Yamadawa online TV

Yamadawa online TV Broadcast is our job
just being with yamadawa online TV for getting good news 📰

TIKASHI:🤔Yadda soyayyar Abubakar Lawan Aliyu  ta kusa samun targade kamar yadda ya bayya na a shafin sa gameda wallafa h...
22/07/2025

TIKASHI:🤔

Yadda soyayyar Abubakar Lawan Aliyu ta kusa samun targade kamar yadda ya bayya na a shafin sa

gameda wallafa hotunan shahararriyar yar jaridar nan hauwa Halliru Gwangwazo

ga abunda yace:

Yau saura kadan soyayya ta da somebody's mother ta samu targade 🙆
Daga yau bazan kara magana akan Hauwa Halliru Gwangwazo ba Insha Allah Salisu Eeditor dama kaine ka ruda mu Ina wani kyau anan 🥺?

Bayan nabi trending inata hyping din yarinyar nan yar Gwangwazo ashe beb tana ganin duk motsi na tayi screenshot ta aje.....

To yau dai ta sauke min caji na 🥺
Kunga yadda mukai da ita to nidai daga yau bazan kara magana akan hauwa ba

Wadancan kalaman da nai akanta na janye beb dita tafi hauwa kyau 🤩💔

Da tini yau garina ya bare 🙆🥺
Allah yaceceni

09/07/2025

😥 DUK WANDA YA TAIMAKI WANI... 😥

Jama’a, ina yi maku sallama assalamu alaikum

A yau kuma za mu duba muhimmanci, tasiri da kuma dinbin sinadaran da ke tattare da taimako ga rayuwarmu ta yau da kullum* , *a matsayinmu na mutane. Abu ne da ya kamata kowa ya gane cewa, duk wani dan Adam, komai mukaminsa, komai karfin arzikinsa, komai karfin jikinsa, yana bukatar taimako .

Idan ba ya bukatar tallafin dukiya, to yana bukatar wani, idan bai bukatar wani tallafin, to ala tilas dinsa, yana da wata bukatar daga dan uwansa mutum

Yan uwa na Yan wannan gida munsan Kuna iya kokarin Kuma baza kuso ace Yan uwanku suna wani yanayi ba kun kusa share musu hawaye ba 😥

Akwai wani issue na gaggawa Daya tun Karo mana wannan gida Mai Albarka Wanda wannan gida ya Kafa gidauniyarsa domin Kawar da wannan abu

Muna da Members 500 to Above a wannan gida a Facebook Muna da 57K members

Iya Group Whatsapp idan mukace Zamu Ajje 500 ko 1000 ko 5000 har Mai 100k
Tabbas Zamu samu nasarar abunnan da ya tunkaro mu cikin gaggawa

Domin Rashin lafiyar da Daya daga cikin Member na wannan gida Mai Albarka 😭

Kofa a Bude take daga yanzu zuwa kwana 7 muka shin Zamu Tara kudin da Zamu fitar da wannan gagarumin abunda ya taso 😥

Account

7088816046
Opay
Muhammad Bawa

LAST BORN CHARITY AND EMPOWERMENT ✍️

Faruq Umar Muhammad

Yamadawa online TV

Inason wannan posting ɗin yaje viral saboda ko an samu wani masoyin baba buhari na gaskiya ya bani kyautar 1M naje nayi ...
06/07/2025

Inason wannan posting ɗin yaje viral saboda ko an samu wani masoyin baba buhari na gaskiya ya bani kyautar 1M naje nayi aure da ita.

Dan wlh lokacin danayi wannan compaing ɗin wlh ko Naira 1 ban samu ba 😭

Allah yabawa baba buhari lfy ya yaye masa abinda yake damun sa amen

Muna buƙatar a dagewa da baba buhari addu'a Allah ya bashi lfy amen ✅🤲

09037365454

Ataimaka mun a yaɗa wannan saƙo ko Allah yasa yaje inda ake son yaje 💪

inji abu nageria

Innalillahi Wa Inna ilaihi Raj'un.Allah ya yiwa Abdullahi Shehu Gano (Mai Qasidar Saba'a) rasuwa, bayan ya yi accident a...
06/07/2025

Innalillahi Wa Inna ilaihi Raj'un.

Allah ya yiwa Abdullahi Shehu Gano (Mai Qasidar Saba'a) rasuwa, bayan ya yi accident a satin da ya wuce.

Muna addu'ar Allah ya gafarta masa yasa aljanna makomarsa ya sada shi da Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallama.

~Bashir Dandago

Abu Biyu Da Yakamata Ku Sani Game Da Masu Musu Akan Rarara Da Naziru Sarkin Waƙa.1. Masu Goyon Bayan Naziru Suna Son Shi...
04/07/2025

Abu Biyu Da Yakamata Ku Sani Game Da Masu Musu Akan Rarara Da Naziru Sarkin Waƙa.

1. Masu Goyon Bayan Naziru Suna Son Shi Ne Domin Allah Ya Don Suna Buƙatar Komai Daga Gare Shi Ba.

2. Masu Goyon Bayan Rarara Mafi Yawansu Kaso 70% Ɗinsu Kwaɗayin Abin Hannunsa Da Neman G!ndin Zama Ne Yasa Suke Kare Shi, Bawai Don Yafi Naziru Ba.

Idan Kuka Lura Zaku Ga Yadda Magoya Bayan Rarara Suke Canza Topic Ɗin Asalin Topic Ɗin Akan Mota Akayi Shi Amma Sai S**a Dawo Cewa Ai Naziru Baya Taimako.

Mene Haɗinsu Da Taimakon Shi Wani Baban Su Yana Da Tarin Dukiya Mai Yawa Amma Da Idonsa Bai Taɓa Gani Babansu Ya Taimakawa Mabuƙatan Unguwarsu Ba Kuma Bai Taɓa Yiwa Baban Nasu Ƙorafi Ba Amma Ya Dira Kan Naziru Yana Zaginsa Yana Cewa Baya Taimako.

Taimako Fa Ba Wajibi Bane Idan Ka Taimaka Kanka Idan Ma Baka Taimaka Ba Kanka Domin Kaine Zaka Amfana.🙄

Nura Kasafi ✍️.

Menene abin alfahari don ka tara dukiya? Gidaje, motoci, sutura, da duk wani kayan alatun duniya? Menene abin gorantawa ...
04/07/2025

Menene abin alfahari don ka tara dukiya? Gidaje, motoci, sutura, da duk wani kayan alatun duniya? Menene abin gorantawa wanda basu da su?.

Shin baka lura cewa kowanne Dan Adam, bashi da iko akan arziki ko rashinsa ba? , kuma da akwai mai wannan damar babu wanda zai zabi talauci, shi kansa talakan ba zabinsa bane zama talaka, Allah ne ya zaba masa, kaida kasamu Allah ne yaga damar baka don bakafi kowa ba.

Don haka kuskure ne alfahari da fariya, kuskure ne wulakanta mutane don Allah ya baka wata damar rayuwa, kasani cewa kowanne abu da Allah ya baka jarrabawa ce ka gode maka koka kafirce masa.

Mai cikakken iko kan kudi ko wata alfarma ta duniya shi ne Allah, babu wanda s**ai taraiya da shi a wannan fage, in kana bukatar amsa kalli kanka lokacin da baka samu wani abu ba, da second daya kafin faruwarsa baka San komai ba, haka kiftawar ido bayansa baka sani ba.

Samu da rashi na Allah ne, mafi alkairin dukiya wadda akabi Allah da ita, sannan akayi aikin alkairi don saukakawa al’umma rayuwa…

Abdallah Amdaz

Shafin jarida na Spectatorindex ya ruwaito cewa kasar Isra'ila tana kashe dala miliyan 285 a kowacce rana a wannan yaƙin...
18/06/2025

Shafin jarida na Spectatorindex ya ruwaito cewa kasar Isra'ila tana kashe dala miliyan 285 a kowacce rana a wannan yaƙin da suke da Iran, wannan ya ƙara fito da raunin kasar Isra'ila a fili domin duk da uwar wadannan kuɗi da suke kashewa tare da makaman shingen su na Arrow-2, Arrow-3 da su Iron Dome da sauransu bai hana Iran dagargaza su ba tare da jefa masu manyan bamabamai a wurare masu mahimmanci na ƙasar, cikin harda hedkwatar cibiyar leƙen asiri ta ƙasar (Mossad), da tashar kasuwanci ta Haifa, wannan ya ƙara fito da zahirin tsaron su da suke yaɗa farfagandar cewa shi ne mai girma a duniya.

Daga ranar da aka fara wannan yaƙin Isra'ila ta shirya farfaganda iri-iri da sunan Amurka domin ta shigo da ita cikin yaƙin, wanda abinda yake ɓoye shi ne Isra'ila yakin nan ya fi ƙarfin ta, har ta kai a filin Tsinannen Firaministan su Netanyahu ya fara neman ɗauki kasashen duniya ciki harda Amurka da su shigo su tallafa masa a cikin yaƙi da Iran.

Kashe dala miliyan 285 a kullum, dai dai yake da kashe dala biliyan 104 a shekara idan yaƙin ya cigaba ya zama mai dogon zango. Iya kuɗin yaƙin nan kuwa sun ninka budget din tsaron Isra'ila sau 4 (dala biliyan 24 ~ SIPRI), makamin su na Iron Dome mai amfani da rokar Tamir da s**a fi ji dashi a yana laƙume masu dala 40,000 a kowanne harsashin roka da zai harba, Iran na fatattakar su da daruruwan rokoki a kowace rana, saboda lissafin kuɗin su yana mugun haw-hawa, saboda yawan rokokin Tamir din da suke harbawa. Kuma Isra'ila ba tada karfin tattalin arzikin da zata ɗauki wannan kashe kuɗin yaƙin nan.

Ƙasar Amurka ita ce kasar da tafi turawa Isra'ila kuɗi a duk shekara, a ƙalla dala biliyan 3.3 duk shekara Amurka ke baiwa Isra'ila, dama masana suna cewa Isra'ila sune yan lelen Amurka da abinda Amurka da mallaka.

Tsohon mashawarci a fanni kuɗi ga Hukumar tsaron Isra'ila (IDF Financial adviser) Re’em Aminach ya ce Isra'ila na kashe dala miliyan 725 a kowacce rana a wannan yaƙin da suke da Iran, kimanin kashi 20 na gaba-daya tattalin arzikin ƙasar (GDP). Wanda wannan shi ne kididdiga mafi kusa da hakika musamman duba da wanda ya fadi maganar.

Isra'ila ba zata iya wannan yaƙin ba, makaman da suke karyar suna shi, sun gaza masu, kuɗin da suke kashewa sun yi yawa, basu da abinda zasu cigaba da ɗaukar dawainiyar wannan yaƙin shi yasa Netanyahu ya haukace da hauka iri-iri don yin duk abinda zai sanya Amurka ta kawo masa ɗauki ta shigar masa wannan yaƙi. Idan kuma ba haka ba to dole su rage ƙarfin abinda s**a fito da shi filin daga, wannan kuma Nasara ce ga Iran domin zai bata damar ninka irin dagargazar da suke wa Isra'ila.

Ga rashin kuɗin cigaba da yaƙi, ga kuma rashin Nasara, wannan shi ne halin da Isra'ila take ciki.

Ya Allah ka cigaba da tabbatar da rashin Nasara ga ƙasa yahudawa, Isra'ila tare da ruguza duk mai taimakon Isra'ila. Amin.

Bn Umar Gishiri ✍🏽
Faruq Umar Muhammad
Yamadawa online TV

TALLA:Kuzo ayi muku Kowane kalar aiki da ya shafi graphic design 🤞🤞🥰🥰🥰 Muna haɗa LOGO, INVITATION, ENGAGEMENT STICKER 🤞 ...
13/06/2025

TALLA:

Kuzo ayi muku Kowane kalar aiki da ya shafi graphic design 🤞🤞🥰🥰🥰
Muna haɗa
LOGO, INVITATION, ENGAGEMENT STICKER 🤞 POSTER BANNER BIRTHDAY STICKER 🤞 RAMADAN STICKER, SALLAH STICKER 🤞
MUNA KOWANE IRIN EDITING
ZAKU IYA SAMUN MUTA WHATSAPP
08032440171
KO
07085369493

12/06/2025

Yau ce ranar dimukuradiyya !
Me kuke fata ga kasa Nigeria?

A Matsayinki Na Ƴar Social Media Kiyi Ƙoƙari Bayan Neman Followers K**e Haɗawa Da Neman Mijin Aure Karki Bari Girman Kai...
12/06/2025

A Matsayinki Na Ƴar Social Media Kiyi Ƙoƙari Bayan Neman Followers K**e Haɗawa Da Neman Mijin Aure Karki Bari Girman Kai Ya Hanaki Kula Kowa a DM Domin Wasu Daga Haka Suke Zama Masoya Har Suyi Aure.

Karki Kuskura Ki Yarda Da Abinda Mafi Yawan Mutane Suke Cewa Wai Ƴan Facebook Basa Auren Macen Facebook Wlh Duk Buge Ce Ana Aure Saidai Akwai Waɗanda Ko Kyauta Ba Za'a Auresu Ba.

Saboda Kai Da Ganinsu Kasan Ana Kai Ruwa Rana Dasu Idan Kina So Ki Fice Daga Cikin Irin Waɗannan Dole Ki Zama Mai Kamun Kai Ki Mutunta Kanki Sai Mutane Su Mutunta Ki.

Idan Kuma Kika Bazama Neman Followers Ruwa a Jallo Kuma Kika Ɗorawa Kanki Girman Kai To a Sannu Zaki Bikin Cika Shekara 60 a Gidanku Kina Kwana Cikin Ƙannenki.🤦🏾

Idan Haka Ya Faru Dake Wa Gari Ya Waya.?

Nura Kasafi

11/06/2025

Ina masoya?
Idan budurwar ka ta kiraka a waya kana iya ɗaga kiranta ko kuma
Kana bari seta katse se ka kirata da katinka?

Address

Dambatta Local Government Area
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yamadawa online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share