27/09/2023
Ilimin Hacking (Kutse)
Gare ku masu son zama hackers.
Kamar yadda nake fada maku shima fa hacking
ilimi ne wanda sai ka koya zaka iya, bawai cika
baki da hacking din Facebook account din mutane
shine hacking ba, wannan kawai dai kana trying
amma ba shine ainahin duniyar hacking ba.
Bari kuji; idan kanaso ka zama shahararren
hacker to fa sai ka tsunduma wajen karantar
bangaren dan'uwa, kuma idan ka koya ka iya to
ya zama hanyar da zaka dinga taimakon
Addininka, basai na maku dogon bayani ba
kungane abinda nake nufi.
Wato kwarewa a hacking yana buqatar ka maida
hankali bangaren koyon wadannan abubuwan da
zan lissafo guda 10 yanzu in sha Allah, wadanda
idan ka iya su to lallai ka tabbata shahararren
hacker.
1. Intermediate Computer Skills; wato yanada
kyau ace ka iya kirkirar Word documents ko kuma
kana iya surf din web, sannan dole ya kasance
kasan yadda zaka dinga amfani da mabanbantan
Commands Lines na Windows, ka iya seta
network, sannan ka iya Editing din Registry din
Computer dinka.
2. Good Networking Skills; wato yawancin
hackers sunfi yin ta'adi a Online sunfi yin barna a
saman yanar gizo dan haka dole ka koyi ilimin
Networking da Terms dinsa k**ar irinsu;
• WEP versus WPS password
• NAT
• MAC Addresses
• Routers
• Ports
• VPN
• IPv6
• DNS
• Subnetting
• DHCP
• Private and public IPs
• Ipv4
• OSI Modelling
• Packets
• TCP/IP
3. Using a Linux operating system; yawancin
hackers sunfi amfani da "Linux OS" saboda tana
barin programs da tweaks a windows da kuma
Mac operating system. Yawancin hacking tools
din sunfi aiki acikin wannan operating system din.
4. Virtualization; kafin ka fara qoqarin yin hacking
farko kafara sanin menene zakayi kuma ka
tabbatar komai kanayin shi akan tsari batareda
kuskure ba, kwararren hacker baya barin kuskuren
da za'a k**ashi, idan kasamu kwarewa kanaso
ka jaraba baiwar naka to karka ce zaka fara da
babban aiki, kafara jarabar Hacking dinka ga
qaramin abu haka, k**ar "Virtualization Software
package" k**ar irinsu; VMWare Workstation.
Wajen amfani da Virtual Workstation hakan zai
baka damar kayi gwajin fikirarka ta hacking
batareda wani hadari ma kuma batareda ka jawo
wa computer dinka wata matsalar ba ko lalace
wa, sbd idan kana koyo kace zakayi hacking din
wani abun bayan baka kware ba to Ido zai raina
fata domin kana iya lalata computer dinka.
5. Tcdump or Wireshark; shi dai Tcdump anfi
saninsa da Command Line Protocol analyser ko
kuma kace Sniffer duk sunansa ne Tool ne na
hacking mai dan bala'in sata. Shi kuma Wireshark
yawanci mutane sunsan shi shima aikinshi iri
daya da Tcdump.
6. Knowledge of security Technologies and
concepts; lallai duk hacker yanada buqatar mafi
muhimmanci acikin Concept and technologies
wanda yake da alaqa da information technology.
Saboda haka yanada kyau kasan Wireless
Technology And Concepts irinsu; "Secure Sockets
Layer" (SSL) Firewalls, Intrusion Detection
System (IDS), Public Key Infrastructure (PK) da
sauransu.
7. Scripting Skills; kasamu damar iya kirkira da
editing din Scripts hakan zai baka damar ka iya
kirkirar naka Tool din, ta yadda zaka zama
Independent! Kana harkarka ba ruwanka da
amfani da tools din wasu, zaka kirkiri kayan aikin
da ba kowa yasanta ba kayi amfani da abinka
wurin kai hari, to idan kanaso ka kware wajen
hakan dole ka maida hankali wajen karantar
Scripting language k**ar irinsu; Ruby on rails, ko
kuma Python.
8. Database Skills; idan kanason kasan yadda
hackers suke kutse su fada cikin rumbun adaba
bayanan mutane ko kuma kanaso ka iya hakan to
yanada kyau kasan shi yaya ma database din
take aiki da sauransu, dan haka yanada kyau ka
samu kwarewa a "Database management system"
k**ar irinsu; Oracle, ko MySQL.
9. Reverse Engineering; shi wannan zai baka
damar ka iya converting piece na malware ko
kuma mai k**a da Exploit into more advanced
hacking tool.
Daga lokacin da ka fahimci yadda "malware da
exploit features suke aiki to tabbas kasamu
damar gane yadda ake cikakken hacking din
computer.
10. Cryptography; wannan skill din yana baka
damar kasan yadda hacker suke samun damar
boye kansu idan zasuyi barna ko ta'asa a wani
wuri to zaka iya gane yadda suke batar da sawu
kaima kuma zaka iya koya, sannan zai baka
damar gane mabanbantan weakness algorithm
wadanda ake amfani dasu wajen Decrypting
Personal information k**ar irinsu; Stored
Password.
Allah ya tsare mu da shairinsu lawi