04/04/2026
Kukan zuci…
Shafuka a kafafan sada zumunta na ta ƙara yawa ma su kira izuwa ‘Hausa zalla’ da wai ‘Bahaushe ya mulki kansa’. Ba hakan ba ne matsala. Da man kowacce ƙabila a Najeriya ta na da na ta ƙungiyoyin irin haka. Matsalar ita ce wasunsu na ta yaɗa gaba da tunzuri tsakanin Hausawa da Fulani. Ko jiya sai da lamarin nan ya hana ni bacci. Amman fa duk lokacin da lamarin ya dame ni, sai kuma na tuna cewa duk waɗannan matsalolin rashin tsaro ya haifar da su. Kuma da man ai a kan tafe kan taras…
Tabbas ba ƙaramar illa a ka yi ma na ba da a ka kasa shawo kan banditry. Waɗanda ya dace su yi abin da ya dace a lokacin da ya dace ba su yi ba. Matsalar babba ce, amman ba ta fi ƙarfin hukomomin tsaron Najeriya musamman idan su ka haɗa kai da jihohi cikin ikhlasi. Sai dai kash…
Bandits har TikTok live su ke yi, kuma da yawan su za su faɗa ma ka cewa su Bahaushe maƙiyinsu ne, ga kuma Hausa villages da su ke raiding. Sun sha su yi video su na lalatawa Hausawa amfanin gona su na dariya. Unfortunately matsala ta ƙi tafiya, har kuma wasu Hausawa su ka fara tunanin matsalar ƙabilanci ce. Yo ko akwai wanda ya taɓa ganin bandits sun yi raiding ruga? Abun babu daɗi. Da gwamnati ta yi abun da ya dace a kan lokaci da ba mu kai ga haka ba. Yanzu ga shi mun zo lokacin da matsalar tsaro da wawayen cikinmu su ka haddasa na neman assasa gaba tsakanin ma su hankalinmu daga Hausawa da Fulani.
Abubuwa ne fa su kai ta faruwa na dabbanci tsawon shekaru kusan goma. Bandits ɗin nan dai ‘yan ƙabilar Fulani ne yawancinsu, su kuma victims yawanci Hausawa. Ƙiri-ƙiri a ka ciwa Sarkin Gobir mutunci kuma a ka kashe shi. Sarki guda fa. Har kuma wai sulhu a ke da bandits a basu kuɗi, su kuma victims ɗin an ƙyale su. Da yawa victims na ganin ƙabilanci ne kawai. Akwai Lokacin da a ka fara maganar yaƙar bandits, har former ES na NHIS ya fito ya yi magana a matsayinsa na Fulani wai ba sa goyon bayan hakan. Hakan ya ƙara ingiza ma su rajin Hausa zalla. Maimakon a samu daidaito da maslaha, sai kuma a ke neman nuna cewa su reactionists ɗin Hausawa su ne wai za su tada fitina. Ga kuma ci mu su mutunci da a ke a na kiransu da maguzawa. Wai har wani na cewa “Mu na zaman lafiyarmu za’a tada ma na rikici”…
To ai shi ya sa victims ɗin ke ganin saboda mu na cikin gata shi ya sa mu ke ganin matsalarsu ba wata matsala ba ce. Da yawanmu za ka ji mun ce mu na tsoron ka da abunda ya afku a Rwanda ya afku, amman fa da yawan ƙauyukan Hausawa a SOKEZA, su sun ga Rwanda tun tuni - an yiwa ‘ya’yansu fya*ɗe a gabansu, an kashe mu su iyaye a gabansu, an kore su daga ƙauye an banka ma sa wuta, an same su a masallaci su na sallah duk an yayyankasu, duk sati ko wata wasunsu sai sun baiwa ‘yan ta’adda haraji. To kuma me ya rage?
Ma su hankali dai sun san cewa abinda ke faruwa da man zai faru. A duk lokacin da wasu mutane daga wata ƙabila su ka fitini wasu mutane daga ƙabila mabambanciya, to fitinar ta kan zama biyu - ga rashin aminci ga kuma hassada gaba tsakanin ƙabilun. Mafitar a ko yaushe ɗaya ce - a tabbatar da tsaro ga kowa da kowa.
Marzuq Ungogo