10/07/2025
Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Na Samar da Damarmakin Cigaba — Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana samar da damarmaki na cigaban ƙasa a fannoni daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Minna, Jihar Neja, yayin taron Kwamishinonin Yaɗa Labarai daga jihohin da jam’iyyar APC take mulki, wanda Ƙungiyar Gwamnonin APC ta shirya don ƙarfafa dabarun sadarwa da haɗin gwiwa tsakanin matakai daban-daban na gwamnati.
Ya ce: “Shirin Sabunta Fata ya wuce sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya. Magana ce ta samar da damarmakin cigaban ƙasa a fannoni daban-daban – ga mutum ɗaya, ga iyalai, da kuma ga al’umma gaba ɗaya.”
Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana aiwatar da shirye-shirye masu ɗaukar hankali ta hanyar manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen tallafa wa matasa, da kuma sauye-sauye a fannonin noma, mak**ashi, ilimi da ƙere-ƙere.
Ministan ya bayyana cire tallafin fetur a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan da gwamnatin ta ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziki.
Ya ce: “Ɗaya daga cikin manya kuma mafi tasiri daga cikin matakan da wannan gwamnati ta ɗauka shi ne cire tallafin fetur, wanda ko da yake ya kasance mai raɗaɗi, amma sauyi ne da ya zama dole. Bayan ceton tattalin arzikin ƙasa daga rugujewa, wannan mataki ya hana ɓarna da asarar kuɗi sosai a tattalin arzikin mu.”
A cewar sa, kuɗaɗen da aka ceto daga cire tallafin ana amfani da su ne wajen manyan ayyukan raya ƙasa irin su hanyar Legas zuwa Kalaba, hanyar Sakkwato zuwa Badagiri, shimfiɗa layin dogo na Kaduna zuwa Kano, da sake gina hanyar mota ta Abuja zuwa Kaduna da Kano.
Ya ƙara da cewa akwai cigaba da aka samu wajen saka hannun jari a fannin ayyukan jin daɗi a faɗin ƙasar nan, tare da ƙaruwa a cikin kuɗaɗen da ake tura wa jihohi a kowane wata, wanda ke ba su damar aiwatar da ayyuka masu tasiri a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Da