Sani Alhaji Abba Jakusko

Sani Alhaji Abba Jakusko Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sani Alhaji Abba Jakusko, Digital creator, Kano.

Fulani masu duniya, kunga wadanda s**a kankarowa ABU Cultural Carnivals aji😃😃😃😃
17/08/2025

Fulani masu duniya, kunga wadanda s**a kankarowa ABU Cultural Carnivals aji
😃😃😃😃

ABUBUWA GUDA 10 GAME DA KALLON BATSA WANDA KAFOFIN YANAR GIZO BA ZA SU TAƁA GAYA MUKU BA !1️⃣ Kallon batsa ba ya ƙara ji...
17/08/2025

ABUBUWA GUDA 10 GAME DA KALLON BATSA WANDA KAFOFIN YANAR GIZO BA ZA SU TAƁA GAYA MUKU BA !

1️⃣ Kallon batsa ba ya ƙara jin daɗi a rayuwa – yana cinye kwakwalwarka ne a hankali k**ar yadda ruwan acid yake huda dutse.

2️⃣ Yawancin ’yan wasan batsa ( actors & actress ) ba sa rayuwa cikin farin ciki – suna rayuwa ne cikin ƙunci da kuma zargin kansu,
Da yawa wadanda s**a tuba daga cikin su suna sanar da haka.
Wasu da yawa kuma s**an kashe kansu ne ma sanadiyyar depression.

3️⃣ Babban manufar kamfanonin fina-finan batsa shine su mayar da kowa ya aminta da sha'awar jinsi.
Shi yasa zaku ga sun fi karfafa bidiyoyin sha'awar jinsi kuma sun fi ware budget mai nauyi akansa.
Sannan in dai mutum zai juri kallon batsa a kullum to sai ya dawo yana sha'awar kallon bf na jinsi ɗaya.

4️⃣ Batsa yana koyar da kwakwalwarka kaji mace ta gundureka ko kiji namiji ma kawai wahala ne gaskiya. Shi ya sa ko mutum yayi aure to ba zai iya dainawa ba.

5️⃣ Da yawa daga cikin ’yan wasan batsa sun daina jin daɗin jima’i na gaskiya sai da ƙwayoyi ko idan kyamara na kallonsu,
Haka kai ma idan kaima kace kwaikwayon su zaka dinga yi to nan gaba jima'i ba zai maka daɗi ba kwata-kwata.

6️⃣ Jima’in da kake gani a batsa ba gaskiya ba ne – wasan kwaikwayo ne mai haɗari da ake ɗauka a matsayin al’ada.
Duk wannan ihu da nishi ɗin duk ƙaryan banza ce.

7️⃣ Jarabar kallon batsa gaskiya ce ( addiction )– masana sun tabbatar tana sace kwakwalwa fiye da yadda co***ne ko tabar wiwi take yi.

8️⃣ Wannan masana’antar da ake cewa tana da “tsaro da yarda”? Cike take da cututtuka, cin zarafi, da tilastawa musamman ga yara da mata.

9️⃣ Yawancin abin da ake kira “fantacy” a batsa – hakikanin labarin cinikin mutane ne.
Ko kun san cewan har yanzu ana safaran mutanen mu a ƙasashe irin su Italy, Egypt da sauransu,
Kuma ana tursasa su akan su fito a fina-finan batsa ko da ace basa so ?

🔟 Batsa ba ’yanci ba ne – wata kurkuku ce ta zamani wato ( Digital ) da ke ɗaure zuciyarka, sha’awarka, da ruhinka.

---

⚠️ Idan ka

17/08/2025
17/08/2025

Muje maha

Gizo da Budurwar DanƙoYau dai Iya mai tatsuniya murya ta dashe gaba ɗaya. Ɗazu ta ƙware da goro, amma dai Gizo da kansa ...
16/08/2025

Gizo da Budurwar Danƙo

Yau dai Iya mai tatsuniya murya ta dashe gaba ɗaya. Ɗazu ta ƙware da goro, amma dai Gizo da kansa ya ce zai ba mu labarin yanda su ka ƙarke da budurqar danƙo k**ar haka:

Ga ta nan ga ta nan ku!

Akwai wani Sarki mai suna Jabiru da ke da manyan gonaki a ƙasarsa. Ya na da bayi masu tarin yawa da ke yi masa aiki a waɗannan gonakin. Sai dai kuma akwai wani babban abu da ke damun Sarki. Wannan abu kuwa ba wani abu ba ne illa yawan satar masa amfanin gona da ake yi tun kafin su ƙarasa nuna a girbe.

Da Sarki ya gaji sai ya yi shawara da mashawartansa kan neman mafita. Wazirin Sarki, wanda ya kasance malami mai ɗumbin sani da hikimomi sai ya ce: a haɗa mutummutumi na budurwa amma da danƙo. Idan Allah ya yarda za'a k**a ɓarawon nan cikin sauƙi.

Sarki ya karɓi shawarar Waziri. Aka nema masu hikima su ka ƙera wata zankaɗeɗiya budurwa amma da danƙo mai tsananin danƙo da ƙarfi. Aka ɗauki budurwar nan ta ɗanƙo aka dasa ta a tsakuyar ɗaya daga cikin gonar Sarki da ɓarayi su ka addaba.

Daman ba kowa ne ke yin satar amfani a gonar Sarki ba sai Gizo. Da dai Gizo ya shiga ɗaya ɗaga cikin gonakin Sarki domin yin abinda ya saba. Kwatsam sai idanunsa su ka kai kan wannan zankaɗeɗiyar budurwa.

Nan take Gizo ya fara tunkarar budurawa ya na magana yana ce mata: "Yai budiwa budiwa, in taɓa hannunki? Sai ya taɓa sai hannun Gizo ya maƙale a cikin danƙon hannun budurwa. Ya ƙara cewa: "Au idan kin yiƙe wannan ai ba ga wani hannun ba?" Ya ƙara yunƙurawa yace: "Ƴar budiwa budiwa, in taɓa kumatun ki?" Ai kuwa ya na taɓawa shi ma ɗaya hannun sai ya maƙale a jikin danƙon jikin kumatun ta. A haka dai sai da duk hannaye da kafafuwan Gizo guda shida su ka kame kam a jikn danƙon jikn budurwa. Gizo ya yi, ya yi amma ina? Ya kasa cire kansa daga jikin ɗanko.

Washegari, fadawa da bayin Sarki sun je gewaya, sai ga Gizo a jikin budurwar danƙo duk ya gama galabauta domin tun da tarkon ya k**a shi tun jiya ko ruwa bai samu ya sha ba. Da dai fadawa su ka ga halin da Gizo ya ke ciki

GIZO DA BABBA DOGOAWani lokaci daya gabata Akwai wani wuri a cikin daji inda wani babban mutum mai suna Babba Dogo yake ...
16/08/2025

GIZO DA BABBA DOGO

AWani lokaci daya gabata

Akwai wani wuri a cikin daji inda wani babban mutum mai suna Babba Dogo yake zaune. Wannan mutumin yana da ƙarfi sosai, yana iya ɗaga dutse k**ar ya ɗauki leda, kuma yana iya ɗaukar buhun hatsi goma a kafaɗar sa k**ar bai ɗauki komai ba

Gizo ya gano cewa Babba Dogo kullum yana samun wani babban kifi daga wani kogi mai zurfi da babu wanda zai iya shiga aciki ya kamo kifi, sai dai babba Dogo kaɗai zai iya . Duk lokacin da Babba Dogo ya dawo daga kamun kifi, yanayin suya, sai kamshin ya baza har cikin unguwa.

Gizo ya fara aika matarsa cewa:
— ", ki je wurin Babba Dogo ki ce muna buƙatar ya y'ammuna ɗan garwashin wuta domin muyi dafa abinci."

Duk lokacin da matarsa ta je, ba wai garwashi kaɗai yake bata ba, har da babban kifi mai mai girma. Amma duk lokacin da ta kawo gida,sai Gizo ya fisge shi yacinye shi kaɗai, ya bar matarsa da yunwa.

Da matarsa ta gaji da wannan zaluncin, ta ce:
— "Ni ba zan ƙara zuwa ba, tunda duk nasamo kifi fisgewa kakeyi kacinye kai kaɗai ka barni da yunwa."

Gizo ya ce:
— "To, ni zan je da kaina."

Lokacin da ya je, Babba Dogo ya ba shi kifi kuma yace mishi:
— "Ina kamo wadannan kifayen a wani kogi mai zurfi. Idan kana so, ka zo mu tafi tare gobe."

Gizo ya yi farin ciki har ya kasa barci a daren nan. Da safe s**a tafi zuwa kogin.next episode is coming.

゚viralシviralシfypシ゚viralシalシ








A cikin wani ƙauye, anyi wani manomi wanda yake zaune tare da matarsa da jaririnsa. Suna da wani kare amintacce wanda s*...
16/08/2025

A cikin wani ƙauye, anyi wani manomi wanda yake zaune tare da matarsa da jaririnsa. Suna da wani kare amintacce wanda s**a raine shi tun yana ƙarami.

Wata rana, matar da mijinta s**a fita domin yin wasu muhimman abubuwa, s**a bar jaririn yana barci a gadonsa, sannan kuma s**a bar Karen a cikin gida.

Da mahaifin ya dawo gida, ya buɗe ƙofa, sai ya ga karen yana tsaye a bakin ƙofa… bakinsa cike da jini!

Sai hankalinsa ya ta tashi! Ya yi ihu yana cewa:

“Karen nan ya cinye min ɗana!!”

Ba tare da ya tabbatar ba… sai ya ɗauki gatari, ya hau saran karen har sai da ya kashe shi.

Ya shiga cikin gida da gudu zuwa ɗakin jaririn… sai ya tarar da jaririn yana barci lafiya lau, kuma a gabansa akwai maciji babba matacce!

A nan ne ya fahimci gaskiya:

Karen ne ya kashe macijin da zai kai wa jaririnsu hari… ya cece shi daga mutuwa…
amma a ƙarshe, kare ya biya farashin amincinsa da rayuwarsa!

🧠 Darasi:

Kada kayi saurin yanke hukunci bisa abin da ka gani kawai.

Daukar mataki cikin gaggawa yayin da kake fushi na iya jawo maka babbar asara.

08/01/2024

Address

Kano

Telephone

+2348121901479

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sani Alhaji Abba Jakusko posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sani Alhaji Abba Jakusko:

Share