04/04/2026
Da ɗumi-ɗumi: Matasa sun yi bore kan zargin kuɗaɗen N84.2bn, sun ƙi amincewa da Garo a matsayin Mataimakin Gwamna.
Bayan rahoton da jaridar Mikiya ta wallafa kwanakin baya, inda ta tattara tare da fitar da cikakken lissafin kuɗaɗen da Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke zargin su Hon. Murtala Sule Garo da sacewa—wanda adadinsu ya kai kimanin Naira biliyan 84.2bn lamarin ya fara ɗaukar sabon salo a tsakanin jama’a.
A wani sabon yanayi, wasu matasa dauke da rubuce-rubucen saƙonni a hoton banabana sun tarbi Gwamnan a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, inda s**a fito karara suna nuna adawa da yiwuwar bai wa Murtala Garo mukamin Mataimakin Gwamna.
Matasan sun bayyana cewa ba za su amince da irin wannan mataki ba, musamman duba da cewa gwamnatin jihar ta riga ta shigar da ƙara a kotu kan zarge-zargen da s**a shafi kuɗaɗe masu yawa da s**a haura biliyan 84.2.bn.
Rahoton da Mikiya ta fitar ne ya zama tushen wannan zanga-zanga, inda matasan s**a fara amfani da lissafin da jaridar ta bayyana domin nuna rashin goyon bayansu ga Hon. Murtala Sule Garo.
Lamarin na ƙara ɗaukar zafi yayin da jama’a ke jiran yadda gwamnati da masu ruwa da tsaki za su mayar da martani kan wannan matsin lamba daga matasa…