30/06/2022
MUN FUSKANCI KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN ZUL-HIJJAH 1443/2022 DA YARDAR ALLAH.
Kwanaki Goman farko na zul-hijjah suna da fifiko akan ko waɗanne ranaku kamar yadda ya tabbata daga Manzon ALLAH (ﷺ) saboda sun ƙunshi manya manyan ibadodi acikinsu: Sallah, azumi, Sadaƙa, hajji, Wanda basa samuwa a lokaci ɗaya face sai acikin goman zul-hijjah. Kamar yadda Manzon ALLAH (ﷺ) ya bayyana mana darajarsa.
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Ayyuka masu falala basu fi falala acikin wasu kwanaki ba kamar waɗannan kwanaki goman (Zul-hijjah) sai sahabbai s**a ce; Ya Manzon ALLAH koda jahadi domin ALLAH? Yace: koda jihadi domin ALLAH, sai dai mutumin da ya fita yana sadaukar da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai ba.” [Bukhari ya ruwaito shi]
Sai muyi ƙoƙari wajen ganin mun samu wannan falala dake tattare da waɗannan kwanaki goman kuma mu yawaita hailala da dukkan nau'o'in ayyukan da zasu kai mu ga samun lada.
ALLAH Ya kaimu ya kuma taimake mu ya bamu iko da damar aikata ingantattun ibadodi acikin waɗannan kwanaki da zamu fuskanta (Aameen)
Masha Allah, Allah ka tabbatar mana da Nasara, Ameen.
Mungode.
📜✍🏽:- Alh.Isah Mustapha (Chief Tailor)
Chairman;
Taragon A.A Zaura Media Team, Kano State.
30/June/2022.