07/05/2026
"Naira Biliyan 2.79 Don Ƙarfafa Matasa Manoma — Wani Babban Tsarin Barau I. Jibrin Na Sauya Tattalin Arzikin Kano
A wani babban yunƙuri na bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin noma na zamani da aka ware masa sama da Naira biliyan 2.79 domin tallafa wa matasa manoma a Kano ta Arewa da Jihar Kano baki daya.
Shirin, wanda ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen ƙarfafa matasa a yankin Arewa, ya mayar da hankali ne wajen samar da sabbin attajiran manoma ta hanyar amfani da ilimin zamani, fasahar noma da tsarin gudanarwa mai ɗorewa.
A ƙarƙashin wannan tsari, an ware Naira miliyan 5 ga kowane matashi manomi guda 558 ba tare da an ɗora musu nauyin biyan kudin ruwa ba. Wannan tallafi zai ba su damar fara harkar noma daga tushe ko kuma faɗaɗa gonakinsu domin ƙara yawan amfanin gona da ribar da suke samu.
Wannan shiri ya zo ne a daidai lokacin da matasa da dama ke fama da rashin aikin yi da ƙarancin jari, inda aka tsara tsarin cikin hikima domin bai wa matasa damar dogaro da kansu ta hanyar noma mai amfani da fasaha, injina da dabarun zamani.
Masu anfani da shirin za su samu damar shiga harkokin noman zamani kamar noman hatsi, kayan lambu, kiwon amfanin gona mai amfani da ban ruwa, da sauran fannoni da ke taimakawa wajen samar da wadataccen abinci da bunƙasa tattalin arziki.
Baya ga tallafin kuɗi, an kuma raba taki da kayan aikin noma ga manoma a faɗin ƙananan hukumomin Kano domin ƙarfafa yawan amfanin gona da rage matsalolin da manoma ke fuskanta wajen samun kayan aiki.
Wannan mataki na nuna yadda Sanata Barau ke ƙoƙarin mayar da noma ginshiƙin tattalin arzikin matasa, tare da rage zaman kashe wando da kuma ƙarfafa samar da abinci a cikin gida.
Masana harkar noma da tattalin arziki sun bayyana cewa irin wannan shiri na da matuƙar tasiri wajen rage talauci, bunƙasa kasuwanci a karkara, da kuma rage dogaro da shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje.
Haka kuma, shirin zai taimaka wajen samar da dubban ayyukan yi kai tsaye da kuma waɗanda ba kai tsaye ba, musamman ga matasa masu sha’awar harkar noma amma s**a rasa jari da kayan aiki.
Al’umma da dama sun yabawa wannan shiri, suna mai bayyana shi a matsayin wata sabuwar hanya ta gina matasa masu dogaro da kai, masu iya samar da abinci da kuma taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Ana sa ran cewa cikin ƴan shekaru masu zuwa, waɗanda s**a amfana da wannan tallafi za su zama manyan manoma masu zaman kansu, tare da ɗaukar ma’aikata da kuma taimakawa wajen ciyar da al’umma gaba."