24/09/2025
Majalisar Dokoki ta nemi Gwamnatin Kano ta gyara babban masallacin jihar
Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi Gwamnatin jihar ta gyara Babban Masallacin cikin Gari mai cike da tarihi.
Freedom Radio ta rawaito cewa a zaman majalisar jihar da aka gudanar yau, ɗan majalisar Birni, Aliyu Yusuf Daneji, ya sake kira ga gwamnati da ta gaggauta fara aikin gyaran masallaci da aka riga aka gabatar mata a baya, amma har yanzu ba a aiwatar ba.
Haka kuma, ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Rano, Ibrahim Muhammad Malami Rano, ya bukaci gwamnati ta gyara muhimman hanyoyin cikin garin Rano.
Yan majalisun biyu sun bayyana cewa gyaran masallacin da kuma hanyoyin na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma, tare da roƙon gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.