22/01/2026
Wani lauya a Jihar Kano, Mubarak Abubakar, ya ce kiran da ake yi kan a gaggauta kashe waɗanda aka k**a bisa zargin kashe wata uwa da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi-Chiranci, ba daidai ba ne kuma ya saɓa wa tsarin shari’ar laifuka na Najeriya.
Yayin da yake bayani daga mahangar shari’a, lauyan ya ce ba za a iya aiwatar da hukuncin kisa ga kowa ba sai kotu mai ikon yanke hukunci ta same shi da laifi.