24/11/2025
Lokacin da nake Jami’a (kafun a kore ni) akwai wani abokin Gwagwarmayan mu (bana son inyi tagging din shi amma ze ga wannan rubutun) yayi broke se yake fadawa wani abokin shi bakano yana bukatar Emergency N50,000 ya biya kudin makaranta sannan yayi wani lalura be ma san ta ina ze fara ba, Abokin yace masa shi be san inda zaa samo N50k ba, Amma dai yana da numban wayan Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, bari ya bashi kila ya dace!
Ya karbi lambar kwankwaso ya zauna ya tsara masa Text message cewa shi bakano ne, yana Jami’ar ABU yana neman wani opportunity a wata kasa an kirashi visa interview a Abuja kuma bayi da ko sisi da ze je Abuja, be da masauki b***e guzuri, ya rubuta masa cewa Interview din zaayi nan da sati 3.
Shi dai kawai ya tura text ne ba wai don yana sa rai da wani abu ba!
Kwatsam, bayan kwana 17 yana kwance aka kirashi da sassafe da wata lamba, kai ne wane? Yace eh, kana da jarabawa ranar kaza (har ya ma manta saboda kasan halin karya) be gane mene ake fadi a waya ba, se da me kiran yace masa ba kai ne kayiwa Sen Kwankwaso message ba? Se yayi zumbur ya miqe, yace masa ai ya dauka yan damfara ne!
Aka fada masa anyi masa booking hotel kaza a Abuja na kwana 5, zasu bashi Abinchi kullum sau uku, sannan Sen. Yace a bashi N250,000 yayi kudin mota yazo ya koma, sannan yayi zirga zirga a Abuja, Idan kuma akwai wani matsala ko taimakon da yake bukata, ya kira wannan da ya kirashi! A karshe yace ya koma numban Sen yayi masa Godia kuma ya fada masa yadda s**ayi a text kawai ze gani In sha Allah.
Ya tashi ya tafi Abuja, ya sha barcin shi na kwana 5 a hotel, ya karbo N250k din shi ya biya kudin makaranta, ya siya waya, ya dinka sabbin kaya ya dawo Zaria abun sa!
Har yau, Kwankwaso beyi replying message din sa ba, be san shi ko dan gidan waye bane, kuma be nemi ya sani ba, kawai dai yaga message an ce bakano ne, kuma ana neman kudin makaranta!
Da ace wani dan siyasar ne, abunda zaa fara dubawa shine: sau nawa yake posting Alheri ne, kuma a rana sau nawa yake yabon sa Idan aka gama vetting din sa aka ga he’s clean kuma yana posting kullum , sannan se a tura masa N30,000
Daga Elhassan Kauran Mata