19/07/2025
Wani ɗan gajeren hutu da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya je Birtaniya domin duba lafiyarsa, ya ƙare da alhini bayan rasuwarsa a asibitin London Clinic da ke birnin Landan a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa kafin mutuwarsa, Buhari yana cikin yanayi na murmurewa har ma da annashuwa a ranar Asabar, 12 ga Yuli — inda ake sa ran zai samu sallama cikin kwanaki masu zuwa. Sai dai daga bisani, lafiyarsa ta ɗauki wani sabon salo a tsakiyar Lahadi, wanda hakan ya kai ga rasuwarsa.
Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda shi ma yana kwance a wannan asibiti a lokacin, ya samu sauƙi kuma aka sallame shi kafin wannan ibtila’i ya afku ga abokinsa.
Dan uwan marigayin, Mamman Daura, ya tabbatar da cewa Buhari yana cikin koshin lafiya da annashuwa kafin al’amura su canza. A cewarsa, “Yana cikin nishadi a ranar Asabar. Mun yi fatan zai fito nan da kwanaki kaɗan. Amma ranar Lahadi lafiya ta sake tabarbarewa.”
Buhari ya bar gida Najeriya tun watan Afrilu don ci gaba da jinya, wacce ya jima yana karɓa a ƙasashen waje, musamman Birtaniya.
Ina Ne London Clinic?
London Clinic wani katafaren asibiti ne mai zaman kansa da ke tsakiyar birnin Landan, wanda aka kafa tun 1932. Asibitin ya shahara wajen kula da cututtuka masu tsanani k**ar ciwon daji (cancer), cututtukan ciki, tiyata da kuma sashin kulawa na musamman (ICU).
An fi ganinsa a matsayin wurin da manyan ’yan siyasa da mashahurai ke zuwa domin samun ingantacciyar lafiya. Har ila yau, wasu daga cikin dangin gidan sarautar Ingila sun taba karɓar jinya a nan.
Wani likitan Najeriya da ke aiki a Landan ya bayyana cewa asibitin na da kayan aiki na zamani da ƙwararrun likitoci daga sassa daban-daban na duniya. Ya ce farashin jinya a nan ba ƙarami ba ne – ganin likita na iya kaiwa daga £100 zuwa £750, yayin da tiyatar manyan cututtuka ke kaiwa daga £10,000 zuwa £13,000. Haka kuma kwana guda a sashen ICU yana kaiwa £3,500!
Yaushe Asibitocin Najeriya Za Su Habaka?
Rasuwar Buhari a irin wannan asibiti na ƙasashen waje ya sake tada muhawarar da ake ta yi tsawon shekaru a Najeriya — shin me ya sa shugabanninmu ke yawan barin ƙasar domin neman lafiya? Menene makomar cibiyoyin lafiyar cikin gida?
Wannan mutuwa ta bar darussa masu yawa ga ƙasa da kuma masu riƙe da madafun iko. Sai dai lokaci ne kaɗai zai nuna ko darasin zai zama koyi.
Tambaya ta musamman: Shin ya dace a sake duba tsarin kiwon lafiya na Najeriya bayan wannan al’amari?
Ku faɗi ra’ayinku.