18/09/2025
Gidauniyar Sanata Barau I. Jibrin Foundation (BIJF) ta fitar da sunayen ɗalibai 1,000 da s**a rabauta da tallafin guraben karatun digiri na farko
Mataimakin Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya sanar da zaɓar ɗalibai 1,000 da za su ci gajiyar shirin tallafin karatun digiri na farko na zangon 2025/2026 a ƙarƙashin Barau I. Jibrin Foundation (BIJF).
A sanarwar da ofishinsa ya fitar, an ce za a raba takardun tallafin ga waɗanda s**a ci gajiyar shirin a ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025, a Jami’ar Bayero Kano (New Site) da ƙarfe 12 na rana.
Haka kuma, bikin ƙaddamar da shiga jami’a (matriculation) na ɗaliban da aka tallafa wa zai gudana a ranar Litinin, 22 ga Satumba, 2025, a Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma, Jihar Katsina da ƙarfe 10 na safe.
Sanata Barau ya bayyana cewa wannan shiri wani ɓangare ne na manufofin BIJF na ƙarfafawa matasa da ba su damar samun ilimi domin ci gaban ƙasa.
Za a wallafa jerin sunayen waɗanda s**a samu guraben karatun a jaridun Daily Trust da The Nation na ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025.
Sanatan ya taya ɗaliban murnar samun damar, yana mai cewa za su ci gaba da goyon bayan matasa don ganin Najeriya ta samu ci gaba ta fuskar ilimi da ƙwarewa.