Kanawa Radio

Kanawa Radio News, Media and Broadcasting Station.

Bankin Duniya yayi gargadin cewa tsadar man fetur na iya kawo cikas ga ƙoƙarin rage talauci a Najeriya, duk da hasashen ...
07/10/2026

Bankin Duniya yayi gargadin cewa tsadar man fetur na iya kawo cikas ga ƙoƙarin rage talauci a Najeriya, duk da hasashen samun cigaba a bunƙasar tattalin arziki da kuma raguwar hauhawar farashin kayayyaki a shekarar 2026.

Gargadin na ƙunshe ne a cikin sabon rahoton Bankin Duniya kan tattalin arzikin Afirka, inda ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa daga kashi 4.0 cikin 100 a shekarar 2025 zuwa kashi 4.3 cikin 100 a shekarar 2026, kafin ya ƙara tashi zuwa matsakaicin kashi 4.4 cikin 100 a shekarun 2027 da kuma 2028.

Bankin Duniya ya danganta wannan hasashen cigaba da ƙara samun daidaiton tattalin arzikin ƙasa, da ƙarin amincewar masu zuba jari, da kuma farfaɗowar jarin da kamfanoni masu zaman kansu ke zubawa a hankali.

Jam’iyyar NDC a Ƙaramar Hukumar Albasu ta Jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar a mazaɓar Albasu, Bashir Safiyanu ...
07/10/2026

Jam’iyyar NDC a Ƙaramar Hukumar Albasu ta Jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar a mazaɓar Albasu, Bashir Safiyanu Mai Daura, da Jami’in Hulɗa da Jama’a na jam'iyyar Naziru Ibrahim, bisa zargin rashin da’a da wasu batutuwan da s**a shafi yadda suke gudanar da ayyukansu.

Dakatarwar ta kasance ta wucin gadi ne, kuma za ta ci gaba da aiki har sai an kammala binciken da ake yi kan zarge-zargen da ake yi wa jami’an biyu.

Comrade Hudu Sabo Albasu, Sakataren Jinƙai na NDC a Ƙaramar Hukumar Albasu, ne ya karanta wa jami’an biyu takardar dakatarwar.

Rahoton ya ce sama da shugabanni da mambobin jam’iyyar 30 ne s**a sanya hannu kan daukar matakin.

Bayan dakatarwar, jam’iyyar ta naɗa Adamu Ɗan Atan a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, yayin da aka naɗa Kabiru Adamu a matsayin PRO na riƙon ƙwarya.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah Ya yi wa Saminu Yusuf Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe goba...
07/10/2026

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!

Allah Ya yi wa Saminu Yusuf Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano rasuwa bayan yasha fama da Rashin lafiya

Za’ayi jana’izar sa da misalin karfe 8 da rabi na safe a gidansa dake kawon mai gari masallacin bulama

07/10/2026

“Abu Uku Ne Zai Iya Faruwa: Ko A Dawo Da Sarki Aminu, Ko Sarki Sunusi Ya Cigaba, Ko A Kawo Wani” — Umar Labaran Danga

Alh. Umar Labaran Danga ya yi bayani kan halin da ake ciki, inda ya ce akwai abubuwa uku da ka iya faruwa: a dawo da Sarki Aminu, Sarki Sunusi ya ci gaba da sarauta, ko kuma a bar su duka a kawo wani sabon sarki.

Ku kalli cikakken bidiyon domin jin cikakken bayani kan wannan batu.

06/10/2026

Shirin Muryar ‘Yanchi na wannan Rana ta Talata tare da Khadija Muhammad Inuwa

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar ta’aziyya ga ...
06/10/2026

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Muhammad Sani Lawan, Muhammad Anas da Alhaji Ya’u Sarkin Kasuwa, a garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo.

Mamatan sun rasu ne a sakamakon gajeriyar rashin lafiya a gidajensu da ke Garo, a Ƙaramar Hukumar Kabo.

A yayin ziyarar, Mataimakin Gwamna Alhaji Murtala Sule Garo ya isar da sakon ta’aziyya da jaje na Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma Gwamnatin Jihar Kano ga iyalan mammatan tare da addu'ar Allah ya jikan su da rahama yasa aljannatul firdausi ce makomarsu.

A ƙarshen ziyarar, Mataimakin Gwamnan ya kuma ziyarci kabarin mahaifinsa, Marigayi Alhaji Sule Galadima Garo, da ke makabartar Garo, inda aka roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa Marigayin ya kuma sanya Jannatul Firdausi ta zama makomarsa ta ƙarshe.

06/10/2026

SPONSORED:

Mai girma Kwamishinan Kasa Hon Abduljabbar Umar Garko ya ciri tuta a tsakanin Kwamishinonin jihar Kano.

—- Hon Nasiru Baba Kato.
(Dan Jam’iyyar APC)

05/10/2026

Shirin Muryar ‘Yanchi na wannan rana ta Litinin (05/10/2026) tare da Khadija Muhammad Inuwa.

05/10/2026

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alh. Murtala Sule Garo, ya kasance cikin waɗanda s**a halarci jana’izar marigayiya Hajiya Fa’iza Usman Yahaya, matar Alh. Usman Yahaya Kansila (UYK).

Allah Ya karɓi rayuwarta cikin rahama, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya sanya makomarta ta zama Aljanna. Muna kuma roƙon Allah Ya ba iyalanta da sauran waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban rashi.

Allah Ya sa idan lokacinmu ya zo, mu samu kyakkyawan ƙarshe tare da cika da imani.

‎Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na tallafawa Malaman makarantu tare da inganta jin dadinsu da samar da i...
05/10/2026

‎Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na tallafawa Malaman makarantu tare da inganta jin dadinsu da samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa, domin bunkasa harkar ilimi da samar da ingantacciyar al'umma.
‎
‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya da aka gudanar.
‎
‎Gwamnan wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnati, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai daban-daban na bunkasa harkar ilimi.
‎
‎Yakara da cewar gwamnatinsa ta gina sabbin azuzuwa, gyaran tsofaffin makarantu da samar da kayan koyo da koyarwa.
‎
‎

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kanawa Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category