17/09/2021
Jama'ar jihar Kano kuzo kuyi alkalanci akan masu wakiltarku a majalisun tarayya, akan kudurin da s**a gabatar daga 2019 zuwa yanzu.
- MAJALISAR DATTIJAI
1. Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibril Maliya, ya gabatar da kuduri guda 13
2. Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, bai samu gabatar da kuduri ko daya ba
3. Sanatan Kano ta kudu, Kabiru Ibrahim Gaya, ya gabatar da kuduri guda 3
- YAN MAJALISAR WAKILAI NA KASA
1. Dan majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar karamar hukumar Kumbotso, Manniru Babba Dan Agundi, ya gabatar da kuduri guda 7
2. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Wudil da Garko, Ali Muhammad Wudil, ya gabatar da kuduri guda 6
3. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomi Doguwa da Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya gabatar da kuduri guda 3
4. Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tarauni, Hafizu Muhammad Kawu, ya gabatar da kuduri guda 3
5. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Karaye da Rogo, Haruna Isa Dederi, ya gabatar da kuduri guda 3
6. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alasan Rurum, ya gabatar da kuduri guda 2
7. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa, Sani Bala, ya gabatar da kuduri guda 2
8. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Takai da Sumaila, Shamsuddeen Bello Dambazau, ya gabatar da kuduri guda 2
9. Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Fagge, Aminu Sulaiman Goro, ya gabatar da kuduri guda 2
10. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gezawa da Gabasawa, Nasiru Abduwa, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
11. Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwale, Abdullahi Lawan Ken-Ken, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
12. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwarzo da Kabo, Musa Umar Garo, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
13. Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Birni, Sha'aban Ibrahim Sharada, bai samu damar gabatar da kuduri ko guda daya ba
14. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu, Abdullahi Mahmud Gaya, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
15. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Ali Datti Yako, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
16. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam, Kabiru Idris, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
17. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Ungoggo da Minjibir, Sani Ma'aruf, bai samu damar gabatar da kuduri ko guda daya ba
18. Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, Babangida Alhassan Yakudima, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
19. Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Bichi, Abubakar Kabir Bichi, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
20. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Bagwai da Shanono, Ahmad Yusuf Badau, bai samu damar gabatar da kuduri ko guda daya ba
21. Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa, Nasiru Ali Ahmad, bai samu damar gabatar da kuduri ko guda daya ba
22. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Dambatta da Makoda, Badamasi Ayuba, bai samu damar gabatar da kuduri ko guda daya ba
23. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Tofa, Rimin Gado da Dawakin Tofa, Tijjani Abdulkadir Jobe, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
24. Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa, Mustapha Bala, bai samu gabatar da kuduri ko guda daya ba
Wannan rahoton Order Paper ne da ta fitar, daga watan June na shekarar 2019 zuwa watan May na shekarar 2021, a saboda haka jaridar Kano Online News ke bukatar ku bayyana ra'ayoyinku.
Kowa ya fadi sunansa, karamar hukumarsa, da sunan wakilinsa, da kuma makin dazai iya bashi, banza zagi don Allah.
Daga: Kano Online News
17/9/2021