Falcon Times Hausa

Falcon Times Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Falcon Times Hausa, Media/News Company, Kano.

Falcon Times Hausa, Jaridar Intanet ce dake kawo muku sahihan labarai na Najeriya, Duniya da suka shafi tattalin arziki, siyasa, wasanni da alamurran yau da kullum.

YANZU-YANZU: Kwankwaso da Peter Obi sun isa sakatariyar jam’iyyar NDC na kasa.
03/05/2026

YANZU-YANZU: Kwankwaso da Peter Obi sun isa sakatariyar jam’iyyar NDC na kasa.

APC a Gombe ta zaɓi Jamilu Gwamna a matsayin dan takarar Gwamna na masalaha inda ta yi watsi da PantamiJam’iyyar APC a J...
03/05/2026

APC a Gombe ta zaɓi Jamilu Gwamna a matsayin dan takarar Gwamna na masalaha inda ta yi watsi da Pantami

Jam’iyyar APC a Jihar Gombe a yau Lahadi ta sanar da cewa ta amince da Jamilu Ishiyaku Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamna na masalaha domin zaɓen shekarar 2027.

Tsohon ministan sadarwa da tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami, ya rasa damar tsayawa takara bayan da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar s**a zaɓi Jamilu Gwamna.

An cimma wannan matsaya ne a wani taron manyan jiga-jigan jam’iyyar, wanda jagoran jam’iyyar a jihar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jagoranta.

Haka kuma, taron ya amince da ‘yan takarar masalaha na jam’iyyar a kujerun sanatoci uku na jihar, da kujerun Majalisar Wakilai guda shida, da kuma kujeru 24 na Majalisar Dokokin Jihar.

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci magoya bayansa su fice daga jam’iyyar African Democratic Cong...
03/05/2026

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci magoya bayansa su fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yayin da ake zargin yana shirin komawa wata sabuwar jam’iyya mai suna National Democratic Coalition (NDC) tare da Peter Obi.

Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran Kwankwaso zai haɗu da Peter Obi a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, inda ake hasashen za su yi takarar shugaban ƙasa tare, a tsarin tikitin haɗin gwiwa na Obi–Kwankwaso.

Haka kuma, ana sa ran wasu ‘yan majalisar da s**a bar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa ADC za su sanar da ficewarsu nan ba da jimawa ba, domin komawa NDC a cikin sabon tsarin siyasar da ake ƙulla.

Mahaifin A.A. Zaura ya rasu a KanoMahaifin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Abdussalam Abdulkarim Zaura (A.A. Zaura)...
03/05/2026

Mahaifin A.A. Zaura ya rasu a Kano

Mahaifin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Abdussalam Abdulkarim Zaura (A.A. Zaura), Alhaji Abdulkarim Saleh Zaura, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne da safiyar Lahadi bayan fama da jinya mai tsawo a garin Zaura da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano.

Ya rasu yana da shekaru 108, kuma ya bar ‘ya’ya shida, maza uku da mata uku.

An tsara gudanar da sallar jana’izarsa da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Lahadi a garin Zaura, ƙaramar hukumar Ungogo.

🚨Ina ƴan Kwankwasiyya; Kun shirya komawa NDC?
01/05/2026

🚨Ina ƴan Kwankwasiyya; Kun shirya komawa NDC?

Ɗan majalisar ADC mai goyon bayan Nafi'u Bala ya fice daga jam'iyyarDan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yagba a J...
01/05/2026

Ɗan majalisar ADC mai goyon bayan Nafi'u Bala ya fice daga jam'iyyar

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yagba a Jihar Kogi, Leke Abejide, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC.

Kamar yadda rahotanni s**a nuna, Abejide — wanda aka zaɓe shi sau biyu a majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar ADC — ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Juma’a.

🚨"Babban kuskuren siyasa da Obi da Kwankwaso za su yi shi ne raba hanya da kawancen ADC. Komai kyawun shugaba, mutane ba...
01/05/2026

🚨"Babban kuskuren siyasa da Obi da Kwankwaso za su yi shi ne raba hanya da kawancen ADC. Komai kyawun shugaba, mutane ba sa bin sa zuwa ƙabari. Muddin ADC tana nan, NDC ba za ta yi tasiri ba."

"Idan APC za ta iya dasa Nafiu a cikin babban kawancen adawa na ADC, me yasa kuke tunanin ba za su iya ƙirƙirar wani Nafiu a NDC ko PRP don wargaza su ba. Matsalar da ke damun ADC ba Nafiu ba ce, fannin shari'a mai cike da cin hanci da rashawa da hukumar zaɓe mai son zuciya. Muddin babu wata jam'iyyar adawa da ke da iko a kan shari'a da INEC, waɗannan ƙalubalen za su ci gaba.

"Shawarata ita ce: su zauna a ADC don yaƙi tare."

"Kayar da jam'iyya mai mulki kamar APC da ɗan siyasa kamar Tinubu ba aiki ne mai sauƙi ba, koda kuwa dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya za su haɗa kai don yaƙar sa."

- Jaafar Jaafar

DA ƊUMI-ƊUMI: Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi su na shirin ficewa daga jam’iyyar ADC zuwa wata jam'iyyar Tsohon gwamna...
01/05/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi su na shirin ficewa daga jam’iyyar ADC zuwa wata jam'iyyar

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, tare da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, su na shirin ficewa daga jam’iyyar ADC, kamar yadda rahotanni s**a bayyana.

Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ne yake kokarin hada kawance a tsakaninsu domin samar da sabuwar hadakar siyasa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Yayin da aka hangi wasu makusantan siyasar Kwankwasiyya sun fara ficewa daga jam'iyyar ADC a safiyar yau.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin tunkarar zaben 2027, inda manyan ‘yan siyasa ke sake tsara matsayinsu domin samun karfi a fagen siyasa.

Shin kuna gani wannan hadaka za ta iya tasiri a zaben 2027?

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Falcon Times Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share