CCN Hausa

CCN Hausa CCN Hausa – Creative Communication Network Hausa– Za ta dinga kawo muku labarai ingantattu masu kayatarwa.
(2)

Muna karbar tallan kasuwanci ko na siyasa. 08035996090 Whatsapp kaɗai, idan har ka san ba talla za ka ba mu ba, don Allah kar ka yi mana magana 🙏

SOYAYYAR ANNABI: Mutum sama da dubu 500 ne s**a halarci gagarumin taron Maulidin Manzon Allah SAW na Takutaha a garin Za...
01/09/2026

SOYAYYAR ANNABI: Mutum sama da dubu 500 ne s**a halarci gagarumin taron Maulidin Manzon Allah SAW na Takutaha a garin Zaria, da aka gudanar yau talata. An gudanar da taron cikin salati, yabo da wa’azi, tare da tunawa da rayuwar Manzon Allah SAW da koyarwarsa, cikin yanayi na ƙauna da girmamawa gare shi.

Allah ya ƙara wa Annabi daraja

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Sama da mutane miliyan biyar ne s**a fito a yau a Kano domin zagayen Mauludin Manzon Allah SAW na Takut...
01/09/2026

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Sama da mutane miliyan biyar ne s**a fito a yau a Kano domin zagayen Mauludin Manzon Allah SAW na Takutaha, inda s**a nuna ƙauna da soyayyarsu ga Manzon Allah SAW. Mahalarta sun cika titunan birnin Kano, cikin yanayi na salama da yabon Manzon Allah SAW

YANZU-YANZU: Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara ya gama shirya fito da sandar gashin Manzon Allah SAW wanda zai gabatar wa...
01/09/2026

YANZU-YANZU: Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara ya gama shirya fito da sandar gashin Manzon Allah SAW wanda zai gabatar wa masoya domin su gani a babban taron takutaha da ake gudanarwa yau. Wannan na daga cikin abubuwan da s**a ƙara jan hankalin mahalarta taron, yayin da dubban masoya ke ci gaba da halarta domin nuna soyayya da girmamawa ga Manzon Allah SAW.

YANZU-YANZU: Dubban masoya Manzon Allah SAW kenan a yayin bikin takutaha yau a birnin Kano tare da mawaƙi mai yabon Manz...
01/09/2026

YANZU-YANZU: Dubban masoya Manzon Allah SAW kenan a yayin bikin takutaha yau a birnin Kano tare da mawaƙi mai yabon Manzon Allah Shehi Tajul izzi, inda s**a bayyana ƙaunarsu da girmamawarsu ga fiyayyen halitta. Allah ya ƙara wa Annabi daraja

YANZU-YANZU: Dubban al’ummar Musulmi sun fito kan tituna a jihar Legas domin gudanar da zagayen Mauludin Manzon Allah SA...
01/09/2026

YANZU-YANZU: Dubban al’ummar Musulmi sun fito kan tituna a jihar Legas domin gudanar da zagayen Mauludin Manzon Allah SAW tare da bayyana ƙauna da soyayyarsu ga fiyayyen halitta.

Mahalarta sun rika salati da yabon Annabi SAW cikin yanayi na farin ciki da natsuwa, suna tunawa da rayuwarsa, kyawawan halayensa da koyarwarsa.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen wajeGwamnatin Tarayya ta ƙaddama...
01/09/2026

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen waje
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri mai suna “Hire from Nigeria” (wato 'A ɗauki ma'aikata daga Nijeriya') domin bai wa ’yan ƙasar nan damar yi wa kamfanoni da masu ɗaukar ma’aikata na ƙasashen waje aiki.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wani taron manema labarai da aka yi a ofishin sa a Abuja.

Ya ce: “Ƙaddamar da wannan shiri wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da Nijeriya take yi na sanya ɗaya daga cikin manyan kadarorin ƙasar mu, wato mutanen mu, a sahun gaba wajen hulɗar tattalin arzikin mu da duniya.”

Ya ce yawan matasan Nijeriya, da ɗimbin ƙwararrun ma’aikatan ta da kuma bunƙasar fasahar zamani sun ba ƙasar damar yin gogayya da sauran ƙasashe a fagen tattalin arzikin duniya.

Idris ya ce: “Makomar tattalin arzikin Nijeriya za ta ƙara dogara ne kan ƙwarewa, ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha da kuma ƙwazon jama’ar mu. A shirye Nijeriya take ta yi gogayya a fagen duniya. A shirye ƙwararrun ’yan Nijeriya suke su yi aiki, kuma ya kamata duniya ta mayar da hankali kan Nijeriya."

Ya ƙara da cewa gangamin ya haɗa ma’aikatun tarayya na Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari da na Ilimi, NATEP, iDICE da kamfanoni masu zaman kan su domin haɗa ƙwararrun ’yan Nijeriya da masu neman ƙwararrun ma’aikata a duniya.

Ya ce shirin ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma burin Gwamnatin Tarayya na samar da guraben aiki miliyan ɗaya ta hanyar fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje.

“Ba sai matashi ɗan Nijeriya ya bar ƙasar ba kafin ya samu damar shiga harkokin tattalin arzikin duniya. Idan aka ba shi ƙwarewar da ta dace, ababen more rayuwa, ƙa’idojin sana’a da damar shiga kasuwanni, ’yan Nijeriya za su iya rayuwa, su yi aiki kuma su samu kuɗi a nan gida, yayin da suke samar da ayyuka ga abokan ciniki da masu ɗaukar ma’aikata a faɗin duniya,” inji shi.

Shi kuma Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce ma’aikatar sa tana inganta ƙwarewar ’yan Nijeriya ta hanyar inganta tsarin koyarwa, koyar da sana’o’i da dabarun fasahar zamani, da kuma horar da su bisa buƙatun masana’antu.

“Manufar Ma’aikatar Ilimi ita ce, a duk inda ake neman ma’aikata a duniya, muna son ’yan Nijeriya su samu horo, su samu takardar shaidar ƙwarewa kuma su kasance a shirye don a ɗauke su aiki,” inji shi.

A nata ɓangaren, Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ta ce gangamin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya, da ƙara fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje da jawo zuba jari.

“Shirin ‘Hire from Nigeria’ ya wuce kamfen na wayar da kai kawai; shiri ne na ƙasa da aka tsara domin bunƙasa tattalin arziki,” inji Oduwole.

Ta ce za a gabatar da kamfen ɗin a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, inda Nijeriya za ta bayyana fa’idar ɗaukar ’yan Nijeriya aiki ga masu ɗaukar ma’aikata na duniya.

Tun da farko, Babbar Mataimakiya ta Musamman kan Sadarwa ta Dabaru da NATEP, Misis Olajumoke Dan-Okayi, ta ce shirin zai magance matsalolin da ke hana ƙwararrun ’yan Nijeriya samun damar aiki a duniya.

Ta ce: “Ba ƙwarewa ce matsalar ba, kuma ba buri ba ne. Matsalar ita ce yadda za a gano ƙwararrun ’yan Nijeriya, amincewa da su da kuma samun damar shiga kasuwannin duniya. Don haka, shirin ‘Hire from Nigeria’ yana da ayyuka uku masu sauƙi: ya sauƙaƙa wa duniya gano Nijeriya, ya sauƙaƙa amincewa da ƙwararrun ’yan Nijeriya, sannan ya sauƙaƙa ɗaukar ’yan Nijeriya aiki.”

Ana sa ran kamfen ɗin zai haɗa ƙwararrun ’yan Nijeriya da masu ɗaukar ma’aikata, kamfanoni masu neman ma’aikata, masu zuba jari da kasuwannin ƙasashen waje.

ABUN A YABA: Musulmin Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙafa Na Ƙungiyar Alnassr, Sadio Mane Na Ci Gaba Da Gwangwaje Mutanen Garinsu Da ...
31/08/2026

ABUN A YABA: Musulmin Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙafa Na Ƙungiyar Alnassr, Sadio Mane Na Ci Gaba Da Gwangwaje Mutanen Garinsu Da Ababen More Rayuwa.

Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool wanda musulmi ne ya gina katafaren asibiti a ƙauyensu, wanda za a dinga duba marasa lafiya da mata masu haihuwa a kyauta.

Haka nan ya gina makarantu a ƙauyen nasu inda ake koyar da mutane ingantaccen ilmi a kyauta. Sannan ya gina katafaren masallaci, ya kuma gina makeken gidan biredi wanda ake siyarwa da araha, sannan ya samar da filin wasan ƙwallon ƙafa da za a dinga koya wa matasa ƙwallo don su ɗaukaka a harkar ƙwallo ta duniya. Kuma kowanne wata yana biyan €70 ga kowane magidanci a ƙauyen nasu domin rage ɗawainiyar iyalansu.

Wane irin fata za ku yi masa?

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Fitaccen mawaƙin Kudancin Najeriya Burna Boy ya shirya wani katafaren taron Mauludin Manzon Allah SAW w...
31/08/2026

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Fitaccen mawaƙin Kudancin Najeriya Burna Boy ya shirya wani katafaren taron Mauludin Manzon Allah SAW wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a Ikeja da ke Legas. Rahotanni sun ce mawaƙin ya kashe ɗaruruwan miliyoyi wajen rabawa mutane motoci, babura, Firinji, keken ɗinki da sauran kayayyaki, inda ya gwangwaje wasu da kyautar kuɗaɗe domin su yi jari duka a cikin farin cikin haihuwar Manzon Allah SAW. Mawaƙin dai ya musulunta ne a shekarar da ta gabata sakamakon bincike da ya yi ya gano cewa Musulunci ne addinin gaskiya.

Wane irin fata za ku yi masa?

Ku yi following ɗin jaridar CCN Hausa domin samun ingantattun labarai masu ƙayatarwa

ABUN A YABA: Wani ɗan kasuwa Musulmi ɗan asalin Igbo Hon. Alhaji Ibrahim Uchenna Ezeaniya gina katafaren masallaci tare ...
31/08/2026

ABUN A YABA: Wani ɗan kasuwa Musulmi ɗan asalin Igbo Hon. Alhaji Ibrahim Uchenna Ezeaniya gina katafaren masallaci tare da cibiyar koyar da addinin Musulunci a jihar Enugu.

Ana shirin buɗe cibiyar nan ba da jimawa ba domin hidimar al’ummar Musulmi da yaɗa ilimin addinin Musulunci.

Ɗan kasuwar ya sha alwashin ci gaba da gina masallatai da makarantun musulunci domin bunƙasa addinin a lokacin da rahotanni s**a ce shi ne addini mafi saurin yaɗuwa a yankin na Igbo.

Allah ya ƙara wa Musulunci ɗaukaka

ALBARKACIN ANNABI: Yaron da maigidansa ya yi wa duka kuma ya kore shi daga aiki saboda zuwa zagayen Mauludi tare da ƙin ...
31/08/2026

ALBARKACIN ANNABI: Yaron da maigidansa ya yi wa duka kuma ya kore shi daga aiki saboda zuwa zagayen Mauludi tare da ƙin zuwa wurin aiki, ya samu gagarumar kyautar kuɗaɗe daga masoya Manzon Allah SAW, inda zuwa yanzu ya samu sama da Naira Miliyan 7, yayin da ake ci gaba da tura masa kuɗin.

Wane irin fata za ku yi masa?

Address

B. U. K Road
Kano
700301

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when CCN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to CCN Hausa:

Shortcuts

Share