
03/08/2025
Alamomi 9 Na Soyayyar Karya
1- Rashin maida hankali akan maganar ka wato ba a damu da maganar ka ba, idan kayi magana ba a daukarta da mahimmanci.
2- Rashin ganawa: bai damu da ya neme ka ba, ko yazo gurin ka, kokuma ya neme ka ta kafofin sadarwa kamar chart, text, ko kiran waya da makamantan su. Kawai dai kuna soyayya ne kamar bakwayi.
3- Rashin gaskiya da gaskayawa (ba a bayyana maka tsantsar gaskiya, kadai ana bayyana maka abinda akeso kasani ne ba wanda ya kamata kasani ba.)
4- Soyayyar da ba za a fadawa iyaye game dashi ba kuna ba a so iyaye ko yan uwa su sani.
5- Rashin kyakkyawar mu'amala irin su shariya, gadara, da makamantan su. Wani lokacin ma a rinka gani kamar alfarma aka yi maka da ake soyayya dakai.
6- Kin yimaka abu domin soyayya.
7- Yin banza da nuna halin ko-in-kula da shaukin da masoyi ke shiga akan soyayya. Ba a rasa masoyi da shiga wani yanayi akan soyayya amma sai kaga ba a damu da halin da yake shiga ba.
8- Kaucewa shiga sabgar wanda ake so, ma'ana, masoyi ya rinka kin shiga harkoki ko lamarin wanda yake so.
9- Rashin aikata abin da zai kwarara muku gwiwa domin cigaban soyayyar ku.
Nakowa ne ni.