mother of Perpetual Help” ta sallame ta, ta kuma ba ta Naira dubu ₦100,000 tare da kwace rigar addininta.
Sister Kinse ta ce duk da hakan, tana nan a matsayin Katolika mai kishin addininta "amma dai ba zata ki fallasa gaskiya ba"
A ganim ku ya dace a kore ta saboda ta yi fallasa?