
07/08/2025
Tinubu ya naɗa Injiya Ramat a matsayin shugaban NERC da kuma Kwamishinonin hukumar
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC).
Injiniya Ramat, mai shekaru 39, ƙwararren injiniya ne a fannin lantarki kuma gogaggen mai gudanarwa, wanda ke da digiri na uku (PhD) a fannin Gudanarwa ta Dabaru da wasu ƙarin ƙwarewa.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya nada wasu kwamishinoni biyu domin aiki a hukumar NERC. Su ne Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Masu Amfani da Wuta da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa.
Dukkan nade-naden suna jiran tantancewa da amincewar Majalisar Dattawa.
Sai dai, domin guje wa gibin shugabanci a wannan muhimmin bangare na gwamnati, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin cewa Injiniya Ramat ya fara aiki a matsayin mai riƙon ƙwarya kafin tantancewarsa, kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar nada jami’an ta fito ne daga mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga, a ranar Laraba, 7 ga Agusta, 2025.