Gasau news Reporter

Gasau news Reporter Nationwide

 -Huk**ar Hisbah ta jihar Kano ta gamsu da sahihancin Auren da kwamandata mai kula da karamar hukumar Rano ya daura a kw...
05/02/2023

-Huk**ar Hisbah ta jihar Kano ta gamsu da sahihancin Auren da kwamandata mai kula da karamar hukumar Rano ya daura a kwanakin baya da wata bazawara, wacce a shekarun baya, ya ta ba neman yar ta ta da aure kuma hakan bai yu ba.

Da yake mikarahoton binciken kwamatin, shugaban kwamitin kuma mataimakin babban kwamanda hukumar mai kula da aiyuka na musanman, malam Hussain Ahmad Cediyar Kuda shine ya furta hakan a lokacin da yake ga batar da rahotonsa a gaban babban kwamanda a shelkwatan hukumar da ke unguwar sharada.

Yace duba da yadda kwamatin ya gudanar da bincike a tsakanin bangarorin da ake zargi, da aikata tabargaza musanman, wacce aka daura aure, ya kara da cewar dogaro da hujjuji kwara guda biyar Wanda kwamatin ya gano a yayin binciken, shi ya da da tabbatar da sahihancin auren a tsakanin bazawarin da bazawarar.

Wakilinmu Abubakar Sale Yakub, ya rawaitomana cewa, lokacin da yake karban kunshin rahoton kwamatin, babban kwamanda hukumar Hisbah na jiha, Dr. Harun Muhammad Sani Ibin Sina ya godewa yan kwamatin bisa nuna gogewa tare da jajircewa domin tantance gaskiyar abinda ake zargi.

Sheik Ibn Sina yayi kira ga jama'a da su guji yada labaran da ba'a tantance sahinhancinsa ba.

El-Rufai ya taro 'match', ya ce a duk fadin Arewa babu sauran dattijo ko daya.Daya daga dattawan Arewa ya ce El-Rufai ba...
04/02/2023

El-Rufai ya taro 'match', ya ce a duk fadin Arewa babu sauran dattijo ko daya.

Daya daga dattawan Arewa ya ce El-Rufai ba zai gama lafiya ba, kuma zai gani.

Bafarawa ya ce duk wanda ya tozarta Arewa da dattawanta zai sha kunya. MENENE RA AYIN KU AKAN MAGANAR DA EL-RUFA I YAYI AKAN DATTAWAN AREWA

Hon. Ali Hamza Gasau Daya daga cikin jigajigan jagororin jama'iyya PDP Na Mazabar panshekara karamar hukumar kumbotso ya...
20/01/2023

Hon. Ali Hamza Gasau
Daya daga cikin jigajigan jagororin jama'iyya PDP Na Mazabar panshekara karamar hukumar kumbotso yana kira al'ummar Mazabar panshekara da karamar hukumar kumbotso da suje s**arbi katin zaben su yayi wannan kiranne lokaci da s**a yi shira wakiliyar
GASAU NEWS REPORTER

Bayan an yi canjin kudi a Najeriya, Gwamnan CBN ya rage adadin kudin da mutum zai iya cirewa a kullu yaumin.Kungiyar gwa...
18/01/2023

Bayan an yi canjin kudi a Najeriya, Gwamnan CBN ya rage adadin kudin da mutum zai iya cirewa a kullu yaumin.

Kungiyar gwamnonin Najeriya za ta zauna da Godwin Emefiele domin jin hikimar tsare-tsaren da ya kawo.

Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar da sanarwar nan.

Shugabannin APC A Arewacin Najeriya Sun Yi Barazanar Ficewa Daga Jam’iyyar.
17/01/2023

Shugabannin APC A Arewacin Najeriya Sun Yi Barazanar Ficewa Daga Jam’iyyar.

Shugabannin APC A Arewacin Najeriya Sun Yi Barazanar Ficewa Daga Jam’iyyar. Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC na kananan hukumomi 16 na jihar Kwara sun sanar da shugabannin jam’iyyar aniyarsu ta …

Wani dan Najeriya ya amsa laifin bude asusun ajiyar banki na bogi har guda 470 da ya yi amfani da su wajen damfarar bank...
17/01/2023

Wani dan Najeriya ya amsa laifin bude asusun ajiyar banki na bogi har guda 470 da ya yi amfani da su wajen damfarar bankunan Amurka da dama.
https://rfi.my/94eE.f

Malamai kaɗai s**a rage masu faɗa a ji a arewa, su ma sun kusa zama masu faɗa aƙi ji, saboda wasu ɓata gari a cikinsu na...
17/01/2023

Malamai kaɗai s**a rage masu faɗa a ji a arewa, su ma sun kusa zama masu faɗa aƙi ji, saboda wasu ɓata gari a cikinsu na shirin shigar da malamtan siyasa dumu dumu.

“Credit” Shafin Sheikh Sani Khalifa Zaria.

An Kammala Aikin Gina Katafaren Kamfanin Shinkafa Mafi Girma A Nahiyar Afirika Mangal Rice A Jihar Katsina DAGA Comr Nur...
17/01/2023

An Kammala Aikin Gina Katafaren Kamfanin Shinkafa Mafi Girma A Nahiyar Afirika Mangal Rice A Jihar Katsina

DAGA Comr Nura Siniya.

Attajirin Ɗan-kasuwa shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max-Air da kamfanin gine gine da tsare tsare na Afdin Construction Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, ya kammala aikin gina katafaren kamfanin shinkafar da yake ginawa a jihar Katsina mai suna “Mangal Rice” wanda za a riƙa fitar da shinkafa tan dubu 300 a kowace rana.

Kamfanin ya tsaftace shinkafarsa ta yadda za tayi gogayya da kowace irin shinkafa a duniya. inda a yanzu za a fara fitar da Shinkafar a kasuwannin duniya.

Haka zalika a cikin kamfanin an samar da bangaren yin takin zamani mai ƙyau "Gobarau Agro Fertilizer” domin amfanin manoman rani dana damina.

“A cewar Babban daraktan kamfanin Alhaji Fahad Dahiru Mangal , ya ce kamfanin zai riƙa fitar da shinkafa tan dubu ɗari uku 300,000 a kowace rana.

Kamfanin ya laƙume kuɗi har kimanin biliyan 20b. inda zai samar da ɗinbin guraben ayyukan yi ga matasa har mutun dubu goma tare da bunƙasa tattalin arziƙin jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.

Allah Ya ƙara bamu zaman lafiya da ƙaruwar arziƙi a jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.

TSADAR RAYUWA: A yayin da tsadar rayuwa ke damun al'ummar Afirkiyya musamman ma Afirka ta yamma, ita ma jamhuriyyar Nija...
17/01/2023

TSADAR RAYUWA: A yayin da tsadar rayuwa ke damun al'ummar Afirkiyya musamman ma Afirka ta yamma, ita ma jamhuriyyar Nijar ta hau layi wajen ƙara kuɗin sayen Data ga ƴan ƙasar.

Domin haka gidan jaridar Nijar Hausa 24 ya wallafa wa ƴan Najeriya cewa "Idan ka daina ganin abokanka na Nijar a online, to tsadar Data ce ta ɓoye shi domin 1GB daidai ta ke da N3000.

Ku danna nan 👉 Arewa Pyramid Hausa ku yi following ɗin mu domin samun labarai na cikin gida da wajen Najeriya.

17/01/2023

SSS sun dira a CBN sun kuma mamaye ofishin Emefiele

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, SSS sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya, CBN inda s**a kwace ofishin gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a kwai wata jiƙaƙƙiya tsakanin jami’an SSS da Emefiele kan zargin tallafawa ta’addanci.

A baya dai hukumar ta SSS ta nemi kotu ta bata izinin k**a Emefiele amma ya fice daga kasar domin hutun shekara da zai kare a gobe 17 ga watan Janairu.

Sai dai a watan Disamba ne babbar kotun birnin tarayya ta haramtawa SSS k**a, gayyata, ko kuma tsare Emefiele.

Amma kuma a yau Litinin da jami’an SSS da s**a isa hedikwatar ta CBN, sun shigo da motoci kusan 20 dauke da jami’an tsaro.

Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Emefiele.

Peter Afunanya, mai magana da yawun SSS, har bai amsa sakon neman bahasi da wakilin Daily Nigerian ya aike masa ba.

16/10/2022

KALLI WANNAN VIDEON ASALIN GARGAJIYAR, FULANI KAIMA KANA DA TAKA GARGAJIYAR?

Address

Gasau Transformer Street
Kano
GASAUTOWN

Telephone

+2347038212567

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gasau news Reporter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gasau news Reporter:

Share