
30/05/2025
SALBAS OIL AND GAS SHINE YA ZARE TAKOBI DOMIN KAKKABE AIYUKAN TAADDANCI DA SHAYE SHAYE A YANKIN RANO
A Bisa hasashe nan da shekaru goma masu zuwa matasan Rano zasu daga tutar ilimi a jihar Kano tare da karamar Hukumar bichi
Hakan zai faru sakamakon kidiiddiga na yawan masu samun admission a Jamia a gida da wajen kasar Nan
A yankin Rano an samu yawan matasa masu shiga Jamia a dalilin tallafin karatu ko nace daukar nauyin karatu Wadda attajirin matashin
Dan kasuwa CHAIRMAN SALBAS OIL AND GAS
Wanda ya kudiri niyyar duk wani matashi mai muradin neman ilimi Kuma Babu sukuni tare da marayu da Yara masu kwazo wadanda iyayensu basuda karfi , chairman ya dauki nauyin Sai ya ilimintar da matasan wannan yaki na Rano , a duk shekara mutanen da yake daukar nauyi bazasu lissafu ba, Allah ya saka Masa da alkhairi domin idan matasa s**a samu ilimi bazasu aikata taaddanci ba wannan shine matakin farko na yakar shaye shaye da aiyukan taaddanci, muna Kira da matsakaitan masu arzikinmu dasu yi koyi da shi
Wannan itace hanya Daya tilo dazaa dakile aiyukan taaddanci a RANO Kuma Dama Rano batayi suna wajen Shaye shaye da mugayen laifuka ba , muna addua Allah ya tsare mana gsrinmu da Kano da kasa baki daya
NAGODE
NASIRU IBRAHIM
(MASO RANO)