Atlas News Hausa

Atlas News Hausa I M Film Producer/Editor/actor In Kannywood
(4)

Ribadu Na Nan Daram A Matsayin NSA, Sabon Ofishin Tsaro Na Karfafa Gwiwa Ne – Fadar Shugaban Kasa​​Wata majiya mai tushe...
11/05/2026

Ribadu Na Nan Daram A Matsayin NSA, Sabon Ofishin Tsaro Na Karfafa Gwiwa Ne – Fadar Shugaban Kasa

​Wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, bai yi murabus daga mukaminsa ba k**ar yadda wasu jita-jita ke yaduwa.

​Wannan karin haske ya biyo bayan nada Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa (mai ritaya) a matsayin Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa kan Tsaron Cikin Gida (Homeland Security).

​Majiyar ta bayyana cewa, nadin Janar Famadewa wani bangare ne na yunkurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake garambawul ga tsarin tsaron kasar nan domin fuskantar kalubalen tsaro.

​Ga wasu muhimman hujjoji da majiyar ta bayar:

​Hadin Gwiwa: Sabon ofishin zai taya ofishin NSA aiki ne, ba wai zai maye gurbinsa ba.

​Kwarewa: Janar Famadewa tsohon jami’i ne a ofishin NSA tsakanin 2015 zuwa 2021, don haka ya san dabarun aikin.

​Ayyukan Ofishin: Sabon ofishin zai fi mayar da hankali ne kan shige da fice (Immigration), jami’an tsaro na farar hula (Civil Defence), tsaron sufuri da kuma tattara bayanan sirri na cikin gida.

​Majiyar ta tabbatar da cewa Mallam Nuhu Ribadu na ci gaba da jin dadin amincewar Shugaba Tinubu, kuma yana nan yana gudanar da ayyukansa na hada kan hukumomin tsaro da sarrafa bayanan sirri na kasa baki daya.

​"Jita-jitar cewa Mallam Nuhu Ribadu ya yi murabus karya ce tsagwaronta, kuma k**ata ya yi jama'a su yi watsi da ita domin ba ta da tushe b***e mak**a." — Majiyar Fadar Shugaban Kasa

​A karshe, fadar shugaban kasar ta yi kira ga ’yan Najeriya da su guji bin labaran bogi wadanda ka iya haddasa rudani a cikin tsarin tsaron kasar nan, musamman a wannan lokaci da ake kokarin kawo karshen ayyukan ta’addanci da bindiga.

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’unAllah ya yi wa tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Birniwa/Guri/Kirikas...
11/05/2026

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un

Allah ya yi wa tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Birniwa/Guri/Kirikasamma, Hon. Abba Anas (Laushi) rasuwa, sak**akon garkuwa da aka yi da shi a hanyar Abuja.

Za a sanar da lokacin gudanar da jana’izarsa da zarar an kawo gawarsa gida.

Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa kura-kuransa, Amin.

Kotun majistiri mai lamba 9 da ke Nomansland a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Halima Wali, ta hana jarumar Kanny...
11/05/2026

Kotun majistiri mai lamba 9 da ke Nomansland a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Halima Wali, ta hana jarumar Kannywood Rashida Adamu Mai Sa’a yin posting a kafafen sada zumunta har sai an kammala shari’ar da jaruma Ruƙayya Dawayya ta shigar a kanta kan zargin ɓata suna.

Rahotanni sun bayyana cewa Dawayya ta kai ƙarar Mai Sa’a ne bisa zargin cin mutunci, ɓata suna da kuma hana zaman lafiya.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Wajen Gina Dakunan Kwanan Dalibai ​Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin ...
11/05/2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Wajen Gina Dakunan Kwanan Dalibai

​Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kashe kudi kusan naira biliyan 250 a cikin shekarar 2026 domin gina sabbin dakunan kwanan dalibai a manyan makarantun gaba da sakandare na kasar nan.

​Wannan mataki na kunshe ne a cikin wani babban shiri na kyautata jin dadin dalibai da kuma fadada damar samun ilimi mai inganci, wanda ake ganin shi ne jari mafi tsoka da aka taba zubawa a fannin gidajen dalibai a tarihin Najeriya.

​Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa wannan shiri zai magance matsalolin karancin masauki da dalibai ke fuskanta.

Za a kashe naira biliyan 100 wajen gina dakunan kwanan dalibai masu dauke da gado 500 a kowace jami'a daga jami'o'i guda 50 a fadin kasar nan. Kowanne aiki daya an kiyasta shi a kan naira biliyan 2.

​Za a gudanar da wasu ayyukan guda 24 na hadin gwiwa da masu zuba jari masu zaman kansu, inda gwamnati za ta bayar da biliyan daya, su kuma masu zuba jari su bayar da biliyan 3 a kowanne aiki. Wannan zai samar da masauki ga dalibai tsakanin 1,200 zuwa 1,500 a kowace makaranta.

​Hukumar tallafawa manyan makarantu ta TETFund ce za ta dauki nauyin samar da wadannan kudade, inda za a yi amfani da su wajen gina sabbi da kuma gyara tsofaffin dakunan kwanan dalibai da s**a lalace.

​Babban burin wannan shiri shi ne samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa, tare da rage cinkoson dalibai a daki daya da ake samu a manyan makarantun kasar nan a halin yanzu.

​"Wannan shiri ne da zai tabbatar da cewa dalibanmu sun samu wurin kwana mai tsafta da walwala, wanda hakan zai taimaka musu wajen mayar da hankali kan karatunsu." — Maruf Olatunji Alausa

​Masana ilimi sun yi amanna cewa idan har aka kammala wadannan ayyuka, za a samu sauki kwarai wajen rage kuncin da daliban jami'o'i da kwalejoji ke fuskanta, musamman 'ya'yan talakawa da ke dogara da masaukin makaranta.

WATA SABUWA:~ Mawaƙi Tijjani Hussaini Gandu yace kuzo da hujja a addinance ba a jahilce ba ina akace kar a zaɓiOBI/ KWAN...
11/05/2026

WATA SABUWA:~ Mawaƙi Tijjani Hussaini Gandu yace kuzo da hujja a addinance ba a jahilce ba ina akace kar a zaɓi
OBI/ KWANKWASO a mulkin dimokuraɗiyyar?

Nijeriya ta wajabta yin gwajin ƙwaya ga ɗaliban sakandareGwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da sabbin tsauraran matakai domi...
11/05/2026

Nijeriya ta wajabta yin gwajin ƙwaya ga ɗaliban sakandare

Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da sabbin tsauraran matakai domin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a makarantun sakandare, ciki har da wajabta gwajin ƙwaya ga ɗalibai.

A cewar jaridar Punch, sabuwar dokar ta tanadi cewa duk sabbin ɗaliban da za su shiga makarantar sakandare za a yi musu gwajin ƙwaya kafin karɓarsu.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaliban da aka samu suna amfani da miyagun ƙwayoyi fiye da sau ɗaya bayan an yi musu jinya da gyaran hali na iya fuskantar dakatarwa daga makaranta na ɗan lokaci.

Musa Maisana'a Da Maigidansa, Malam Nuhu Ribaɗu
11/05/2026

Musa Maisana'a Da Maigidansa, Malam Nuhu Ribaɗu

2027: Tinubu ne ya kafa jam'iyyar NDC don ya yi wa ƴan adawa illa - ADCJam’iyyar adawa ta ADC ta zargi Shugaban Ƙasa Bol...
11/05/2026

2027: Tinubu ne ya kafa jam'iyyar NDC don ya yi wa ƴan adawa illa - ADC

Jam’iyyar adawa ta ADC ta zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma jam’iyyarsa ta APC da hannu wajen kafa sabuwar jam’iyyar NDC domin raunata haɗin kan ƴan adawa a Najeriya.

BBC ta rawaito cewa, zargin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tafka muhawara tsakanin jam’iyyun siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

A cewar ADC, kafa jam’iyyar NDC wata dabara ce da aka ƙirƙira domin raba kan masu jefa ƙuri’a ga jam’iyyun hamayya, tare da rage ƙarfin manyan jam’iyyun adawa da ke shirin ƙalubalantar gwamnati mai mulki.

Jam’iyyar ta ce maimakon bunƙasa dimokaraɗiyya ta gaskiya, an kafa sabuwar jam’iyyar ne domin kawo cikas ga haɗin kai tsakanin ƴan adawa.

Sai dai jam’iyyar APC ta musanta zargin, inda ta ce ba ta da hannu wajen kafa jam’iyyar NDC, tare da ƙoƙarin wanke kanta daga zarge-zargen da ADC ke yi.

Ya k**ata Gwamna Abba ya fahimci manufar Shugaba Tinubu akan Farouk LawanDaga NASIR S. GWANGWAZODaga dukkan alamu Gwamna...
11/05/2026

Ya k**ata Gwamna Abba ya fahimci manufar Shugaba Tinubu akan Farouk Lawan
Daga NASIR S. GWANGWAZO

Daga dukkan alamu Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki matsaya kan wanda zai tsaya wa Jam’iyyar APC takarar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Bagwai da Shanono a babban zaben 2026, inda yake kokarin mika takarar ga wanda ba shine akasarin al’iummar yankin suke so ba, duk da cewa, mazabar tana da mai neman takarar wanda duk Nijeriya an yarda da tasirinsa a Majlisar Dokoki ta Kasa, wato tsohon dan majalisa, Hon. Farouk Lawan.
Sunan Hon. Farouk Lawan ba bakon abu ba ne a siyasar Nijeriya, ballantana ta Jihar Kano, mahaifarsa, saboda tasirin da ya yi a Majlisar Wakilai lokutan gwamnatoci daban-daban da s**a shude k**a daga ta Obasanjo, Yar’Adua zuwa ta Jonathan, inda har aka rika yi masa lakabi da ‘Mr. Integrity’ ko ‘Ka Fi Speaker’.
A lokacin da Farouk Lawan ke sharafinsa a Majalisar Dokoki ta Tarayyar Nijeriya, kowa ya yarda cewa, majalisar tana da nagarta fiye da yadda ake gani bayan da ba ya nan daga zamanin gwamnatin Buhari zuwa yanzu, saboda yadda a lokutansa Majalisar Wakilai ke iya taka wa bangaren zartarwa birki a duk lokacin da aka nemi kauce hanya.
Amma sai dai hakan ba ya nufin a lokacin da Faruku ke majalisa, ita majalisar ba ta mara wa bangaren zartarwa baya kan kyawawan manufofin da s**a zo da su a koyaushe, illa dai kawai ana yin abun ne cikin mutuntaka da bin doka da ka’idojin aiki. Babban misali shine, yadda aka zauna lafiya tsakanin Majalisar Dokoki da bangaren zartarwa a zamanin Marigayi Yar’Adua, gwamnatin da ake kallo a matsayin mafi nagarta da aka taba yi tun bayan kafa wannan Jamhuriya ta Hudu.
Wannan tsari na daga cikin dalilan da s**a sanya Shugaba Tinubu ya yi yafiya ga Hon. Farouk Lawan bayan da ake ganin gwamnatin Jonathan ta shafa masa kashin kaji, sannan gwamnatin Buhari ta kasa yi masa abin da gwamnatin Tinubu ta yi na yafiya. Yafe wa Hon. Farouk Lawan na daya daga cikin abubuwan da Tinubu ya yi wa ’yan Arewa, wadanda ba za a taba manatawa da su ba, saboda Shugaba Tinubu yana da basirar gane cewa, samun irin su Faruku a Majalisar Dokoki zai taimaka matuka gaya wajen dawo da martabar Nijeriya a idanun duniya ba tare da kace-nace tsakanin bangaren zartarwa da majalisa ba. Bai dace Gwamnan Kano ya hana wa Nijeriya samuwar hakan ba.
A yanzu da ake ganin al’amura sun cakude kan yadda ake tafiyar da Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu, manazarta da dama suna kallon hakan yana da nasaba da yadda Majalisar Dokoki ke tafiyar da dangantakarta da bangaren zartarwa, inda wasu ke ganin cewa, majalisar ta kasa ba ta taimaka wa bangaren zartarwa wajen aiwatar da kyawawan manufofin da Gwamnatin Tinubu ta tsara har ma ake kallon ta a matsayin gwamnatin da ta yi bakin jini a idanun ’yan kasa, alhali wasu manufofin da ta ke gabatarawa za a ga amfaninsu a nan gaba, amma yadda ake gabatar da su a majalisa kuma ake amincewa da su kai tsaye ne yake janyo surutai a tsakanin ’yan Nijeriya, musamman ’yan Arewa. Wannan ya sanya ake kallon majalisa a matsayin ’yar amshin Shata.
Don haka lallai ya dace a samu kwararru a Majlisar Dokoki ta Kasa, wadanda za su iya amfani gogewarsu wajen ganin an saisaita al’amura, k**ar yadda ya faru a lokacin Yar’Adua, domin ba koyaushe ba ne fada da bangaren zartarwa ke amfanar ’yan kasa.
Dakile dawowar Farouk Lawan zuwa majalisa a wannan lokaci zai kawo cikas ga manufofin Tinubu na ganin an dawo da martabar Gwamnatin Tarayya da ita kanta majalisar, kuma koma-baya ne ga jihar Kano da Arewa, domin akwai bukatar samun gogaggu, wadanda va dolaye ba ne, a Majalisar Dokoi kuma dan majalisa daya tamkar da goma irin Faruku, don saita al’amura.
Hakika lallai ya wajaba ga Gwamna Abba Yusuf ya fahimci Shugaba Tinubu akan batun nan na tsayar da dan takara kuma ya gane alkiblar al’ummar mazabar Bagwai da Shanono da Jihar Kano da Arewa da ma Nijeriya bakidaya!
Rigingimun da ake haifarwa da sunan masalaha a wajen tsayar da ’yan takarar APC, tabbas wagegiyar kofa yake budewa ga ’yan adawa, wadanda a shirye suke su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatin jihar!

Nasir Gwangwazo ɗan jarida ne mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya

2027: Hon. Muslihu Yusuf Ali Ya Bayyana Gaban APC Domin TantancewaHon. Muslihu Yusuf Ali, mai neman takarar kujerar Maja...
10/05/2026

2027: Hon. Muslihu Yusuf Ali Ya Bayyana Gaban APC Domin Tantancewa

Hon. Muslihu Yusuf Ali, mai neman takarar kujerar Majalisar Tarayya a ƙaramar hukumar Kumbotso, ya bayyana a gaban uwar jam’iyyar APC domin tantance shi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Hon. Muslihu Yusuf Ali ya sake jaddada aniyarsa ta kawo ingantaccen wakilci, cigaba mai ɗorewa da kuma kare muradun al’ummar Kumbotso idan aka ba shi damar tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Dubban magoya baya da masu ruwa da tsaki na ci gaba da bayyana goyon bayansu gare shi, tare da bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan siyasar da ake ganin za su kawo sauyi mai anfani ga al’ummar Kumbotso.

PRESS STATEMENTGovernor Yusuf Approves 200 Riyals Support, Ihram for Each Kano PilgrimHis Excellency, Kano State Governo...
10/05/2026

PRESS STATEMENT

Governor Yusuf Approves 200 Riyals Support, Ihram for Each Kano Pilgrim

His Excellency, Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has approved a cash support of 200 Saudi Riyals and Ihram to each intending pilgrim from the state for the 2026 hajj exercise.

Governor Abba Kabir Yusuf, represented by his Deputy, Murtala Sule Garo, disclosed this on Sunday during the launch of the practical demonstration session organised by the Kano State pilgrims Welfare Board for prospective pilgrims in Kano.

Speaking at the event, Alhaji Murtala Sule Garo explained that the exercise was organized to educate, inform, spiritually prepare the intending pilgrims for the Hajj rites from Ihram to Tawaf, from Sa’i to Arafat, from Muzdalifah to Mina and the symbolic stoning of the Jamarat.

He stated that the administration of Abba Kabir Yusuf remains committed to the welfare and well-being of all the pilgrims from the state.

Garo said, “This demonstration is a vital aspect of Hajj preparation. Hajj is not merely a journey of travel; it is a sacred act of worship that requires adequate knowledge, discipline, patience and sincere devotion to Allah."

Garo further conveyed the Governor's goodwill gesture to the pilgrims.

He added, “I also wish to give the good tidings to our pilgrims that the Kano State Government has approved the sum of 200 Saudi Riyals and Ihram to each and every intending pilgrim as a compliment from His Excellency, Governor Abba Kabir Yusuf."

The Deputy Governor also revealed that the administration has secured conducive accommodation arrangements to ensure the comfort and convenience of the pilgrims throughout their stay in Saudi Arabia.

According to him, the state government has equally deployed well-trained medical personnel to complement healthcare services provided by the National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON), saying qualified Islamic scholars have also been selected to provide spiritual guidance during the exercise.

He urged the intending pilgrims to be worthy ambassadors of Kano State and Nigeria by obeying the laws of Saudi Arabia and conducting themselves with discipline, humility, and responsibility throughout the pilgrimage.

Aminu Dahiru
10th May, 2026

Address

No 11 Kb Ibrahim Umar Street Behind Sahad Store Zoo Road
Kano
700001

Telephone

+2348036970125

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Atlas News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Atlas News Hausa:

Share