01/09/2025
KEVIN DAVID MITNICK SHUGABAN HACKERS NA DUNIYA
Kevin David Mitnick Ba’amurke ne mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kwamfuta, marubuci kuma wanda aka yanke masa hukunci. An fi saninsa da k**a shi da Akai a shekarar 1995 da kuma daurin shekaru biyar a gidan yari saboda laifuka daban-daban da s**a shafi Hacking a kwamfuta da sadarwa.
Kevin David Mitnick (an Haife shi a watan Agusta 6, 1963)
Kevin Mitnick Mashhurin dan datsa Kutse Hacking na Duniya, yayiwa Asusan banki da yawa kutse a kasarsa dama makota, wani lokaci an yanke masa hukuncin daurin shekaru 5 a Gidan gyaran hali saboda tuhumarsa da satar lambar kwamfuta daga manyan kamfanoni masu fasaha da s**a hada da Sun Microsystems, Nokia, da Motorola Corporation.
Wasu sun yi kiyasin cewa haramtacciyar hanyar sadarwarsa ta yanar gizo ta kashe kamfanonin da ke da hannun Jari kusan dala miliyan 300.
Bayan an kaisa Gidan yari ne, ya goge hukuncin daga kundin tattare bayanai na kasar bayan ya kutsa, kuma ya dira kan Kudin Alkalin da ya yanke masa hukunci suma ya kwamushe su daga Asusun ajiyarsa na Banki.
Yanzu haka yana tafiyar da kamfanin tsaro Mitnick Security Consulting, LLC.
Har ila yau, shi ne Babban Jami'in Hacking na sashin kamfanin horar da wayar da kai Kan tsaro KnowBe4, da kuma mamba mai ba da shawara a Zimperium, wani kamfani wanda ke haɓaka tsarin rigakafin kutse ta hannu. ( a firm that develops a mobile intrusion prevention system )
Mitnick tare da William L. Simon da Robert Vamosi, sun Wallafa littattafai hudu, uku kan tsaro na kwamfuta da daya na tarihin rayuwarsa.
© Saliadeen Sicey