Kasar Kano Jiya Da Yau

Kasar Kano Jiya Da Yau KASAR KANO JIYA DA YAU: Sanin Tarihinmu da Magabatanmu

Labaran Juma'a 25/11/1446AH - 23/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki masu c...
23/05/2025

Labaran Juma'a 25/11/1446AH - 23/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki masu cewa gwamnatinsa na ingiza ’yan Najeriya wajen bin tsarin jam’iyya ɗaya.

Damagun ya bugi ƙirji da cewa duk waɗanda s**a sauya sheƙa daga PDP, babu wanda zai iya fitowa ya ce jam’iyyar ta yi masa wani laifi: “Sai dai ma ta yi musu riga ta yi musu wando.”

Gwamnatin tarayya tayi karar Sanata Natasha kan laifin ‘ɓata suna’ da yin ƙazafi ga Akpabio da Yahaya Bello.

Shugaban babbar jam'iyyar, PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewa yana yi wa jam'iyyar, APC aiki ne shi ya sa rikicin PDP din ya ki ci ya ki cinyewa.

Ana tuhumar mutumin ake zargi da kashe ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila a Amurka da laifin kisa.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar damka wa Mauritius ikon tsibirin Chagos.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar ɗinkin ɗuniya (WFP) ta ce fiye da ƴan gudun hijira dubu 700 a Kenya za su sami kashi 1 ne kawai bisa huɗu na abincin da suke buƙata daga wata mai zuwa saboda katse tallafi.

Gwamnatin Trump ta haramta wa jami'ar Harvard ɗaukar ɗalibai ƴan ƙasashen waje.

Manchester United ta ba da himma don ganin ta sayar da 'yan wasan ta Rashford, Jadon Sancho, da kuma Antony, a matsayin wani bangare na sake fasalin kungiyar.

Duk da rashin buga gasar cin kofin zakarun Turai, Manchester United za ta yi watsi da duk wani yunkuri na son daukar kyaftin dinta Bruno Fernandes.

Dan wasan Real Madrid Modric zai bar kungiyar a karshen kaka.

Tsohon kocin Manchester United Ten Hag zai karbi koyar da Bayern Liverkusen.

18/05/2025

Assalamu alaikum!
Masu kallonmu da saurare!!
Dafatan mun sameku lafiya!!!
Wannan gidan Tv da Jarida za ta ci gaba da gabar maku da shirye-shiryenta daga gobe In sha Allah.
Amma za ta dinga wallafa wasu daga cikin shirye-shiryen a shafinta na Tiktok.
Za mu so ku ƙara bibiyarmu acan kuma muna gab da ba da certificate na girmamawa ga duk wanda suke bibiyarmu Ali da yaushe.
Meye ra'ayinku?

Labaran Yammacin Litinin  14/11/1446AH - 12/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da sh...
12/05/2025

Labaran Yammacin Litinin 14/11/1446AH - 12/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da shirinsa na ci gaba da aikin haƙo danyen mai a yankin Arewa da kuma kammala aikin shimfiɗa bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano.

Kungiyar ASUU ta zaɓi Christopher Piwuna a matsayin sabon shugabanta.

Wani ƙasurgumin ɗan fashi da ke sanya hijabi da niƙabi yana satar babura da ƙwacen waya, ya shiga hannu a unguwar Ɗorayi da ke Kano.

JAMB ta ce za ta yi nazarin ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar kan sak**akon Jarrabawar UTME.

Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi zargin cewa ƙungiyar Boko Haram ta ƙwace mak**an sojoji da kuɗinsu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas.

Ƴansanda sun k**a wani matashi kan zargin kashe saurayin ƙanwarsa a Kano.

’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun harbe wani malami har lahira sannan s**a yi garkuwa da wasu mata uku a wata makarantar sakandaren gwmanati da ke Jihar Zamfara.

Hukumar Kwastam ta ƙaryata zargin sakin wata shinkafa mai guba da ta ƙwace a Legas.

Hare-haren masu iƙirarin jihadi sun kashe gomman mutane a Burkina Faso.

Hamas ta miƙa wa Red Cross Ba'amurken Isra'la Edan Alexander.

China da Amurka sun amince da rage harajin kaya da s**a sanya wa juna.

Amurka ta amince da fararen fata ƴan Afrika ta Kudu a matsayin ƴan gudun hijira.

Ambaliya ta hallaka ɗaruruwan mutane a Gabashin DR Congo.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce akwai yiwuwar ya halarci tattaunawar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Istanbul.

An tabbatar da kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti a matsayin sabon kocin babbar tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brazil.

Labaran Yammacin Asabar 12/11/1446AH - 10/5/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Shugaba Tinubu ya kare matakin sauye-sauyen ta...
10/05/2025

Labaran Yammacin Asabar 12/11/1446AH - 10/5/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Shugaba Tinubu ya kare matakin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka, inda ya ce ya yi haka ne domin ƙasar ta samu ci gaba.

Gwamnonin arewa da kuma sarakunan gargajiya na gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da s**a addabi yankin.

Shugaban Jam'iyyar APC, Ganduje ya ce idan ƴan Najeriya s**a buƙaci komawa tsarin jam'iyya guda, ba wanda zai yi faɗa da hakan, kuma ya kwatanta nasarar tsarin da ta China.

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayar da umarnin haramta sayar da man fetur a karamar hukumar Bama na jihar, ciki har da garin Banki.

Hajj 2025: Maniyyata fiye da 2000 sun tashi zuwa ƙasa mai tsarki.

Gidauniyar attajirin ɗan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ta yi wa masu fama da cutar gwaiwa da taruwar ruwa a wasu sassan jiki fiye da 12,300 tiyata kyauta.

Najeriya za ta kwaso 'yan ƙasarta sama da 15,000 da s**a maƙale a wasu ƙasashe.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun k**a ƴan jarida guda uku da suke aiki da wani gidan rediyo mai zaman kansa a ƙasar.

Dakarun RSF sun kashe mutane da dama a Sudan.

Shugabannin wasu ƙasashen Turai sun buƙci Rasha ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ko ta fuskanci sabo kuma gagarumin takunkumi kan ɓangaren banki da kuma mak**ashi.

An k**a wani mutum kan zargin kashe tsoho mai shekara 87 a Landan.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Indiya da Pakistan sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta nan take.

Firaiministan Pakistan, She]hbaz Sharif ya ce ƙasarsa ta mayar wa da India bikin da ta yi mata.

EPL: Southampton da Manchester City sun tashi 0:0 a wasan yau.

EPL: Everton ta sami nasara akan Fulham da ci 3:1 a wasan yau.

La Liga: Celta Vigo ta sami nasara akan Sevilla da ci 3:2 a wasan yau.

Labaran Yammacin Alhamis  03/11/1446AH - 01/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Fiye da biliyan 71 na bashin karatun ɗaliba...
01/05/2025

Labaran Yammacin Alhamis 03/11/1446AH - 01/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Fiye da biliyan 71 na bashin karatun ɗalibai sun yi ɓatan dabo a Najeriya.

Gwamnatin jihar Katsina ta sanya gobe Juma'a a matsayin ranar hutu sabida ziyarar da Shugaba Tinubu zai kai jihar.

Gwamnan jihar Edo ya kara mafi karancin albashi zuwa dubu 75 a jihar.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashin teku ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa.

Gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya na taro kan tsaro a yankin.

Aikin gina tashar jirgin ƙasa ta zamani a Kano, ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana ci gaba da tafiya babu k**a hannun yaro.

Wata mota ta kone, bayan ta k**a da wuta yayin da take tsaka da tafiya akan titin gidan gwamnatin Kano, kusa gidan Sarki na Nasarawa.

Wata gobara da ta tashi a wata shahararriyar kasuwar wayoyin salula da ke ‘Challenge Market’, a Ilorin Jihar Kwara, kuma ta yi mummunar ɓarna.

Kamfanin CBEX da ya damfari ƴan Najeri sama da Triliyan ɗaya ya dawo aiki.

India za ta hukunta masu hannu kan hari a yankin Kashmir.

Fiye da tawagar mutane 150 da kuma jiragen sama masu kashe gobara ne ke ci gaba da ƙoƙarin shawo kan abin da aka bayyana da mummunar wutar dajin da ta afkawa Isra'ila wadda ba a taɓa ganin irinta ba a tarihi.

Matar da ta fi kowa tsufa cikin mutane, Sister Inah Canabarro ta rasu tana da shekara 116 a duniya.

An k**a masu fasaƙwaurin zinare a Ghana.

Bankin Japan ya rage hasashen bunƙasar tattalin arziƙin ƙasar.

Kamala Harris ta zargi Trump da haddasa taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

An kashe wani babban ɗan majalisar Kenya a wani harin bindiga da aka kai masa a wata unguwa da ke Nairobi.

Ukraine da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar haƙar ma'adinai wadda Trump ya buƙata.

Syria: Mutane sama da 100 sun mutu a cikin kwanaki biyu a rikicin addini.

Labaran Safiyar Alhamis 03/11/1446AH - 01/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Shugaban hukumar EFCC, ya musanta zargin da a...
01/05/2025

Labaran Safiyar Alhamis 03/11/1446AH - 01/05/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Shugaban hukumar EFCC, ya musanta zargin da ake yi wa Shugaba Tinubu, na yin amfani da hukumar wajen muzguna wa jam'iyyun adawa.

Gwamnati ta ƙaddamar da yaƙi da cutar sanƙarar bakin mahaifa a Bauchi.

Ƙungiyar Lauyoyi reshen jihar Lagos ta karrama wani jami'in ɗansanda ɗan arewa, CSP Umar Ali Jada da lambar yabo sak**akon bajintarsa ta magance matsalar garkuwa da jama'a a jihar.

Hukumomi a jihar Borno sun tabbatar da tashin gobara a rumbun adana mak**ai da ke barikin sojoji da ake kira 'Giwa Barrack' a birnin Maiduguri.

Gwamnan Kano, ya amince da ware kuɗi har Bilyan daya da milyan 111 don samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a fadar gwamnatin Kano.

Tashin abubuwan fashewa a Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri ya girgiza unguwanni da dama a Jihar Borno. Hukumomi sun bayyana cewa ma'aikatan ceto na kokarin shawo kan lamarin.

Wata kotun Majistare a jihar Ogun ta yanke wa mawaki Habeeb Okikiola hukuncin daurin wata uku a gidan yari bisa laifin cin zarafin dan sanda.

Mai Martaba Sanusi II ya naɗa sabon dagaci a garin Kenfawa da ke karamar hukumar Garun Mallam a jihar Kano, duk da dakon hukuncin kotu da ake yi.

Kwastam ta k**a Jirage marasa matuka da sauran kayayyaki da darajarsu ta haura naira Biliyan 921 a Legas.

Wata kotun soji ta yanke wa wani kurtun soja hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifn kashe buduwarsa a Enugu.

Mahukunta a Abuja sun markade babura 601 da a k**a suna aiki ba bisa ƙa'ida ba.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Gabon bayan dakatar da ƙasar saboda juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2023.

Hukumomin Amurka sun yi biyayya ga umarnin kotu inda s**a saki ɗalibi ɗan Falasɗinu da jami'an shige da fice s**a tsare a farkon watan nan.

UEFA Champions League: Barcelona da Milan sun tashi 3:3 a wasan jiya.

Labaran Yammacin Laraba  02/11/1446AH - 30/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Karon farko tun bayan zamowarsa shugaban ƙas...
30/04/2025

Labaran Yammacin Laraba 02/11/1446AH - 30/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Karon farko tun bayan zamowarsa shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai ziyarci Jihar Katsina.

NNPC ya sallami shugabannin matatun man fetur uku na Najeriya da ƙarin wasu manyan ma'aikata.

Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya ta naɗa Sheikh Dokta Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta.

Ranar Ma’aikata: Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Alhamis a matsayin ranar hutu.

Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da s**a yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi.

Tsohon gwamnan soja na jihohin Cross River, Akwa Ibom (wanda a baya ake kira jihohin Kudancin Gabas), Manjo-Janar Paul Ufuoma Omu, ya rasu.

Shaguna kusan 500 ne s**a ƙone a kasuwar Terminus ta Jos.

Sojoji sun daƙile harin yan Bindiga, sun ceto Fasinjoji 6 a jihar Taraba.

Shugaban Koriya ta Arewa ya ba da umarnin shirya makamin nukiliya.

Gobarar daji wacce tsananin zafi da iska mai ƙarfi suke izawa ta afka tsakanin Birnin Kudus da Tel Aviv, inda ta tilasta wa mutane fita daga gidajensu da rufe wata muhimmiyar babbar hanya.

Wata tsohuwa mai shekara 80 a kasar Turkiyya za ta shafe sama da shekara 4 a gidan yari, saboda ta daki jikarta ’yar shekara 18 da silifa a lokacin da suke takaddama.

Tattalin arzikin Amurka ya ragu karon farko cikin shekara uku.

Jagororin Indiya sun gudanar da taro yayin da zaman tankiya tsakaninta da Pakistan ke ƙara ta'azzara.

Gwamnatin Nijar ta ɗauke wa sababbin kamfanoni biyar haraji.

'Yansandan Sweden sun k**a matashin da ya harbe mutum uku.

Pakistan ta ce Indiya na shirin kai mata hare-haren soji yau ko gobe.

An gudanar da gangamin goyon bayan kaftin Ibrahim Traore a Burkina Faso.

Kocin Inter Milan Simone Inzaghi ya ce ba sa tsoron Barcelona duk da cewa ya ce ya yarda tauraruwar kungiyar tana haskawa sosai a wannan lokaci.

Labaran Safiyar Laraba 02/11/1446AH - 30/04/2025 CE Ga Takaitattun Labaran.Gwamnatin tarayya tace Ɗalibai za su fara rub...
30/04/2025

Labaran Safiyar Laraba 02/11/1446AH - 30/04/2025 CE Ga Takaitattun Labaran.

Gwamnatin tarayya tace Ɗalibai za su fara rubuta jarrabawar WAEC da NECO ta amfani da kwamfuta.

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar PDP, ya ce ko a jikinsa kan ficewar da mambobinsa ke ci gaba da yi zuwa APC mai mulki.

Wata gagarumar gobara ta tashi a cikin dare a Kasuwar Terminus da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato, inda aka tabka asarar dukiya mai tarin yawa.

Aisha Achimugu ta fara yajin ƙin cin abinci a inda take tsare a EFCC.

Wata kungiya a Katsina tace wasu kwamandojin 'yan bindiga da dama sun mika wuya sakamkon shiga tsakanin da ta yi a sulhun da aka yi da su.

Ƴan bindiga sun kashe shanu 37 a kauyen Tashek dake karamar hukumar Riyom a jihar Filato.

Canada tace ta cancanci mutuntawa daga Amurka kuma za ta shiga tattaunawar kasuwanci da tsaro ne kawai a bisa sharuɗan da ta gindaya.

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta koyi darasi daga katsewar lantarkin da ta faru bagatatan a Sifaniya da Portugal.

Sojojin Isra'ila sun saki jami'in lafiya a Gaza da s**a tsare.

Marcus Rashford na iya komawa Manchester United da wuri daga aron da yake a Aston Villa bayan ya ji rauni a kafarsa.

Manchester City da Liverpool suna sha'awar sayen dan wasan bayan Juventus Cambiaso, wanda da alama zai bar kungiyar sa a bazara.

Brazil na tattaunawa da kocin Real Madrid Carlo Ancelotti game da zama sabon kocinta, inda ake ci gaba da tattaunawa game da ma'aikatan da za su dafawa kocin dan Italiya.

UEFA Champions League: PSG ta sami nasara akan Arsenal da ci 1:0 a wasan jiya.

Labaran Safiyar Talata 01/11/1446AH - 29/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwarta kan yad...
29/04/2025

Labaran Safiyar Talata 01/11/1446AH - 29/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun karuwar aikata laifuka da damfara ta Intanet a yammacin Afrika.

'Yan Boko Haram sun hallaka mutum bakwai a yankin Chibok.

Wasu abubuwan fashewa da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne s**a dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.

Mataimakin gwamnan Neja Yakubu Garba ya musanta yin murabus daga muƙaminsa.

Ƴan ta'addan Boko Haram sun hallaka mafarauta da ƴan sa kai na CJTF guda 10 a kauyen Kwabre na karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.

Sojoji sun ceto mutum 50 da aka sace, sun kwato shanu 32 a jihar Katsina.

Iran ta ce sakaci ne ya haifar da mummunar fashewa a Iran.

Manyan Limaman cocin Katolika da ke ganawa a Fadar Vatican sun ayyana Larabar makon gobe a matsayin ranar soma shirin zaɓen magajin Fafaroma Francis.

Ghana ta kaddamar da shirin raba wa dalibai mata Kunzugun al'ada kyauta.

An shiga ɗimuwa a Turai sak**akon katsewar wutar lantarki.

Seria A: Udinesse da Bologna sun tashi 0:0 a wasan jiya.

Labaran Yammacin Litinin  30/10/1446AH - 28/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Mutumin da aka k**a a jihar Ogun ya shaida ...
28/04/2025

Labaran Yammacin Litinin 30/10/1446AH - 28/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Mutumin da aka k**a a jihar Ogun ya shaida wa jami'an tsaro cewa ya kai shekara 10 yana sayar da sassan jikin dan Adam.

Gwamnatin Kano ta gano ma’aikatanta 240 da ke ƙarɓar albashi sau biyu a duk wata, da wasu 217 da ke amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) guda ɗaya.

NDLEA ta ce ta k**a miyagun ƙwayoyi na naira biliyan ɗaya a Kano da Legas.

Makafi 37 sun zana jarabawar JAMB a jihar Bauchi.

Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya.

Zanga-zangar ɗalibai ta tilasta rufe kwalejin Adamawa kan rashin lantarki.

Ƙungiyar Amnesty International ta zrg gwamnatin tarayya da gazawa wajen kare rayuka da dukiyar al'umma lamarin da ya sanya masu aikata laifi ke kai farmaki tare da hallaka al'umma.

A wannan yanayi na matsin tattalin arziki a Najeriya, mata na gasar neman haihuwar ’yan uku domin cin gajiyar tallafin tsabar kuɗi da abinci da tufafi da ragunan suna a Jihar Sakkwato.

Hukumar NDIC ta fara biyan masu ajiya a bankin Heritage kuɗaɗensu.

Kotu a Abuja ta yankewa mai gidan fitacciyar mawaƙiyar bushara ta Najeriya Osinachi hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bankin Sifaniya ya ce harkokin hada-hada ta intanet na ci gaba da aiki yadda ya k**ata, sai dai an ambato wasu masu cirar kuɗi sun fuskanci ƙalubale a na’urar ATM.

Falasɗinawa sun ba da bahasi kan Isra'ila a kotun duniya.

Ɗaukewar lantarki ta jefa mazauna Sifaniya da Portugal cikin duhu.

Iran ta yi tayin bai wa ƙasashen Afirka fasaharta a fannin tsaro.

Koriya ta Arewa ta amince sojojinta na taya Rasha yaƙar Ukraine.

An ciro gawar mutane 68 a ƙarkashin baraguzai bayan harin Amurka a Yemen.

Watakila Marcus Rashford, wanda ke buga wasannin aro a Aston Villa daga Manchester United, zai yi jinya har karshen kakar nan.

Labaran Yammacin Lahadi 29/10/1446AH - 27/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke m...
28/04/2025

Labaran Yammacin Lahadi 29/10/1446AH - 27/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke mutane tara kan zargin satar mutane.

Rundunar ƴansanda ta ce ta kuɓutar da mutum goma da ƴan bindiga s**ayi garkuwa da su a kan babban hanyar Funtua zuwa Gusau.

Tsohon Babban Sakataren Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa, Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin murƙushe ’yan adawa da kuma rufe bakinsu ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati.

Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto tace ta k**a wani mutum dauke da mak**ai da ake zargin yana da alaka da ƴan ta'adda.

Ƴan sanda a jihar Neja Niger sun k**a Adaidaita sahu 56, da motoci 94 ƙasa da kwanaki biyu da kafa dokar takaita zirga zirga a Birnin Minna.

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta k**a wani yaro dan shekaru 16 dauke da bidiga.

A ranar Asabar ne mayaƙan Boko Haram s**a far wa wasu manoma har s**a kashe mutum 14 a yankin Gwoza da ke jihar Borno.

Fitaccen jarumin fina finan Kannywood Muhammad Shuaibu wanda aka fi sani da Baba Hasin ya rasu yana da shekara 68 a duniya.

Ƴan sanda sun k**a wani mutum dauke mak**ai da ake zargin yana da alaka da ƴan bindiga a jihar Sokoto.

Girgizar ƙasa ta hallaka mutum huɗu, ta jikkata 13 a Aljeriya.

Mutum tara su mutu bayan da mota ta kutsa cikin taron jama'a a Canada.

An k**a ɗan Ukraine kan zargin kashe Janar ɗin Rasha.

Saudiyya ta k**a mutum kusan 13,000 da s**a shiga ƙasar ba bisa ka'ida.

Rundunar Sojan Nijar ta ce an k**a wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harin da yayi sanadin mutuwar sojojin ta 12.

Uganda ta sanar da kawo ƙarshen annobar Ebola a wannan karo.

Tanzania ta janye haramcin shigar da kayan gona daga Malawi da Afrika ta kudu.

Za a iya dakatar da Rudiger tsawon lokaci bayan jifan alkalin wasa da ƙanƙara.

EPL: Bounemouth da Manchester United sun tashi 1:1 a wasan yau.

Seria A: Roma ta sami nasara akan Milan da ci 1:0 a wasan yau.

Labaran Yammacin Alhamis 26/10/1446AH - 24/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.Shugaba Tinubu ya ba da umarnin gaggawa da a...
24/04/2025

Labaran Yammacin Alhamis 26/10/1446AH - 24/04/2025CE Ga Takaitattun Labaran.

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile kashe-kashe a jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara.

Gwamnatin tarayya ta sanar cewa za a bai wa mahajjata kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.

Sojoji sun dakile yunkurin kai hari tare da kashe ɗan bindiga a Filato

Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta k**a wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7.

Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa ta k**a wani mutum bisa zargin kashe matar ƙaninsa a ƙauyen Gunka da ke karamar hukumar Jahun a jihar.

Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta sallami ɗaya daga cikin malamanta, daga jami’ar bisa zargin neman yin lalata da wata ɗaliba matar aure da ke karatun digiri na biyu.

Yajin aikin ma'aikatan NIMET ya hana wasu jirage tashi a Najeriya.

Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano, ta mayar da martani da nuna jin daɗi ga ficewar Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, zuwa Jam’iyyar APC inda ta ce ficewarsa za ta kawo zaman lafiya a jam’iyyar.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da s**a fi zaman lafiya a Najeriya.

Baffa Bichi, Kabiru Rurum, Sha’aban Sharada da wasu ƴan siyasa a Kano sun koma jam’iyyar APC.

Direban mota ya hallaka jami'in Karota da wuka a jihar Kano.

Gwamnatin Kano ta soke tsaftar muhalli a watan Afrilu saboda jarabawar JAMB.

Rasha ta ƙaddamar da ƙazamin hari kan birnin Kyiv.

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Congo da mayaƙan M23.

Mutanen da s**a mutu a harin da Rasha ta kai Kyiv sun kai 12.

An gurfanar da tsohon shugaban Koriya ta Kudu kan zargin cin hanci.

Tanzaniya ta haramta shigo da kayayyaki daga Afirka ta Kudu da Malawi.

Ƙasar Benin ta tabbatar da kashe sojojinta 54

Van Nistelrooy bai da tabbaci ko zai ci gaba da horar da Leicester City.

Address

Airport Road
Kano
2355

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kasar Kano Jiya Da Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kasar Kano Jiya Da Yau:

Share

Category